Menene gaskiyar bacin Sallar wanda kare ya wuce ta gabansa ?



 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


YA KAMATA ASAN MAGANA 'DAYA TA GASKIYA


Na sha ji daga bakin maluma na cewa duk wanda yake sallah sai Kare ya gifta ta gabansa, to, sallarsa ta bace sai dai ya sake wata sabuwa. 


Ban taba cin karo da wata magana wacce ke saba wannan magana ba har sai da nayi artabu da wasu hadisai cikin SUNAN na ABU DAWUD. 


Ga riwayoyin nan kamar yadda naci karo dasu. 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇



باب مَا يَقْطَعُ الصَّلاَةَ: 


702- حَدَّثَنَا حَفْصُ بْنُ عُمَرَ حَدَّثَنَا شُعْبَةُ (ح) وَحَدَّثَنَا عَبْدُ السَّلاَمِ بْنُ مُطَهَّرٍ وَابْنُ كَثِيرٍ- الْمَعْنَى- أَنَّ سُلَيْمَانَ بْنَ الْمُغِيرَةِ أَخْبَرَهُمْ عَنْ حُمَيْدِ بْنِ هِلاَلٍ عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ الصَّامِتِ عَنْ أَبِي ذَرٍّ- قَالَ حَفْصٌ- قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَقَالاَ عَنْ سُلَيْمَانَ قَالَ أَبُو ذَرٍّ: ((يَقْطَعُ صَلاَةَ الرَّجُلِ- إِذَا لَمْ يَكُنْ بَيْنَ يَدَيْهِ قِيدُ آخِرَةِ الرَّحْلِ الْحِمَارُ وَالْكَلْبُ الأَسْوَدُ وَالْمَرْأَةُ)). فَقُلْتُ مَا بَالُ الأَسْوَدِ مِنَ الأَحْمَرِ مِنَ الأَصْفَرِ مِنَ الأَبْيَضِ فَقَالَ يَا ابْنَ أَخِي سَأَلْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَمَا سَأَلْتَنِي فَقَالَ: ((الْكَلْبُ الأَسْوَدُ شَيْطَانٌ)).



BABIN ABINDA KE YANKE SALLAH 



Hafsu Bn Umar ya bamu labari, Shu'ubatu ya bamu labari, kuma Abdus-Salam Bn Mudahhari da Ibn Katheer Al-Ma'anah sun bamu labari cewa, Sulaiman Bn Mugeerata ya basu labari daga Humaid Bn Hilaal, daga Abdullahi Bn Saamiti, daga Abu Zarr yace : Hafsu yace : Manzon Allah (S. A. W. W) yace; kuma suka ce daga Sulaiman, Abu Zarr yace; 


" SALLAR MUTUM TANA YANKEWA IDAN YA KASANCE A GABANSA BABU WANI ABU GWARGWADON SANDAR MASHI, (sai aka sami giftawar) JAKI, DA BAQIN KARE DA KUMA MACE (ta gabansa). "


(Abu Zarr yace), Sai nace, menene laifin baqi (black) daga ja (red) daga fatsi (yellow) daga fari (white)? Sai yace; 


Yaa 'Dan dan'uwana ! Na tambayi Manzon Allah (S. A. W. W) kamar yadda ka tambaye ne, sai yace; 


" AI BAQIN KARE SHAIDANI NE. "


 (SUNAN ABU DAWUD) 


Cikin hadisin za muga cewa an kawo mana abubuwa uku ne masu yanke sallar mutum in bai sanya sutura a gabansa ba, sune :-


- JAKI, 


-BAQIN KARE da kuma 


-MACE.


               TAMBAYA 

          ------------------------


Idan aka ce baqin Kare Shaidan ne shi yasa yake yanke sallar mutum, to, Jan Kare da Fari su ba shaidanu bane saboda haka basu da matsala kenan in sun gifta ta gaban mai sallah ?


Sannan kuma ita ma matar Shaidaniya ce yasa aka ce tana yanke sallah? Shi kuma Jikin fa, ko wanne iri ne ko kuma shi ma sai baqin ne ?


A wani hadisi na gaba kuma ya qara da cewa; 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


704- حَدَّثَنَا مُحَمَّدُ بْنُ إِسْمَاعِيلَ الْبَصْرِيُّ حَدَّثَنَا مُعَاذٌ حَدَّثَنَا هِشَامٌ عَنْ يَحْيَى عَنْ عِكْرِمَةَ عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ قَالَ أَحْسَبُهُ عَنْ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: ((إِذَا صَلَّى أَحَدُكُمْ إِلَى غَيْرِ سُتْرَةٍ فَإِنَّهُ يَقْطَعُ صَلاَتَهُ الْكَلْبُ وَالْحِمَارُ وَالْخِنْزِيرُ وَالْيَهُودِيُّ وَالْمَجُوسِيُّ وَالْمَرْأَةُ وَيُجْزِئُ عَنْهُ إِذَا مَرُّوا بَيْنَ يَدَيْهِ عَلَى قَذْفَةٍ بِحَجَرٍ)). 

قَالَ أَبُو دَاوُدَ: فِي نَفْسِي مِنْ هَذَا الْحَدِيثِ شَيْءٌ كُنْتُ أُذَاكِرُ بِهِ إِبْرَاهِيمَ وَغَيْرَهُ فَلَمْ أَرَ أَحَدًا جَاءَ بِهِ عَنْ هِشَامٍ وَلاَ يَعْرِفُهُ وَلَمْ أَرَ أَحَدًا يُحَدِّثُ بِهِ عَنْ هِشَامٍ وَأَحْسَبُ الْوَهَمَ مِنَ ابْنِ أَبِي سَمِينَةَ- يَعْنِي مُحَمَّدَ بْنَ إِسْمَاعِيلَ الْبَصْرِيَّ مَوْلَى بَنِي هَاشِمٍ- وَالْمُنْكَرُ فِيهِ ذِكْرُ الْمَجُوسِيِّ وَفِيهِ: ((عَلَى قَذْفَةٍ بِحَجَرٍ)). وَذِكْرُ الْخِنْزِيرِ وَفِيهِ نَكَارَةٌ. 

