'Kuyi ta kanku, wanda ya ɓata ba zai cutar daku ba matuqar kun shiryu'


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

WANNAN BA HUJJA BACE TA KAME BAKI DAGA ZALUNCIN AZZALUMAI

Idan ka kasa al'umma kashi 100, to, za ka sami kashi 72% na ganin hujja ce gare su suyi shiru bisa zaluncin azzalumai da sunan duk abinda mutum yayi kansa ya yiwa. 

Akwai wasu daga cikinsu masu yin wa'azi amma dangane da abinda ya shafi zaluncin azzalumai sai su kawar da kansu suyi shiru. Wasu kuma ba ma yin wa'azin suke ba, sai dai kaga sun kebanta da wasu ayyukan ibada ko kuma na neman kusanci ga Allah bisa zaton shine kadai umarnin da Allah yayi musu.

To, gaskiya wannan gurbatacciyar fahinta ce da kuma rashin sanin ma'anar ayoyin Allah tare da bin son zuciya. 

Manzon Allah (S. A. W. W) shine mai fassara ayoyin Allah da kyakkyawar fassara, kuma aiki da fassarar tasa ita ce tsira ga dukkan wani mumini. 

Ya zo cikin Sunan na Tirmidhi kamar haka;

👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇

«3335» حدثنا سعيد بن يعقوب الطالقاني حدثنا عبد الله بن المبارك أخبرنا عتبة بن أبي حكيم حدثنا عمرو بن جارية اللخمي عن أبي أمية الشعباني قال أتيت أبا ثعلبة الخشني فقلت له كيف تصنع في هذه الآية قال أية آية قلت قوله: {يا أيها الذين آمنوا عليكم أنفسكم لا يضركم من ضل إذا اهتديتم} قال أما والله لقد سألت عنها خبيرا سألت عنها رسول الله صلى الله عليه وسلم فقال: ((بل ائتمروا بالمعروف وتناهوا عن المنكر حتى إذا رأيت شحا مطاعا وهوى متبعا ودنيا مؤثرة وإعجاب كل ذي رأي برأيه فعليك بخاصة نفسك ودع العوام فإن من ورائكم أياما الصبر فيهن مثل القبض على الجمر للعامل فيهن مثل أجر خمسين رجلا يعملون مثل عملكم)). قال عبد الله بن المبارك وزادني غير عتبة قيل يا رسول الله أجر خمسين رجلا منا أو منهم قال: ((لا بل أجر خمسين منكم)).

قال أبو عيسى: هذا حديث حسن غريب.

Sa'eed Bn Ya'aqub Al-'Dalaqaaniy ya bamu labari, Abdullahi Bn Mubarak ya bamu labari, Utbata Bn Abiy Hakeem ya bamu labari, Amru Bn Jariyata Al-Lakhamiy ya bamu labari daga baban Umayyata As-Sha'abaaniy yace : Na jewa Baban Tha'alabata Al-Kashniy sai nace masa, ya kuma aikatawa dangane da wannan aya; Yace, aya ? Wacce aya ce? Nace, fadinSa:

" YAA KU WADANDA SUKA YI IMANI ! KUYI TA KANKU, WANDA YA 'BATA BA ZAI CUTAR DAKU BA MATUQAR DAI KUN SHIRYU ."

Sai yace, amma wallahi kayi tambaya game da ita don sanin labari. Na tambayi Manzon Allah (S. A. W. W) game da ita, sai yace; 

" A'A, (ba wai ana nufi kuyi shiru bane ko ku kebe kawukanku da nufin neman kusanci ga Allah), KUYI UMARNI DA KYAKKYAWA KUMA KUYI HANI GAME DA MUMMUNA, HAR SAI IN KUNGA ANA YIN 'DA'A GA SON RAI KUMA ANA BIN SON ZUCIYA , KUMA DUNIYA ANA FIFITATA, SANNAN KUMA ANA AMSAWA DUKKAN WANI RA'AYIN MAI RA'AYI (mummuna) , TO, (anan) NA HORE KA DA KEBE KANKA, KA BAR JAMA'A. DOMIN A BAYANKU AKWAI WASU KWANUKA, YIN HAQURI CIKINSU TAMKAR WANDA YA RIQE GARWASHIN WUTA NE. MASU YIN AIKI CIKINSU (umarni da kyakkyawa da kuma yin hani game da mummuna) LADANSA KAMAR LADAN MUTANE HAMSIN (50) NE. SUNA YIN AIKI IRIN AYYUKANKU. "

Abdullahi Bn Mubarak yace : wani wanda ba Utbata ba ya qara min cewa : Aka ce; " Yaa Ma'aikin Allah ! Ladan mutane hamsin (50) daga cikinmu ko daga cikinsu ?" Yace :

" A'A, LADAN MUTANE HAMSIN DAGA CIKINKU !"

Abu Isah (Al-Tirmidhi) yace, wannan hadisi mai kyau ne baqo (saboda wasu basu kawo shi ba).

(SUNAN TIRMIDHI, KITABUL-TAFSIR, HADISI MAI LAMBA 3335)

Kunga anan ba zai taba zama hujja gare ku ba ku kame bakunanku daga fadawa azzalumai gaskiya kuna kebe kawunanku da yin wasu abubuwa da sunan gyaran ruhi kuna barin umarni da kyakkyawa da kuma yin hani game da mummuna. Domin da ace wanda ya kawo saqon (Muhammad S. A. W. W) ya kebe kansa ne da sunan gyaran ruhi ba tare da yin umarni da kyakkyawa da yin hani game da mummuna ba, to, da kuwa ba a sami gyara ba. 

Daga wakilanmu na Bauchi zone. 

Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.

      (08137925034)

19th June, 2021/ 9th Zul-Qadah, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post