Hukuncin wanda zai iya cutuwa ta dalilin qishirwa ko yunwa yayin Azumi !


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


BABU ABINDA YAFI MUSLIMCI SAUQI DA HIKIMA 


Umarni ne na Allah cewa a azumci watan Ramadan baki dayansa, kuma ya sharadanta masu yinsa da wadanda ba za suyi ba saboda wani dalili. 


Akwai wadanda hukunci yahau kansu, sai dai wani lokaci akan sami wani dalili wanda zai iya hana su yi, walau gaba dayansa ba tare da ramuwa ba ko kuma dai a ajiye sannan a rama daga baya. 


Cikin wannan rubutu za mu kawo irin matsalar da ke sa asha ruwa ne kuma a ciyar yayin sha din ba tare da ramawa daga baya ba. 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


فقه الرضا عليه السلام‏ إِذَا لَمْ يَتَهَيَّأْ لِلشَّيْخِ أَوِ الشَّابِّ الْمَعْلُولِ أَوِ الْمَرْأَةِ الْحَامِلِ أَنْ يَصُومَ مِنَ الْعَطَشِ وَ الْجُوعِ أَوْ خَافَتْ أَنْ يُضِرَّ بِوَلَدِهَا فَعَلَيْهِمْ جَمِيعاً الْإِفْطَارُ وَ يُتَصَدَّقُ عَنْ كُلِّ وَاحِدٍ لِكُلِّ يَوْمٍ بِمُدَّيْنِ مِنْ طَعَامٍ وَ لَيْسَ عَلَيْهِ الْقَضَاءُ.


بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج‏93، ص: 321


Ya zo cikin Fiqhu na Imam Ridha (A. S) cewa; 


" IDAN HAR BA ZAI IYA YIWUWA GA TSOHO KO MATASHI MAI 'DAUKE DA WATA LALURA KO MACE MAI CIKI, YAYI AZUMI SABODA QISHIRWA KO YUNWA KO KUMA TSORON CUTUWAR 'DANTA, TO, ABINDA KE KANSU DUKKANSU SHINE SAI SU SHA (ruwa) KUMA SUYI SADAQA GA KOWANNE "DAYA A KOWACCE RANA NA MUDUN ABINCI, KUMA BABU RAMUWA A KANSU. "


Wato hukuncin wadannan shine ciyarwa a kowacce rana don fansar wannan azumi da suka sha, kuma babu wata ramuwa a kansu bayan wucewar azumin. 


Sai dai kuma malamai na cewa hakan ba zai yiwu kawai bisa tunanin mutum ba, dole sai ya zama an sami tabbacin yin azumin zai iya cutarwa bisa umarnin likita ko kuma dai tabbaci ga wadanda abin ya shafi. 


Abin la'akari dai shine a kiyaye zato ko tsammanin hakan za ta faru ba tare da an gwada an tabbatar ba. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.


      (08137925034)


     18TH APRIL, 2021

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post