Muqawama ba ɗaukar makami bace ɗaukar matakin dagewa ce!


__Faruq Sani Kudan


Ga masu ɗaukan cewa za a ɗauki makami ne, daman munsan wannan kiran daga maƙiyan mu ya ɓullo suke neman su burkita mana addinin, su ɗauka cewa shi addinin nan addinin ɗaukan makami ne In mutum ya karanta tarihin Manzo Allah (S) zai ga cewa a da'awar sa na Makkah, an sa makami an kashe mutane shashidin farko, sumayya an kashe tane da makami Ita ta fara shahada na ce mata shashidin farko, dan kar na ce mata shahidiyar farko ku ɗauka akwai shashidin farko Namiji. Ita tafara shahada.


An ce, gasa mashi akayi, aka soka mata a al'aura a loƙacin ba abin da musulmai suka iya yi, ba su ɗauko makami ba saboda ba marhalan su ɗauki makamiba ne, marhalan dauriya ne sunyi ta daurewa ne da abin da aka musu, suna cijewa suna dakewa bayan wannan matakin da'awar da dauriya yayi ƙamari, ana dauriya, har an nemi mafita sai Manzo Allah (S) yace to ga mafita wasu su tafi habasha su tsira da addinin su, suka tafi habasha, sannan shi ma ya yi hijira zuwa Madina. To kaga wannan marhalan kenan, har ya shekara goma sha uku a Makka ba za kaga wata aya ta jihadi ba, sai dai ace ku tsaida sallah.


Ku bada Zakka. Zakkan me, ana fassara shi da zakkatun- Nafs ne, ba zakkan dukiyoyi bane in ka ga Zakka a makka, zakkan zuciya ne, ba zakkan dukiya ba.a Madina ne zakkan dukiya tazo to sannan Manzon nan, sai aka biyo shi da yaƙi akai ta ma kai musu hare hare, duk da haka basu mayar da martani ba, har sai da aya ta sauƙo, tace ''Uzina ( lillazina yaƙataluna bi annahum zalimu, wa innallaha ala nasri him kaƙadir).


Harma su Sahabban Annabi suka ce, ya Rasulullah (S) haka nan zasu yi ta kawo mana hari, ba muyi wani abu ba? Yace ni ba a ce min komai dangane da wannan ba. Yana jiran umarni, kaga in da maza kace waye yayi yaƙi? Annabi ne ya yaƙe su, ko su suka yaƙe shi? Su suka yaƙe shi. Sannan kuma, loƙacin da aka bada izinin, sannan aka samu aka yi ƙwamin badar, suka zo da Uhud, kama-kama duk Allah (T) ya bawa Manzonsa nasara sannan sai da Daula ta kafu sannan aka fara kawo mata barazana, sannan ta ɗauki mataki na kare kanta ta gefe har da matakin kare kanta ta kai hari.


Alal misali, harin Khaibar ai matakin kare kai ne, don manzo Allah (S) shi yakai harin me yasa ya kai harin? Saboda nan ne Ummul haba'isin ingizo masa da maƙiya, bayan Handaƙ, ainahin gangamin daga can Khaibar ne, yahudawan Khaibar suka je suka tattaro ƙabilun larabawa da sauran su, aka zo aka dirar masa a Madina saboda haka, tun da nan ne tushe sai aka kai hari tushen, aka rusa tushen tsiya ɗin.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post