Haramcin Kuɗin Ruwa (Interest) Da Hukuncinsa..!


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


AKAN WA YAKE, MAIBAYARWA KO MAI KARBA ?


Kudin ruwa ku Riba shine wani qari da ake samu cikin harkar mu'amala ta bashi, ana yinsa ne cikin kudi ko kuma abinci. Zai iya haram na baka na baka bashin Buhun Dawa sannan nace idan ka tashi biya za ka mayar min da Duhu da rabi 1.5. Amma da ace zan baka bashin Buhun Shinkafa 1 sai kuma nace ka biya ni da Buhun Dawa daya da rabi 1.5 zai iya zama halas, domin jinsinsu ya bambanta kuma aka samun fifiko a tsakaninsu. 


Ta bangaren kudi ma zai iya zama halas na baka Zinari ko Azurfa, kai kuma ka biya ni da kudin takarda irin namu na Nigeria, domin su ma suna da bambanci a daraja. 


Amma haramun ne ta kowacce fuska na baka bashin kudi irin namu na takarda sannan nace idan ka tashi biyana za ka qara min wani abu kan abinda na baka. Misali, ace na baka dubu daya #1,000 sannan nace ka mayar min da dubu daya da dari biyu #1,200.


Sannan yana zama haramun idan ya kasance kaya na da zaunannen farashi a kasuwa, kuma idan kazo wajena da kudi a hannu a haka zan sayar maka, amma kuma idan bashi ka nema sai na dora maka wani qari akai. 


Bashi da ruwa (interest) ya samo asali ne tun a jahiliyya, amma kuma su nasu yafi tsarki akan wanda muke yi a wannan zamani, duk da cewa dai dukkansu haramun ne. 


A Jahiliyya ba sa yin qari akan bashin da suka bayar har sai in wanda aka bawa bashin ya kasa biya sannan ayi masa qari. 


Misali:- Na baka bashin #1,000 bisa alqawarin za ka biya ni zuwa sati 1, to, da satin ya cika baka samu ba sai kazo ka yimin bayani tare da neman alfarma na jinkirta maka zuwa kwana uku. To, anan ne sai suce tunda hakane #1,100 za biya idan ka tashi kawowa. Ma'ana sai an kasa biya ne a jahiliyya suke yiwa mutum qari. 


Amma mu a wannan zamani kanmu ya waye bamu da jahilci, saboda haka tun lokacin da mutum ya nemi bashi ake qara masa abinda zai biya ba wai sai ya kasa biya ba. 


To, mu sani cewa Allah (T) na gargadinmu da cewa; 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇



ٱلَّذِينَ يَأۡكُلُونَ ٱلرِّبَوٰاْ لَا يَقُومُونَ إِلَّا كَمَا يَقُومُ ٱلَّذِي يَتَخَبَّطُهُ ٱلشَّيۡطَٰنُ مِنَ ٱلۡمَسِّۚ ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمۡ قَالُوٓاْ إِنَّمَا ٱلۡبَيۡعُ مِثۡلُ ٱلرِّبَوٰاْۗ وَأَحَلَّ ٱللَّهُ ٱلۡبَيۡعَ وَحَرَّمَ ٱلرِّبَوٰاْۚ فَمَن جَآءَهُۥ مَوۡعِظَةٞ مِّن رَّبِّهِۦ فَٱنتَهَىٰ فَلَهُۥ مَا سَلَفَ وَأَمۡرُهُۥٓ إِلَى ٱللَّهِۖ وَمَنۡ عَادَ فَأُوْلَٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلنَّارِۖ هُمۡ فِيهَا خَٰلِدُونَ ٥٧٢ 


