Sun Ji Tsoron Tunkarar Gaskiyar Sheikh Abduljabbar Ne -Inji Sheikh Adamu Tsoho Jos.



Gangamin 'yan maja


Maganar 'Ƴan Maja nake yi, zuwa yanzu 'Ƴan Maja sun 'majance' domin sun razana sun san cewa in an zo anyi wannan muƙabala to za a sha kunya ne, daman a cikin kunya suke. Don haka yanzu suna magana cewa wai anje kotu kuma kotun ta bada "Izini" kada ayi wannan muƙabala. To, ko ayi muƙabala ko kada ayi muƙalaba ita fa gaskiya sunan ta gaskiya ce, ba a nasara akan gaskiya. Gaskiya da mai gaskiya ba a taba nasara akan su. Amma ƙaryan mai ƙarya fa ? Kuma an ce Ramin mai ƙarya ƙurarriya ce don haka malaman Maja Ramin su ya ƙure. 


Sai ya zama an sa ranar Lahadi gaskiya zata tunkari ƙarya, to kuma daman tun kan a je ko ina mun san wannan mutane ba zasu iya ba. Idan kana maganar shi'a ne kaje ka duba tarihi ba a taba muƙabala  da ɗan shi'a anyi nasara akan sa ba. Domin wanda yayi riko da Alkur'ani da Ahlulbait wallahi ba za a taba nasara akan shi ba, saboda yana da hujja a cikin littattafan da ba zaki iya lada shi ba. 


Wannan bawan Allah Sheikh Abduljabbar ƙoƙari yake yi ya kare martabar Manzon Allah (Saww), kullum kokari yake ya farkar da mutane ce wa wannan littafan da ake cewa sahihai cewa akwai abin da suke faɗa akan Annabi kuma cin mutuncin sa ne. Wanda kwanan nan shugaban kasar Faransa ya fito ƙarara yana zagin musulmai yana cin zarafin Manzon Allah ƙarara. Kuma duk abin da ya faɗa yana cikin Bukhari da Muslim.


A lokacin ana ta zanga-zanga an ƙauracewa kayan Faransa hakan ya girgiza kasar Faransa sai ya kira manya-manyan ƴan kasar Faransa yayi magana aka nuna 'Live' a duniya yana basu hakuri yana cewa, lallai yanzu tattalin arziki kasar Faransa ya girgiza saboda wani hali da barazana da ake fuskanta, amma ba ba zai taba bawa musulmai hakuri ba, abin da ya faɗa kenan. Ya ce in musulmai suna so ya basu haƙuri to, suje su soma Muzahara  akan wani sahabi ya ambaci sunan sa saboda shi wannan sahabi yace Manzon Allah bai da hankali.


Wannan bawan Allah ya fito ya shelantawa duniya ce wa, wannan abin da kuke faɗa ba daidai bane, to ba sai ku fito ku zauna ku fada ce wa, ba daidai bane in gyara ne da gaske. To, tsoron me kuke ji? Wannan tsoron nasu sun san ba a kan gaskiya suke ba. Shi yasa kullum maganar su shine kada ku Saurari wa'azin 'Ƴan Shi'a kada ku saurari 'Ƴan Shi'a, saboda me ! Duk wanda ya saurari wa'azin gaskiya zai bi gaskiya ko ba zai bi ba ? Shi yasa suke tsoron azo ayi wannan muƙabala ɗin. 


Naji wani "Baƙidahume" shugaban wata ƙungiya, saboda wani ma abin bakin ciki wai ana ce mai shugaban malamai. Ya dubi wannan bawan Allah Sheikh Abduljabbar yace mai "Bama Guje Ne" yace mai wai "Jahili". Mutumin akan sa Asalinsa akasan gidansu, ina da 'Littattafansa' wanda Mallam Nasiru Abduljabbar ya rubuta da hannun sa, wanda shi wannan mai magana ko da rubutun Hausa banga littafin da ya rubuta da hannun sa ba, ballantana ayi gamana na larabci.


Saboda jahilci da wauta akan munbirin Annabi kazo kana cewa wani mutum 'Bamaguje' kana tsine mishi, a shari'ar Musulunci hukunci mafi hatsari shine hukuncin jefa wa mutum kallar 'Ridda' to, wannan abin yana da hadari mai girman gaske, musamman in an tabbatar mutum da hankalinsa yayi sannan yana sane yayi. Idan kun ce Malam Abduljabbar zagi yake sai ku zo a zauna ayi magana a tantance kai gaskiya. 


Mallam Zakzaky (H) shima yayi haka a lokacin da aka ce shi'a yake yi su sun balle, akan mimbari Mallam (H) yace ku zo muyi tsinuwa tsakanin ni da ku akan abin da nake yi in ba gaskiya bane yace  Allah in ba gaskiya bane nake yi, ka bayyanar wa mutane cewa ba daidai bane. Idan kuma abin da nake yi shine daidai shi ka yarda dashi, abin da wannan mutane suke ba shi bane daidai baka yarda  da shi ba ka rusa nasu. Tambaya anan shine akwai 'ƴan tawayiya anan ? Da yawa ma mutane basu san 'Yan tawayiya ba.


Wanda yake kan gaskiya baya tsoron ayi muƙabala da shi, to ya yanzu zaku ce kada ayi kuƙabala da shi ! To, in dai akan gaskiya kuke magana ya zaku bar shi ya cigaba da ɓatar da mutane, ashe kuma kuna da laifi kenan, haƙƙi ne a hannun ku kuce ya daina. Ƙin wannan yin muƙabala ya nuna cewa wannan mutane ba a kan gaskiya kuke ba, ya nuna abin da wannan bawan Allah Sheikh Abduljabbar gaskiyar yake, kuma yana ƙoƙari ya kare martabar Manzon Allah (Saww) ne. 


Jawabin Sheikh Adamu Tsoho Jos wanda yayi jiya 6-Jan-2021 a wajen Mauludin Imam Aliyu (As), Wanda Dandalin Matasa Garin Jos suka gabatar. 


   -Idishia Jos


#FreeZakzaky. 

@Media Forum Jos.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post