Dalilin da yasa Abu Huraira ya fi kowa yawan hadisai !!!


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


SA-IN-SA TSAKANINSA DA UMAR BN KHADDAB 


Abu Huraira na daya daga cikin jerin Sahabban Manzon Allah (S. A. W. W) wadanda suka karbi muslimci a shekara ta biyu kafin Hijrar Annabi (S. A. W. W), wato a shekarar FATAHUL-MAKKATA. 


Annabi (S. A. W. W) ya rasu shekara biyu ne bayan cin garin Makkah da yaqi, wanda hakan ke tabbatar mana cewa Abu Hurairata ya rayu dashi na tsahon shekaru biyu kenan.


Kaf cikin Sahabban Annabi (S. A. W. W) tun daga Muhajiruun har Ansaar ba a sami mai yawan hadisansa wadanda suka karade littafan muslimci ba. Ganin yawan hadisansa yasa mutane ke mamaki kan ya akayi wanda ya shekara biyu (2) da Annabi (S. A. W. W) yafi wadanda suka shekara ashirin da uku (23) yawan hadisai? 


Kamar ya san za ayi masa irin wannan tuhuma, saboda haka tun ta wuri ya bayyanarwa mutane hanya da dalilin da yasa ya tara hadisai masu yawa fiye da kowanne Sahabi. 


Ga dalilin nasa nan cikin hadisin dake biye. 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


(7354) - حدثنا علي: حدثنا سفيان: حدثني الزُهري: أنه سمعه من الأعرج يقول: أخبرني أبو هريرة قال: 

إنكم تزعمون أن أبا هريرة يكثر الحديث على رسول الله صلى الله عليه وسلم، والله الموعد، إني كنت امرأ مسكيناً، ألزم رسول الله صلى الله عليه وسلم على ملء بطني، وكان المهاجرون يشغلهم الصفق بالأسواق، وكانت الأنصار يشغلهم القيام على أموالهم، فشهدت من رسول الله صلى الله عليه وسلم ذات يوم، وقال: (من يبسط رداءه حتى أقضي مقالتي، ثم يقبضه، فلن ينسى شيئاً سمعه مني) 



Aliyu ya bamu labari, Sufyan ya bamu labari, Zuhriy ya bani labari : Cewa ya ji shi daga A'araj yana cewa; Abu Hurairata ya bani labari yace; 


" LALLE KUNA RIYAWA CEWA ABU HURAIRA YA YAWAITA HADISAI DAGA MANZON ALLAH (S. A. W. W), ALLAH SHAIDA NE. LALLE NI NA KASANCE MUTUM MISKINI, INA LAZIMTAR MANZON ALLAH (S. A. W. W) CIKINA BABU KOMAI (with empty stomach), KUMA MUHAJIRAI SAMMAKONSU ZUWA KASUWA NA SHAGALTAR DASU, SU KUMA ANSAR TSAYUWA KAN DUKIYARSU NE KE SHAGALTAR DASU. 


SAI WATA RANA NA KASANCE TARE DA MANZON ALLAH (S. A. W. W), SAI YACE; 


" WANENE (daga cikinku) ZAI SHIMFIDA MAYAFINSA (a qasa) HAR SAI NA QARE MAGANA TA SANNAN YA NADE SHI, BA ZAI MANCE WANI ABU DA YAJI DAGA GARE NI BA ?"


(Abu Huraira yace); " SAI NA SHIMFIDA MAYAFINA HAR SAI DA YA QARE MAGANARSA SANNAN NA NADE, TUN DAGA NAN BAN QARA MANCE ABINDA YA FADA BA ."


(An cire wannan qarashen maganar, amma in kuka duba hadisin a lambar dana baku cikin littafin da ku gani insha Allah) 


(SAHIHUL-BUKHARI, KITABUN RIQO GA LITTAFIN ALLAH, BABIN LALLE HUKUNCIN ANNABI YA KASANCE A BAYYANE, HADISI MAI LAMBA 7354)



Na ji mutane da dama na cewa Abu Huraira fa maqaryaci ne, domin wai har Umar ya taba yi masa barazanar bulala in bai rage irin wannan qaryar tasa ba. 


To, ni dai ban gani ba, amma dai naga inda Umar Bn Khaddab ke zargarsa da tara dukiyar haram har ma sai da suka yi misayar yawu (verbal exchange) .


Ga maganar nan kamar haka; 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼



وحين وليّ أبو هريرة البحرين ادّخر مالا، من مصادره الحلال، وعلم عمر فدعاه الى المدينة.. ولندع أبو هريرة يروي لنا ما حدث بينهما من حوار سريع: " قال لي عمر: يا عدو الله وعدو كتابه، أسرقت مال الله..؟؟ قلت: ما أنا بعدو لله ولا عدو لكتابه،.. لكني عدو من عاداهما.. ولا أنا من يسرق مال الله..! قال: فمن أين اجتمعت لك عشرة آلاف..؟؟ قلت: خيل لي تناسلت، وعطايا تلاحقت.. قال عمر: فادفعها الى بيت مال المسلمين"..!! ودفع أبو هريرة المال الى عمر ثم رفع يديه الى السماء وقال: اللهم اغفر لأمير المؤمنين"


Yayin da aka nada shi Gwamnan Bahrain ya tara dukiyarsa ta hanyoyinsa na halal. Da Umar ya ji sai ya aika masa yazo Madinah. Abu Hurairata ya cigaba da bamu labarin abinda ya faru tsakaninsu. 


Sai Umar yace min; 


" YAA KAI MAQIYIN ALLAH KUMA MAQIYIN LITTAFINSA, KA SACI DUKIYAR ALLAH ?


Sai nace masa, " Ni ba maqiyin Allah bane kuma ba maqiyin littafinsa ba, amma dai ni maqiyi ne ga wanda ya qi su, kuma ni ban sace dukiyar Allah ba !"


Sai (Umar) yace; 


" TO, TA INA KA TARA DUBU GOMA (10,000) !"


Nace, " Dokina (horse 🐴 ) ne da yake aiki kuma yana zuwa min da kudi ."


Sai (Umar) yace ;


" KA MAYAR DASU CIKIN BAITIL-MALIN MUSULMI !"


Sai Abu Hurairata ya mayarwa Umar dukiyar. Sannan ya daga hannayensa zuwa sama yana cewa; 


" Yaa Allah ! Ka gafartawa Sarkin muminai !"


(HAYATUS-SAHABA) 


Wannan shine abinda ya faru tsakaninsu, duk da cewa ga abinda Abu Hurairata ya fadawa Umar amma ya qi ya gaskata shi, kuma ya tilasta shi ya mayar da wannan dukiya. 


To, ban dai san hujjar da Umar ya dogara da ita wajen qin yarda da maganar Abu Huraira ba, ko dai wannan batu da mutane ke yi ne na cewa Umar yayi masa barazanar Bulala saboda qaryarsa ?


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.


         (08137925034)


12th April, 2021/ 1st Ramadan, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post