" LALLE WADANDA KE CIN RIBA (kudin ruwa) BA ZA SU TASHI BA (ranar alqiyama ) FACE KAMAR MISALIN YADDA WADANDA SHAIDAN YA SHAFE SU (bugun Aljan) SUKE TASHI. DALILI KUW A SHINE SUNCE AI SHI KASUWANCI KAMAR RIBA YAKE. (Allah kuma yace musu a'a) ALLAH YA HALASTA KASUWANCI KUMA YA HARAMTA RIBA. TO, DUK WANDA WA'AZI YAZO MASA DAGA UBANGIJINSA KUMA YA HANU (da cin kudin ruwa), TO, YANA DA ABINDA YA RIGA YA GABATA, AL'AMARINSA NA WAJEN ALLAH. AMMA KUMA WANDA YA DAWO (ya cigaba da cin kudin ruwan) TO WADANNAN MA'ABOTA WUTA NE, KUMA SU ZASU DAWWAMA CIKINTA. 


يَمۡحَقُ ٱللَّهُ ٱلرِّبَوٰاْ وَيُرۡبِي ٱلصَّدَقَٰتِۗ وَٱللَّهُ لَا يُحِبُّ كُلَّ كَفَّارٍ أَثِيمٍ ٦٧٢


" ALLAH NA SHAFE (albarkar) RIBA (komai yawanta) KUMA YANA SANYA ALBARKA CIKIN SADAQA (kasuwar da akayi ta ta hanyar halas), KUMA ALLAH BA YA SON DUKKAN KAFIRI MAI SABO. "


(SURATUL-BAQARATA : 275-276)


Kunga anan qarara an nuna mana haramcin cin kudin ruwa, amma idan mutum yaji wa'azi sai ya daina, to, duk abinda ya tara ko ya kai #1,000,000,000 ya zama halas, kamar dai yadda muslimci ke kankare daudar kafirci da shirka. Amma idan mutum ya dawo ya cigaba da cin kudin ruwa bayan wa'azi ya zo masa, to, dan wuta ne kuma zai dawwama a cikinta. 


AKAN WA HARAMCIN YAKE, MAI KARBA KO MAI BAYARWA ?


Mutane da yawa suna karanta ayoyin Alqur'ani har suyi musu fassara amma basu san haqiqanin ma'anoninsu ba. Saboda hakane ma aka riqa samun kuskure cikin hukunce-hukuncen magabata. Za mu fahinci hakan idan mun duba hukunce-hukuncen da Abubakar da Umar suka riqa yi cikin kuskure, Imam Ali (A. S) kuma ya riqa cin gyaransu ta hanyar kafa musu hujjoji daga cikin Qur'ani wanda su basu fahince su ba. 


To, abinda wasu ke cewa shine, wai haramcin na kan mai karbar da mai bayarwa ne babu bambanci, amma lalle ba haka hukuncin yake ba. 


Ku biyo mu cikin littafin Allah don ganewa da idanuwanku. 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَذَرُواْ مَا بَقِيَ مِنَ ٱلرِّبَوٰٓاْ إِن كُنتُم مُّؤۡمِنِينَ ٨٧٢


" YAA KU WADANDA SUKA YI IMANI ! KUJI TSORON ALLAH KUMA KU BAR ABINDA YA RAGE DA RIBA IN KUN KASANCE MUMINAI ."


 فَإِن لَّمۡ تَفۡعَلُواْ فَأۡذَنُواْ بِحَرۡبٖ مِّنَ ٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦۖ وَإِن تُبۡتُمۡ فَلَكُمۡ رُءُوسُ أَمۡوَٰلِكُمۡ لَا تَظۡلِمُونَ وَلَا تُظۡلَمُونَ ٩٧٢


" IDAN KUMA BAKU AIKATA BA (wato idan baku bari ba) ANYI MUKU IZNIN YAQI DAGA ALLAH DA MANZONSA. IDAN KUMA KUKA TUBA (daga cin kudin ruwan), TO, KUNA DA ASALIN DUKIYARKU (wacce kuka bayar) KADA KUYI ZALUNCI (ta hanyar karbar qari ba), KUMA BA ZA A ZALUNCEKU BA (ta hanyar hana muku haqqinku wanda kuka bayar). "


