Iyakacin abinda mace za ta iya sadaqa dashi daga kayan mijinta, ba tare da izinin sa ba !


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

MATA KUYI HATTARA GAME DA DUKIYOYIN MAZAJENKU 

Su mata sun kasu kala-kala wajen halayyarsu ta kyautatawa, akwai wadanda suke da qoqari wajen kyautatawa danginsu daga cikin dukiyar mazajensu, wasu kuma basu warewa tsakanin danginsu da dangin mazajensu. 

Da yawa daga cikin 'yan Boko danginsu ba sa morar dukiyarsu kamar yadda dangin matansu ke cin gajiyarsu. Wannan kuwa na da tasiri ne sakamakon yadda matan nasu ke da tasiri a kansu. 

Na'am, akwai wasu mata masu kirki wadanda suke taimakawa dangogin mazajensu wajen samun wani abu daga cikin abinda mazajen nasu suka mallaka, sai dai qalilan ne daga cikinsu.

To, kada ya kasance ku riqa daukar wani abu daga cikin dukiyar mazajenku kuna yin sadaqa ko kyauta matuqar ba tare da izninsu ba. 

Duk matar data dau wani abu cikin dukiyar mijinta tayi kyauta ko sadaqa dashi ba tare da izninsa ba, to, ta aikata haram. 

Akwai wani abu wanda mace za ta iya yin kyauta ko sadaqa dashi daga cikin abinda mijinta ya mallaka ba tare da izninsa ba kuma bata sami zunubi ba sai dai idan yayi mata hani kan haka, to, zai iya zama haram gare ta in tayi amfani dashi wajen kyauta ko sadaqa. 

Ga wasu riwayoyi masu nuni kan haka kamar yadda za mu kawo. 

👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇

قرب الإسناد مُحَمَّدُ بْنُ الْوَلِيدِ عَنِ ابْنِ بُكَيْرٍ قَالَ: سَأَلْتُ أَبَا عَبْدِ اللَّهِ ع عَمَّا يَحِلُّ لِلْمَرْأَةِ أَنْ تَتَصَدَّقَ مِنْ بَيْتِ زَوْجِهَا بِغَيْرِ إِذْنِهِ قَالَ الْمَأْدُومُ‏[1].

فقه الرضا ص 34.

Ya zo cikin Qarabul-Isnaad daga Muhammad Bn Walid, daga Ibn Bukhair yace : Na tambayi Abu Abdullahi (A. S) game da abinda ya halatta ga mace tayi sadaqa dashi daga gidan mijinta ba tare da izninsa ba. Sai yace; 

" KAYAN MIYA ."

Wannan hadisi yana nuna mana ne cewa kayan miya kamar su :-

- Barkwano, 

-Kuka, 

-Kalwa, 

-Tumatur, 

-Gishiri,

-Kubewa, 

-Albasa D. S za a iya yin sadaqa dasu daga cikin abinda mai gida ya bar miki, sai dai idan yayi miki hani kan haka, to, sai ya zama bayarwar ya zama saba umarninsa. 

  عَلِيٌّ عَنْ أَخِيهِ ع قَالَ: سَأَلْتُهُ عَنِ الْمَرْأَةِ هَلْ لَهَا أَنْ تُعْطِيَ مِنْ بَيْتِ زَوْجِهَا بِغَيْرِ إِذْنِهِ قَالَ لَا إِلَّا أَنْ يُحَلِّلَهَا[3].

قرب الإسناد ص 101.

Daga Aliyu, daga 'Dan'uwansa (A. S) yace : An tambaye shi game da mace cewa za ta iya bayar da wani abu daga cikin gidan mijinta ba tare da izninsa ba ? Yace; 

" A'A, SAI DAI IN HAR YA HALATTA MATA ."

Wannan hadisi ya qara fitar mana cewa koma bayan wancan abinda yazo cikin riwayar farko, ba zai halatta gare ta ta tayi kyautar wani abu daga cikin gidan mijinta wanda ba mallakinta bane har sai in ya halatta mata yin hakan. 

Daga wakilanmu na Bauchi zone. 

Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.

        (08137925034)

17th June, 2021/ 7th Zul-Qadah, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post