قَالَ أَبُو دَاوُدَ: وَلَمْ أَسْمَعْ هَذَا الْحَدِيثَ إِلاَّ مِنْ مُحَمَّدِ بْنِ إِسْمَاعِيلَ وَأَحْسَبُهُ وَهِمَ لأَنَّهُ كَانَ يُحَدِّثُنَا مِنْ حِفْظِهِ. 


Muhammad Bn Isma'il Al-Basariy ya bamu labari, Mu'azu ya bamu labari, Hishaam ya bamu labari daga Yahya, daga Ikrimata, daga Ibn Abbas (R. A) yace : Na same shi daga Manzon Allah (S. A. W. W) yace; 


" IDAN 'DAYANKU YAYI SALLAH BA TARE DA SUTURA (a gabansa ba), TO, SHI SALLARSA NA YANKEWA SABODA (giftawar) KARE DA JAKI DA AL-HANZIR DA BAYAHUDE DA BAMAJUSE DA MACE. AMMA YANA ISAR MASA IDAN SUKA SHUDE TA GABANSA ALHALI AKWAI DUTSE MAI 'DAN KAURI. "


(SUNAN ABU DAWUD, HADISI MAI LAMBA 704)


Duk da cewa Abu Dawud din ya kawo shi cikin Sahihinsa amma ya kawo wasu maganganu game da wannan hadisi inda yake nuna cewa hadisin Munkari ne saboda an ambaci Bamajuse a cikinsa, sannan kuma yace akwai suka cikinsa da aka ambaci Al-Hanzir cikinsa. 


Yace saboda basu taba samun irin wannan hadisi ba sai a wajen Muhammad Bn Isma'il.


                    NAZARI

                 ------------------


Ko da ace ambaton Bamajuse da Al-Hanzir ne cikin hadisin yasa Abu Dawud ya ambace shi da Munkari da kuma cewa akwai suka cikinsa, to, abin lura kuma a cikinsa shine, ai sunyi tarayya cikin KARE da JAKI da kuma MACE .


Abinda za mu dauka daga cikinsu shine, KARE da JAKI da MACE suna bata sallar mutum in dai har suka wuce ta gabansa ba tare da ya sanya sutura ba. 




Sannan kuma idan ka matsa gaba cikin littafin zuwa kan hadisi mai lamba 718 za ka ci karo da wannan hadisi me cewa;


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇



باب مَنْ قَالَ الْكَلْبُ لاَ يَقْطَعُ الصَّلاَةَ: 


718- حَدَّثَنَا عَبْدُ الْمَلِكِ بْنُ شُعَيْبِ بْنِ اللَّيْثِ قَالَ: حَدَّثَنِي أَبِي عَنْ جَدِّي عَنْ يَحْيَى بْنِ أَيُّوبَ عَنْ مُحَمَّدِ بْنِ عُمَرَ بْنِ عَلِيٍّ عَنْ عَبَّاسِ بْنِ عُبَيْدِ اللَّهِ بْنِ عَبَّاسٍ عَنِ الْفَضْلِ بْنِ عَبَّاسٍ قَالَ أَتَانَا رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَنَحْنُ فِي بَادِيَةٍ لَنَا وَمَعَهُ عَبَّاسٌ فَصَلَّى فِي صَحْرَاءَ لَيْسَ بَيْنَ يَدَيْهِ سُتْرَةٌ وَحِمَارَةٌ لَنَا وَكَلْبَةٌ تَعْبَثَانِ بَيْنَ يَدَيْهِ فَمَا بَالَى ذَلِكَ.


BABIN WANDA YACE KARE BA YA YANKE SALLAH 


Abdulmalik Bn Shu'aib Bn Laitheey ya bamu labari yace : Babana ya bani labari daga kakana daga Yahya Bn Ayuba, daga Muhammad Bn Umar Bn Aliyu, Abbas Bn Ubaidullah Bn Abbas, daga Fadl Bn Abbas yace : Manzon Allah (S. A. W. W) yazo mana yayin da muke qauye, kuma tare dashi akwai, sai suka yi sallah cikin Sahara, a gabansa (S. A. W. W) babu wata sutura, kuma ga Jakinmu da Karenmu suna ta wasanninsu a gabansa (S. A. W. W), kuma babu wani laifi cikin haka. "


(SUNAN ABU DAWUD, HADISI MAI LAMBA 718)


To, duk da cewa cikin wannan hadisi ba a kawo mace ba, amma kuma an kawo Jaki da Kare cewa suna ta wasanninsu a gaban Manzon Allah (S. A. W. W) yayin da yake sallah, amma kuma basu sake sallar saboda wadannan dabbobi masu bata sallah ba. 


Tabbas, hadisan nan sun kulle min kai ta yadda na kasa gane maganar gaskiya daga wanne take ? Wato wannene gaskiya daga cikinsu, wanda yace sallah na baci ne ko wanda yace ba ta baci saboda su? 


Wannan dai wata fatawa ce wacce nake neman sani ko a warware min ita ta hanyar ilimin da zai iya gamsar dani. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.


       (08137925034)


16th June, 2021/ 6th Zul-Qadah, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post