Da yawa cikin Sahabbai Na ba za su qara ganiNa ba, in Na barsu - Jawabin Manzon Allah (S) ga sahabbansa




@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

JAWABIN ANNABI (S. A. W. W) GA SAHABBANSA 

Wannan al'amari zai zama abin tsoro abin firgici ga dukkan wani muminin daya rayu da Manzon Allah (S. A. W. W), domin duk wanda bai ga Manzon Allah (S. A. W. W) bayan mutuwarsa ba, to, zamantakewarsu ta dashi a duniya ba ta amfanar dashi da wani abu ba.

Wannan magana ta fito ne daga bakin Manzon Allah (S. A. W. W) wanda Ummus-Salamata ta bayar da labari a kansa. Ga yadda abin yakasance .

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

25894- حَدَّثَنَا أَبُو مُعَاوِيَةَ ، قَالَ : حَدَّثَنَا الْأَعْمَشُ ، عَنْ شَقِيقٍ ، عَنْ أُمِّ سَلَمَةَ ، قَالَتْ : دَخَلَ عَلَيْهَا عَبْدُ الرَّحْمَنِ بْنُ عَوْفٍ ، قَالَ : فَقَالَ : يَا أُمَّهْ ، قَدْ خِفْتُ أَنْ يُهْلِكَنِي كَثْرَةُ مَالِي ، أَنَا أَكْثَرُ قُرَيْشٍ مَالًا ، قَالَتْ : يَا بُنَيَّ ، فَأَنْفِقْ ، فَإِنِّي سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ : " إِنَّ مِنْ أَصْحَابِي مَنْ لَا يَرَانِي بَعْدَ أَنْ أُفَارِقَهُ " , فَخَرَجَ ، فَلَقِيَ عُمَرَ ، فَأَخْبَرَهُ ، فَجَاءَ عُمَرُ ، فَدَخَلَ عَلَيْهَا ، فَقَالَ لَهَا : بِاللَّهِ مِنْهُمْ أَنَا ؟ فَقَالَتْ : لَا ، وَلَنْ أُبْلِيَ أَحَدًا بَعْدَكَ .

Imam Ahmad yace, Baban Mu'awiyata ya bamu labari yace, A'amashu ya bamu labari daga Shaqeeq, daga Ummus-Salamata tace; " Abdurrahman Bn Auf ya shigo gare ni sai yace; 

" Yaa mahaifiyata ! Ni fa ina jin tsoro kada yawan dukiyata ya halakar dani, domin nine nafi dukkan Quraishawa yawan dukiya ."

Sai tace, " Yaa dana ! Ka ciyar, domin ni naji Manzon Allah (S. A. W. W) yana cewa; 

" LALLE DAGA CIKIN SAHABBAINA AKWAI WANDA BA ZAI GANNI BA BAYAN NA RABU DASHI ."

Sai ya fita, sai ya hadu da Umar, ya bashi labarin (abinda Ummus-Salamata tace masa dangane da fadin Manzon Allah (S. A. W. W)). Sai Umar yazo, ya shiga gareta sannan yace mata; 

" DAN ALLAH INA DAGA CIKINSU ?" 

Sai tace; " A'A, AMMA BA ZAN QARA BAYYANARWA WANI BA BAYANKA ."


(MUSNAD AHMAD, HADISI MAI LAMBA 25,894))

                   DARASI 
                 ----------------

Cikin wannan hadisi akwai darusa masu yawa, amma dai ga wasu daga ciki kamar haka :-

(1)- Ashe cikin Quraishawa Abdurrahman Bn Auf shi yafi kowa dukiya ba kamar yadda wasu ke kama sunan wani cewa wai shi yafi kowa dukiya ba. 

(2)- Annabi (S. A. W. W) ya tabbatar da cewa cikin Sahabbansa akwai wanda iya ganinsa dashi kawai a duniya ne, amma in sun rabu daga duniya sun rabu kenan har abada.

(3)- Umar ya tsargu da jin wannan magana har ya nemi sanin matsayinsa ko shi ma na daga cikin wadanda ba za su qara ganin nasa (S. A. W. W) ba. 

(4)- Ummus-Salamata (R. A) ta bayar da amsa kan abinda bata sani ba, domin kuwa cikin hadisin ba a nuna cewa Annabi (S. A. W. W) ya sanar da ita sunayensu ba ballantana ace za ta iya cewa wane na ciki ko banda wane ciki. 

                     D.S

Daga wakilanmu na Bauchi zone. 

Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.

         (08137925034)

     15TH APRIL, 2021

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post