Dalilin Da Ya Hana Annabi (S.A.W.W) Rubuta Wasiyya, Inji Ibn Abbas (R.A) !


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


MATSALA CE TSAKANIN UMMUL-MUMININA A'ISHA DA HAFSAT 


Babu wani malami wanda bai san wannan aya da ke cewa; 


" BA YA KASANCEWA GA MUMINI KO MUMINA IDAN ALLAH DA MANZONSA YA HUKUNTA WANI AL'AMARI YA KASANCE WANI ZABI GARE SHI CIKIN AL'AMARINSA... " 


To, kamar yadda Ibn Abbas (R. A) ya kawo shine Annabi (S. A. W. W) yayi nufin rubutawa wasiyya kamar yadda ya umarci al'ummarsa da rubuta wasiyyah kafin barinsu duniya, sai dai wata matsala da ta faru tsakanin Ummul-muminina A'isha da Hafsat ne yayi sanadin hana shi rubuta wannan wasiyyah a rubuce. 


Ku fahinci wani abu anan, batun rubuta wasiyyah ake yi ba wai yin wasiyyah ba, domin yin wasiyyah ya riga ya yi ta a gurare da dama game da cewa Imam Ali (A. S) shine wasiyyinsa kamar yadda muka kawo cikin rubutunmu na baya. 


Ga dai dalilin da ya hana in ji Ibn Abbas (R. A). 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


حَدَّثَنَا أَبُو كُرَيْبٍ، قَالَ: حَدَّثَنَا يُونُسُ بْنُ بُكَيْرٍ، قَالَ: حَدَّثَنَا يُونُسُ بْنُ عَمْرٍو، عَنْ أَبِيهِ، عَنِ الأَرْقَمِ بْنِ شُرَحْبِيلَ، قَالَ: سَأَلْتُ ابن عباس: اوصى رسول الله ص؟ قَالَ: لا، قُلْتُ: فَكَيْفَ كَانَ ذَلِكَ؟ قَالَ: [قال رسول الله: ابْعَثُوا إِلَى عَلِيٍّ فَادْعُوهُ، فَقَالَتْ عَائِشَةُ:

لَوْ بَعَثْتَ إِلَى أَبِي بَكْرٍ! وَقَالَتْ حَفْصَةُ: لَوْ بَعَثْتَ إِلَى عُمَرَ! فَاجْتَمَعُوا عِنْدَهُ جَمِيعًا، فَقَالَ رسول الله ص: انْصَرِفُوا، فَإِنْ تَكُ لِي حَاجَةً أَبْعَثْ إِلَيْكُمْ، فانصرفا."


Baban Kuraib ya bamu labari: Yunusa Bn Bukhair ya bamu labari yace : Yunusa Bn Amruu ya bamu labari daga babansa, daga Arqam Bn Shurahbila yace : " Mun tambayi Ibn Abbas (R. A) , Manzon Allah (S. A. W. W) yayi wasiyya ?" Yace, " A'A. "


Muka ce, " To, ya haka ya kasance (yana yin umarni da yin wasiyya amma ace shi bai rubuta ba) ?" Yace; 


" Manzon Allah (S. A. W. W) yace; " KU AIKA ZUWA GA ALIYU YAZO. " Sai A'ishatu tace :


" Me yasa ba za ka aika zuwa ga Abubakar ba ? " Hafsat ma tace; 


" Me yasa ba za ka aika zuwa ga Umar ba ?"


Gaba dayansu (A'isha da Hafsat) suka taru a kansa (suna ta yin wannan magana da jayayya kowacce na burin lalle sai dai a kira babanta). "


Sai Manzon Allah (S. A. W. W) yace; 


" KU TASHI KU TAFI ! IDAN INA DA WATA BUQATA (ta dabam ba irin wannan da kuka yi min jayayya a kanta ba) ZAN AIKA ZUWA GARE KU. "


(TARIKUL-'DABARI)


Idan ba ku manta ba mun taba kawo muku cikin Sahihul-Bukhari inda Annabi (S. A. W. W) ya cewa mahaifansu su kawo masa abin rubutu ya rubuta musu abinda matuqar sunyi riqo da shi a bayansa ba za su bata ba, sai Umar Bn Khaddab yace basu buqatar wani rubutu daga gare shi, littafin Allah ma kadai ya ishe su. Har Annabi (S. A. W. W) yace musu su tashi su bashi guri.


Saboda haka dan ance Annabi (S. A. W. W) bai rubuta Wasiyyah ba ba zai zama abin mamaki ko jayayya ba, domin 'ya'ya da iyayensu sun hana kamar yadda muka gani cikin Sahihul-Bukhari da Tarikh na 'Dabari, amma dai wasiyya ta hanyar furuci yayi a gurare da dama kamar yadda muka kawo muku. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.


        (08137925034)


28th May, 2021/ 17th Shawwal, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post