Cigaba da rayuwa da irin wannan kunyar ta hausawa bashida wani anfani..! Inji Matashiyar Marubiya Zarah A Zamsarf

 SABO/ KUSANCI/ SHAKUWA !!!




Na daya daga cikin hanyoyin da ke kawar da wasu hijabai na kunya da dar_dar  a tsakanin al'umma.


Idan nace kunya ba ina magana akan irin kunyar da muka sani ba, kamar misalin irin kunyar da akasan mata da ita, irin wacce Allah da annabi sukayi magana akai,to ba irinta ba, ina magana akan kunya irin ta hausawa, itace irin kunyar da wasu dalilai ne ke kawo ta, bawai ana jinta dinne da gaske har cikin zuciya ba.



Sabo, kusanci ko ince shakuwa yana taka muhimmiyar rawa wurin kawar da irin wannan kunyar, sannan yakan sanya sakin jiki da jin tsoro ko dar_dar din yin wani abu a gaban wanda ake jima irin wannan kunya din.


Sau tari irin wannan kunya din na hana wasu abubuwan da daman gaske, wanda kuma sunada muhimmanci a rayuwa suma, misali idan ya kasance anajin kunyar mutum to ba komi bane ake iya fada masa ko ake iya sakin jiki a tattauna dashi ba, wanda kuma da za'a cire kunyar ayi maganar dashi za'a iya samun mafita cikin sauki ba tare da ansha wahala ba, ina ana jin irin wannan kunyar na mutum to ana zama a takure ne idan yana wuri, wanda akan takura din dagasken gaske.


Shakuwa da sabo da mutune shine yake bada damar kecewar wa'yannan hijaban, wanda ta hakanne ake samun rashin aukuwar wasu matsalolin, domin idan Babu wannan kunyar to akwai matsalolin da za'a samu raguwar faruwan su.


 

A ganina cigaba da rayuwa da irin wannan kunyar ta hausawa bashida wani anfani, domin yana zama sanadin  faruwan wasu matsalolin na daban.



Allah ya bamu ikon kiyaye dokokinsa. Ya rabb


✍️_ Zarah A Zamsarf

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post