Wacce mata ce tafi wata daraja cikin matan Annabi, (S.A.W.W), gogoriyo tsakanin Ummul-Muminina A'isha da Nana Khadijah (S.A)??


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

Nasan daga karanta (Headline) na wannan rubutu nawa wani zai riya cikin zuciyarsa cewa wance ce, sai dai kawai ya bibiyi rubutun zuwa qarshensa don yaga wacece daga cikinsu. 


Wani kuma cewa zai yi, menene fa'idar wannan rubutu? Yayin da wani kuma zai yi wata irin fassara gwargwadon abinda zuciyarsa ta riya masa. 


Tabbas rubutun na da fa'ida, domin kuwa an kawo falalar kowacce daga cikinsu har ma muna jin manyan malamai na ambaton wacce ta fi falala/daraja daga cikinsu bisa hujjojin da suke kawowa. 


A yau za muyi amfani da wasu riwayoyi ne kuma mu nazarce su a ilimance da kuma hankalce. Ga riwayoyin nan kamar haka; 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


(3769) - حدثنا آدم: حدثنا شعبة قال وحدثنا عمرو: أخبرنا شعبة، عن عمرو بن مرة، عن مرة، عن أبي موسى الأشعري رضي الله عنه قال:

قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: (كمل من الرجال كثير، ولم يكمل من النساء إلا: مريم بنت عمران، وآسية امرأة فرعون، وفضل عائشة على النساء كفضل الثريد على سائر الطعام) 


Adam ya bamu labari, Shu'ubata ya bamu labari yace, kuma Amruu ya bamu labari : Shu'ubata ya bamu labari daga Amruu Bn Murrata, daga Murrata, daga Abu Musa Al-Ash'ariy (R. A) yace: Manzon Allah (S. A. W. W) yace; 


" MUTANE DA YAWA DAGA CIKIN MAZAJE SUN KAMMALA, AMMA BABU WADANDA SUKA KAMMALA DAGA MATA SAI; MARYAM BNT IMRANA, DA ASIYA MATAR FIR'AUNA. SHI KUWA FALALAR A'ISHATU AKAN SAURAN MATA KAMAR FIFIKON THAREED NE AKAN SAURAN ABINCI ."


(Thareed dai wani kalan abinci ne, amma kowa ya duba yaga cikin kalan abinci wannene yake gani ya yafi fifiko? To, yadda fifikonsa yake akan sauran abinci haka ma fifikon A'isha yake akan sauran matan duniya). 


(FADHA'ILUS-SAHABA, BABIN FALALAR A'ISHATA, HADISI MAI LAMBA 3769)


             NAZARI

           ----------------


(1)- Idan muka nazarci wannan hadisi za muga cewa yana nuna mana ne mata biyu kadai ke da kamala in har ka cire A'isha, domin ita nata fifikon na dabam ne. Ma'ana har Sayyidah Fatimah (S. A) ma bata kammala ba kamar yadda wannan hadisi ya kawo. 


(2)- Wanne abu ne ke sa ace mutum ya fi kowa ? Fifiko dai shine yin biyayya ga Allah da Manzonsa (S. A. W. W). 


Idan kuwa hakane za mu iya cewa Sayyidah Maryam da Asiya sun sami kalmar yabo cikin Qur'ani. Ita kuwa Ummul-muminina A'isha babu mai kokonton cewa ayoyi da yawa sun sauko wadanda ke nuna zargi a kansu sakamakon wasu halayya da suke nunawa Manzon Allah (S. A. W. W). 


Ga misalai daga ciki :-



......وَإِن تَظَٰهَرَا عَلَيۡهِ فَإِنَّ ٱللَّهَ هُوَ مَوۡلَىٰهُ وَجِبۡرِيلُ وَصَٰلِحُ ٱلۡمُؤۡمِنِينَۖ وَٱلۡمَلَٰٓئِكَةُ بَعۡدَ ذَٰلِكَ ظَهِيرٌ ( ٤)


 (SURAYUL-TAHRIM)



يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّبِيُّ قُل لِّأَزۡوَٰجِكَ إِن كُنتُنَّ تُرِدۡنَ ٱلۡحَيَوٰةَ ٱلدُّنۡيَا وَزِينَتَهَا فَتَعَالَيۡنَ أُمَتِّعۡكُنَّ وَأُسَرِّحۡكُنَّ سَرَاحٗا جَمِيلٗا (٨٢)


           (SURATUL-AHZAB) 



Sannan kuma ta kasance tana zargin wani aiki da Annabi (S. A) ya aikata. Ga shi cikin hadisi kamar haka; 


42 - باب فضل بر أصدقاء الأب


حديث رقم :343


وعن عائشة رضي الله عنها قَالَتْ: 


مَا غِرْتُ عَلَى أحَدٍ مِنْ نِسَاءِ النَّبيِّ صلى الله عليه وسلم مَا غِرْتُ عَلَى خَدِيجَة رضي الله عنها، وَمَا رَأيْتُهَا قَطُّ، وَلَكِنْ كَانَ يُكْثِرُ ذِكْرَهَا، وَرُبَّمَا ذَبَحَ الشَّاةَ، ثُمَّ يقَطِّعُهَا أعْضَاء، ثُمَّ يَبْعثُهَا في صَدَائِقِ خَديجَةَ، فَرُبَّمَا قُلْتُ لَهُ: كَأنْ لَمْ يَكُنْ في الدُّنْيَا إلاَّ خَديجَةَ ‍!فَيَقُولُ: (إنَّهَا كَانَتْ، وَكَانَتْ، وَكَانَ لي مِنْهَا وَلَدٌ) مُتَّفَقٌ عَلَيهِ.


