Maltina Da Peak Milk Basu Kara Jini A Jikin Dan Adam_Inji Drt Siba Muh'd Shinkafi




Yau Filin mu na Cuta da Magani ya Leka Hamshakin Chemis Dinnan Daya Shahara Kuma ya Bunkasa a Garin Shinkafi ta Jihar Zamfara Wanda ake Cewa  "Arrida Chemist💊Shinkafi"


Inda Drt Siba Muh'd Ya Fara Amsa Mana Tambayoyin mu Kamar Haka:-


Da farko:- Inayi maku barka da JUMA'A 🕌


Dayawa za kaga mutanen mu hausawa a lokacin da aka tabbatar da mutum yana da karancin jini, ko macce tana dauke da juna biyu, ko ta Haihu ta zubar da jini da yawa sai kaji ance a bata maltina da peak milk, a fahimtar mutanen mu zai kara jini. 


Gaskiyar magana babu alaka tsakanin karin jini da Maltina da Peak milk, to ku sani waken muke ci kwara daya yafi Maltina da Peak milk wajen samar da sinadaran kara jini.


Nasan zakuyi mamakin maganata, to ba abun mamaki bane~~~Bincike ne~~Kayi tambaya idan baka gane ba.


Idan kun duba jikin gwangwanin peak milk za kuga babu sidaran karin jini a ciki  ( not rich in iron) Haka Maltina ma Babu sinadaran kara jini a cikin ta.


Tambaya anan shine ta Ina Maltina da Peak milk suka zama maganin karin jini ?


Amsa: wannan kawai al'adace ta mutanen mu ba tareda sanin abun ba.


Maltina na dauke da sinadaran:

- Calories

- Carbohydrates

- Fat 

- Vitamin

- No Iron


Peak milk na dauke da sinadaran: 

- Fat

- Carbohydrates

- Protein

- Salt

- Vitamin A and D

- No Iron


Jikin dan Adam yana samar da jini da kansa, shi jini yana bukatar sinadaran iron daga cikin abincin da muke ci yake samo shi.


Daga karshe ina bada shawara garemu kudin da muke kashewa wajen Maltina da Peak milk domin kara mana jini, muyi amfani da su wajen sayen abinci masu dauke da iron kamar :


- Wake

- kifi

- Nama

- kwai 

- Kaza

- Fara

- zogala (yar makka) 

- cavage

- salat

- da sauran su.

Drt Siba Muh'd Shinkafi kenan a Shagon sa


Allah ya kara mana lafiya da zama lfy.


Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post