 وَإِن كَانَ ذُو عُسۡرَةٖ فَنَظِرَةٌ إِلَىٰ مَيۡسَرَةٖۚ وَأَن تَصَدَّقُواْ خَيۡرٞ لَّكُمۡ إِن كُنتُمۡ تَعۡلَمُونَ ٠٨٢


" IDAN KUMA (wanda aka bawa bashin) YA KASANCE MA'ABOCIN QUNCI NE, TO, KU JINKIRTA MASA ZUWA SAMUN SAUQI (ba sai kun dora masa wani abu don jinkirin da aka samu ba). DA KUMA ZA KUYI SADAQA (ku yafe masa) YAFI ALKHAIRI GARE KU (maimakon yi masa qari) IN DA KUN KASANCE MASU SANI. "


(SURATUL-BAQARATA :278-280)


Idan muka nazarci wadannan ayoyi za muga cewa gaba daya suna magana ne kan wanda ke bayarwa ba mai karba ba. Sannan kuma da aka ce, " KUNA DA ASALIN DUKIYARKU. " Ai za mu fahinci cewa wanda ya bada bashi shine mai asalin dukiya ba wai mai karbar ba. Sai kuma aka qara da cewa, " KADA KUYI ZALUNCI. " Wanda hakan ke qara nuna mana zalunci ne na cewa sai an baka sama da abinda ka bayar, wanda hakan ke yin nuni akan shi mai bayarwa. Sai kuma aka qarqare da cewa, " KUMA KU MA KADA A ZALUNCE KU. " Wanda hakan ke nuna cewa kada a hana ku abinda kuka bayar kamar yadda wasu ke yi. Idan an basu bashi sai suqi biya, hakan shine zaluntar wanda ya bada bashin. 


Saboda haka haramcin yana kan mai bayarwa ne, ko kadan mai karba bashi da laifi, hasali ma shi bashi dole ce ke sa a karba. Idan mutum ya san gurin da zai je a bashi bashi ba tare da anyi masa qari ba wallahi can zai tafi ya bar inda ake yin qari. Amma in babu yadda zai yi dole yaje inda za ayi masa qarin. 


DON QARIN BAYANI KU BIYO MU CIKIN WADANNAN HADISAI 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


(1)- حدثنا عفان حدثنا عبد الوارث حدثنا محمد بن جحادة عن سليمان بن بريدة عن أبيه قال سمعت النبي صلى الله عليه وسلم يقول من أنظر معسرا فله بكل يوم مثله صدقة قال ثم سمعته يقول من أنظر معسرا فله بكل يوم مثلاه صدقة قلت سمعتك يا رسول الله تقول من أنظر معسرا فله بكل يوم مثله صدقة ثم سمعتك تقول من أنظر معسرا فله بكل يوم مثلاه صدقة قال له بكل يوم مثله صدقة قبل أن يحل الدين فإذا حل الدين فأنظره فله بكل يوم مثلاه صدقة « حديث آخر » عن أبي قتادة الحارث بن ربعي الأنصاري قال أحمد « 5/308 »


Imam Ahmad Bn Hambal yace, Affan ya bamu labari, Abdul-Warith ya bamu labari, Muhammad Bn Jahadata ya bamu labari daga Sulaiman Bn Buraidata, daga babansa yace; Naji Annabi (S. A. W. W) yana cewa; 


" DUK WANDA YA JINKIRTAWA WANDA KE CIKIN QUNCI, TO, CIKIN KOWACCE RANA YANA DA MISALIN SADAQA (na adadin abinda ya bayar na bashin). 