Daga A'isha (R. A) tace : 


" Ban taba yin kashi cikin wata daga matan Annabi (S. A. W. W) amma nayi kishi kan Khadijatu (R. A). Ko sau daya (1) ban taba ganinta ba, amma dai Annabi (S. A. W. W) ya kasance yana yawan ambatonta ne. Kuma sau da yawa in ya yanka Akuya yakan yanyankata gaba-gaba (into pieces) sannan ya aikata qawayen Khadijah. Sau da yawa ina ce masa; Kamar dai ba a taba yin wata mace a duniya ba sai Khadijah. Shi kuma sai yace min; 


" ITA FA (Khadijah) TA KASANCE KAZA DA KAZA DA KAZA (ya riqa ambato matsayinta a darajojinta), KUMA 'YA'YANA DAGA GARE TA SUKE !"


     (RIYADUS-SALIHEEN)


Kun san kuwa da ace abinda (A'isha) take yi masa daidai ne da kuwa ba zai qalubalanceta har ma da nuna mata cewa 'ya'yansa fa daga gare ta (Khadijah) suke ba. 



       KHADIJAH (S. A) 


Ga wasu riwayoyi guda biyu da za mu kawo insha Allah a kanta 



(3815)- حدثنا محمد: أخبرنا عبدة، عن هشام بن عروة، عن أبيه قال: سمعت عبد الله بن جعفر قال: سمعت عليا رضي الله عنه يقول: سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول 

حدثني صدقة: أخبرنا عبدة، عن هشام، عن أبيه قال: سمعت عبد الله بن جعفر، عن علي بن أبي طالب رضي الله عنهم، 

عن النبي صلى الله عليه وسلم قال: (خير نسائها مريم، وخير نسائها خديجة) 


Muhammad ya bamu labari, Ubadata ya bamu labari daga Hishaam Bn Urwata, daga babansa yace : Na ji Abdullahi Bn Ja'afar yace : Na ji Aliyu (R. A) yana cewa; Na ji Manzon Allah (S. A. W. W) yana cewa; 


Sadaqatu ya bani labari, Ubadata ya bamu labari daga Hishaam, daga babansa yace : Na ji Abdullahi Bn Ja'afar daga Aliyu Bn Abiy 'Dalib (R. A), cewa; Annabi (S. A. W. W) yace; 


" MAFI ALKHAIRIN MATANTA (al'ummar baya) ITA CE MARYAMA, KUMA MAFI ALKHAIRIN MATANTA (Al'ummata) Ita ce KJADIJAH. "



(KITABUN-MANAAQIBUL ANSAAR, BABIN AUREN KHADIJAH DA FALALARTA, HADISI MAI LAMBA 3815)


(3820)- حدثنا قتيبة بن سعيد: حدثنا محمد بن فضيل، عن عمارة، عن أبي زرعة، عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: أتى جبريل النبي صلى الله عليه وسلم فقال: يا رسول الله، هذه خديجة قد أتت، معها إناء فيه إدام أو طعام أو شراب، فإذا هي أتتك فاقرأ عليها السلام من ربها ومني، وبشرها ببيت في الجنة من قصب لا صخب فيه ولا نصب 


Qutaibata Bn Sa'eed ya bamu labari, Muhammad Bn Fufhail ya bamu labari, daga Umarata, daga baban Zur'ata, daga Abu Hurairata yace : Jibrilu ya zowa Annabi (S. A. W. W) sai yace; 


" YAA MA'AIKIN ALLAH ! WANNAN KHADIJAH CE, TA ZO DA WATA QWARYA CIKINTA AKWAI KAYAN MIYA KO KUMA ABINCI, KO KUMA DAI WANI ABIN SHA, TO, IDAN TAZO GARE KA KA ISAR MATA DA GAISUWA DAGA UBANGIJINTA DA KUMA DAGA GARE NI. SANNAN KAYI MATA ALBISHIR DA WANI GIDA CIKIN ALJANNAH NA BENI, BABU WAHALA CIKINSA KUMA BABU CUTUWA ."


(KITABU MANAQIBUL-ANSAR, BABIN AUREN ANNABI DA KJADIJAH, HADISI MAI LAMBA 3820)


A cikin hadisi na farko an kawo cewa Khadijah ce mafi alkhairin mata, to, menene matsayin hadisin da aka ce wai fifikon A'isha akan sauran mata kamar fifikon Thareed ne akan sauran abinci ?


Sannan cikin hadisi na biyu an busharar Aljannah da aka yiwa Khadijah, to, yanzu ace wacce ba ayi mata bushara ba ace ta fi wacce aka yiwa.


Bayan haka kuma, wacce har bayan rasuwarta ana tunata saboda matsayinta sannan ace wacce ayoyin zargi suka riqa sauka a kanta kuma tana fadar mummuniyar magana ga Annabi (S. A. W. W) ace ta fi ta ?


Duk wadannan daga Bukhari muka kawo muku, sai a fayyace mana domin an ruda mu, kuma muna jin ana cewa wance ce tafi daraja. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.


        (08137925034)


11th April, 2021/ 29th Sha'aban, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post