Bayyanar taurari Uku shine farkon shigan dare🌃 !!!


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UUPDATED @


BA AGOGO 🕒 NE MA'AUNIN SHIGAR DARE KO KETOWAR ALFIJR BA


Abinda mafi yawan mutane suka fi dogaro da shi wajen dakatar da yin sahur yayin azumi ko bude baki shine Agogo 🕒, wasu kuma jin kiran sallah daga bakin ladani ko da kuwa ba shi da ilimin lokaci. 


Duk da cewa lokaci na iya cancanzawa, amma hakan ba zai hana yin amfani da Agogo ko kiran sallar ladani wajen wadannan abubuwa biyun ba matuqar ana da ilimin lokaci, domin akwai wadanda ba sa gani (makafi) .


To, ta yaya ake iya gane ko fayyace wadannan abubuwa biyun ba tare da rudani ba ? 'Dan Manzon Allah (S. A. W. W) ya bayyanar mana a ilimance.


Game da fadin Allah (A. W. A) ne cewa; 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


" ثُمَّ أَتِمُّوا الصِّيامَ إِلَى اللَّيْلِ‏."


" SA'AN NAN KUMA KU CIKA AZUMI ZUWA DARE ."


To, da wanne lokaci dare ke shiga ko kuma ya ake gane dare ya shigo ? Ga amsa nan daga bakin jikan Manzon Allah (S. A. A. W), wato Imam Aliyu Al-Ridha (A. S). 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


 فقه الرضا عليه السلام‏ أَوَّلُ أَوْقَاتِ الصِّيَامِ وَقْتُ الْفَجْرِ وَ آخِرُهُ هُوَ اللَّيْلُ طُلُوعُ ثَلَاثِ كَوَاكِبَ لَا تُرَى مَعَ الشَّمْسِ وَ ذَهَابُ الْحُمْرَةِ مِنَ الْمَشْرِقِ وَ فِي وُجُودِ سَوَادِ الْمَحَاجِنِ وَ يُسْتَحَبُّ أَنْ يُتَسَحَّرَ فِي شَهْرِ رَمَضَانَ وَ لَوْ بِشَرْبَةٍ مِنْ مَاءٍ وَ أَفْضَلُ السَّحُورِ السَّوِيقُ وَ التَّمْرُ وَ مُطْلَقٌ لَكَ الطَّعَامُ وَ الشَّرَابُ إِلَى أَنْ تَسْتَيْقِنَ طُلُوعَ الْفَجْرِ وَ أَحَلَّ لَكَ الْإِفْطَارُ إِذَا بَدَتْ ثَلَاثَةُ أَنْجُمٍ وَ هِيَ تَطْلُعُ مَعَ غُرُوبِ الشَّمْسِ.



ثواب الأعمال: 72.


Ya zo cikin Fiqhun Ridha (A. S) cewa;


" Farkon lokacin azumi shine lokacin ketowar alfijri, qarshensa kuma shine dare, bayyanar taurari 🌟 🌟 🌟 uku wadanda ba a ganinsu tare da rana ☀. Da kuma gushewar ja daga mahudar rana da kuma samuwar duhu mai kauri. 


Kuma abin so ne mutum yayi sahur cikin watan Ramadan ko da da kurbi ne na ruwa. Kuma mafificin sahur shine sawiq (ban san ma'anarsa wannan kalma da hausa ba) , da kuma Dabino da abinda ya halatta maka na daga abinci ko abin sha zuwa har sai ka sami yaqinin ketowar alfijri. Kuma ya halatta maka kayi bude baki Idan taurari 🌟 🌟 🌟 uku suka bayyana, suna bayyana ne tare da faduwar rana ☀ (na shari'a). "


Wannan shine ilimin sanin haqiqanin shigar dare ba wai dogaro da Agogo 🕒 ba. Saboda haka in har ba ka san wannan ba, to, daga yau ka soma lura yayin da kaje lokacin shan ruwa. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.


         (08137925034)


2nd May, 2021/ 20th Ramadan, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post