Nace, na ji ka yaa Manzon Allah (S. A. W. W) kana cewa, wanda ya jinkirtawa wanda ke cikin qunci yana da sadaqa cikin kowacce rana misalinta . Sa'annan na ji ka kana cewa, duk wanda ya jinkirtawa wanda ke cikin qunci yana da sadaqa cikin kowacce rana misalinta.


Yace masa , " EH, CIKIN KOWACCE RANA YANA DA SADAQA MISALINTA KAFIN BASHIN YA HAU KANSA (ya kasa biya) .IDAN KUMA BASHIN YA HAU KANSA SAI (mai kudin) YA JINKIRTA MASA, TO, CIKIN KOWACCE RANA YANA DA (ladan) SADAQA MISALINTA. "


Kunga cikin wannan hadisin ma yana magana ne kan wanda ya bada bashin ba wai wanda aka bawa ba. Har ma ake nuna falalar yin haquri da yin jinkiri zuwa ga wanda aka bawa bashi.




(2)- عن حذيفة بن اليمان قال الحافظ أبو يعلى الموصلي حدثنا الأخنس أحمد بن عمران حدثنا محمد بن فضيل حدثنا أبو مالك الأشجعي عن ربعي بن حراش عن حذيفة قال قال رسول الله صلى الله عليه وسلم أتى الله بعبد من عبيده يوم القيامة قال ماذا عملت لي في الدنيافقال ما عملت لك يارب مثقال ذرة في الدنيا أرجوك بها قالها ثلاث مرات قال العبد عند آخرها يارب إنك كنت أعطيتني فضل مال وكنت رجلا أبايع الناس وكان من خلقي الجواز فكنت أيسر على الموسر وأنظر المعسر قال فيقول الله عز وجل أنا أحق من ييسر ادخل الجنة وقد أخرجه البخاري « 2391 » ومسلم « 1560 » 


Daga Huzaifata Bn Yamani, Hafiz Abu Ya'ala Al-Mausiliy yace, Aknaas Ahmad Bn Imrana ya bamu labari ,Muhammad Bn Fufhail ya bamu labari, Abu Malik Al-Ashja'iy ya bamu labari daga Rabi'a Bn Haraash, daga Huzaifata yace, Manzon Allah (S. A. W. W) yace; 


" ALLAH ZAI ZO DA BAWA DAGA CIKIN BAYINSA RANAR ALQIYAMA SAI YACE, " ME KA AIKATA MIN A DUNIYA? Sai yace, " Ban aikata wani abu daidai da qwayar Zarra a duniya gare ka wanda nake neman yardarka ba yaa Ubangijina. Sau uku zai fadi haka. Sai bawan ya fada a qarshe cewa; 


" Yaa Ubangiji ! Haqiqa kai ka bani falala ta dukiya, kuma na kasance mutum wanda wanda ke kasuwanci da mutane. Kuma ya kasance daga cikin dabi'una kauda kai, na kasance ina sauqaqawa wanda ke cikin qunci, kuma ina jinkirtawa wanda ke cikin qunci (idan bashi ya shiga tsakanina dashi). " Yace, sai Allah yace; 


" AI NI NAFI CANCANTA DA SAUQAQAWA, KA SHIGA ALJANNAH. "


(Bukhari ya fitar da wannan hadisi cikin hadisi mai lamba 2391, Muslim ma ya fitar dashi cikin hadisi mai lamba 1560)


            NAZARI 


Idan muka nazarci dukkan ayoyi da hadisan da muka kawo cikin wannan rubutu musu gargadi da kwadaitarwa za muga gaba-daya suna magana ne kan wanda ke bayar da bashi ba wanda ake bawa ba. Saboda haka laifin kudin ruwa na kan mai bayarwa ne shi kadai ba akan mai karba ba , kuma ba akansu dukkansu ba. 


YAA ALLAH KA BAMU ILIMI MAI AMFANI BA NA SHIGA RUDU BA 🙏🏻🙏🏻🙏🏻


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.


          (08137925034)


17th May, 2021/ 6th Shawwal, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post