Kada Ka Kuskura Ka Sha Ruwa Batare da Dare Yayi ba..!!



 SA'AN NAN KUMA KU CIKA AZUMI ZUWA DARE  !!!


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UUPDATED @


KADA KA KUSKURA KA SHA RUWA BA TARE DA DARE YAYI BA


Qur'ani da hadisi sune ajin farko na shari'a (primary sources of shari'a). Ko da na kawo maka abu to dole ka duba menene aya tace ko hadisi kamar wannan abin, kuma dole ya zamana hadisin yana fassara Qur'anin ne ba wai yana kore abinda ke cikinsa ba. 


Allah (T) ya wajabta mana yin azumi sannan ya sharadanta mana cewa mu cika shi zuwa dare kamar yadda yazo cikin Qur'ani mai tsarki. 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


.........وَكُلُواْ وَٱشۡرَبُواْ حَتَّىٰ يَتَبَيَّنَ لَكُمُ ٱلۡخَيۡطُ ٱلۡأَبۡيَضُ مِنَ ٱلۡخَيۡطِ ٱلۡأَسۡوَدِ مِنَ ٱلۡفَجۡرِۖ ثُمَّ أَتِمُّواْ ٱلصِّيَامَ إِلَى ٱلَّيۡلِۚ ... .


"..... KUMA KUCI KU SHA (cikin dare) HAR SAI FARIN ZARE YA BAYYANA GARE KU DAGA BAQIN ZARE NA DAGA ALFIJR, SA'AN NAN KUMA KU CIKA AZUMI ZUWA DARE. 


(SURATUL-BAQARATA:187)


Wannan dai shine umarnin Allah (T) cewa a cika azumi zuwa dare. Amma da shike wannan umarci bai fayyace mana  cewa wannan dare farkonsa ne ko tsakiyarsa ko kuma qarshensa ba ba za mu iya fitar da hukunci ba dole sai mun saurari abinda mai fassara zai fassara, wato ina nufin Manzon Allah (S. A. W. W).


Idan muka yi amfani da ma'anar Alqur'ani sai kuce duk abinda mutum yayi ya zama daidai, ma'ana idan mutum yasha ruwa a farko ko tsakiya ko kuma qarshen dare, domin ba ace mana wanne yanki ne na daren ba. 


To, anan sai Annabi (S. A. W. W) yayi mana wani bayani yadda za mu iya fahintar wannan hukunci.


Ya zo cikin Sahihul-Bukhari cikin babin gaggauta buda baki kamar haka; 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


تعجيل الإفطار


(1957) - حدثنا عبد الله بن يوسف: أخبرنا مالك، عن أبي حازم، عن سهل بن سعد: 

أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: (لا يزال الناس بخير ما عجلوا الفطر)


Abdullahi Bn Yusuf ya bamu labari, Malik ya bamu labari daga baban Haazeem, daga Sahal Bn Sa'ad : Manzon Allah (S. A. W. W) yace; 


" MUTANE BA ZA SU GUSHE BA SUNA TARE DA ALKHAIRI MATUQAR SUNA GAGGAUTA BUDA BAKI. "


(BUKHARI, KITABIS-SIYAAM, HADISI NA 1957)


Wannan hadisi na nuna mana ne cewa mu bude bakinmu a farkon dare ba tsakiya ko qarshensa ba shi yafi alkhairi gare mu. Sai dai kuma mu lura fa cewa akayi dare ba Magrib ba. 


Saboda haka sai wani hadisi cikin Muwadda-Malik shugaban Mazhabar Malikiyyah ya qara fayyace mana haqiqanin ma'anar ayar. 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


An bani labari daga Malik, daga Ibn Shihaab, daga Humaid Bn Abdurrahman yace; 


" LALLE UMAR BN KHADDAB DA USMAN BN AFFAN SUN KASANCE (su biyun) SANA YIN SALLAR MAGRIBA YAYIN DA SUKE SAURARO ZUWA DUHUN DARE KAFIN SUYI BADA BAKI, SA'AN NAN SUYI BUDE BAKI BAYAN SALLAH, KUMA HAKAN CIKIN RAMADAN NE. "


(Muwadda-Malik, Kitabus-Siyaam, babin gaggauta buda baki, hadisi mai lamba 637)


Kunga wannan hadisi shine yazo daidai da ma'anar ayar dake cikin Surataul-Baqarata wacce tayi mana umarnin cika azumi zuwa dare. 


Idan kuwa kace mana a'a  kafin magrib ake shan ruwa sai muce maka kana nufi su Umar da Usman basu fahinci hakan ba kenan da su ba sa shan ruwa kafin magrib har sai bayanta yayin da suke jiran duhun dare?


Ko kuma cewa kake su Umar da Usman sun saba koyarwar Manzon Allah (S. A. W. W) ne a wannan qadiyya? 


YAA ALLAH KA QARA FAHINTA DAMU GASKIYA DA IKON AIKI DA ITA. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.


        (08137925034)


      19TH APRIL, 2021

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post