KO KUN SAN MAFIYA HASARA RANAR ALQIYA ???

 





@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


SUNE DAI WADANDA SUKA JUYA BAYA A BAYAN WAFATIN MANZON ALLAH (S. A. W. W) 


Bin son zuciya da girman kai ba qaramin bala'i bane ga mai yinsa, domin babu inda za su  kai shi a qarshe sai wutar Jahannamah.


Kuma kun san duk wani mai bin son zuciyarsa yana zaton hakan wani abin kirki ne, shi yasa ma ba zai taba bari ba, kuma sai kaga 'yan'uwa suna goya masa baya a matsayin abinda yake yi ko yayi din shine daidai. 


Mu dan leqa wadannan ayoyi muji tare da ganin yadda makomarsu take kasancewa.  Allah (S. W. A) na cewa; 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


" قُلۡ هَلۡ نُنَبِّئُكُم بِٱلۡأَخۡسَرِينَ أَعۡمَٰلًا .٣٠١


" KACE " SHIN, MU BA KU LABARI GAME DA MAFIFITA HASARA GA AYYUKA ? (wato wadanda suka yi aiki amma aikin nasu ya tashi a banza sakamakon munana ayyukansu a qarshe ). 


.

 وأخرج ابن مردويه عن أبي الطفيل قال: سمعت علي بن أبي طالب، وسأله ابن الكواء فقال: مَنْ {هل ننبئكم بالأخسرين أعمالاً}؟ قال: فجرة قريش.


Ibn Mardawaihi ya fitar daga baban 'Dufail yace : Na ji Aliyu Bn Abiy 'Dalib (A. S) Ibn Kawwa'a ya tambaye shi yace; Wanene, " SHIN, MU BA KU LABARI GAME DA MAFIFITA HASARAR AYYUKA  ?" Yace; 


" Fajiran Quraishawa ne  ." (Wato Quraishawannan da suka bijire Annabi (S. A. W. W) a halin rayuwarsa dana bayan rayuwarsa). 


Cikin wata riwayar kuma yace, 



وأخرج عبد الرزاق والفريابي وابن المنذر وابن أبي حاتم وابن مردويه من طريق، عن علي أنه سئل عن هذه الآية {قل هل ننبئكم بالأخسرين أعمالاً} قال: لا أظن إلا أن الخوارج منهم.


Abdurrazaq da Faryabi da Ibn Munziri da Ibn Abiy Haateem da Ibn Mardawaihi sun fitar daga wata hanya, daga Aliyu cewa an tambaye shi game da wannan ayar, 


" KACE, " SHIN, MU BA KU LABARI GAME DA MAFIFITA HASARAR AYYUKA ? " Yace, 


" Ba na zato face lalle Khawarijawa na daga cikinsu. "


    (Tafsir Durrul-Mansur na Suyudi)


Idan muka duba riwaya ta biyu za muga cewa cigaban ta farko ce, domin cikin na farko yace Fajiran Quraishawa ne. A na biyu kuma yace Khawarijawa na daga cikinsu. 


Wato sune Quraishawa da suka juya baya da kuma Khawarijawa da suka rufa musu baya. 


Sai Allah (T) ya cigaba da cewa, 



 ٱلَّذِينَ ضَلَّ سَعۡيُهُمۡ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا وَهُمۡ يَحۡسَبُونَ أَنَّهُمۡ يُحۡسِنُونَ صُنۡعًا . ٤٠١


" SUNE (dai) WADANDA AYYUKANSU SUKA LALACE CIKIN RAYUWAR DUNIYA (tun kafin su mutu), SU KUWA SUNA TSAMMANI CEWA SUNA AIKATA AIKIN QWARAI NE (da suke tunanin ai bai kamata ace yaro ya jagoranci manya Dattawa ba). 


 أُوْلَٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بِـَٔايَٰتِ رَبِّهِمۡ وَلِقَآئِهِۦ فَحَبِطَتۡ أَعۡمَٰلُهُمۡ فَلَا نُقِيمُ لَهُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ وَزۡنٗا ٥٠١ 


" TO, WADANNAN SUNE WADANDA SUKA KAFIRTA DA AYOYIN UBANGIJINSU DA KUMA HADUWA DA SHI, SAI AYYUKANSU (wadanda suka yi na alkhairi) SUKA BACI. (Saboda haka) KO MA'AUNINSU MA BA ZA MU TSAYAR (don auna ayyukansu ba) RANAR ALQIYAMA. "



ذَٰلِكَ جَزَآؤُهُمۡ جَهَنَّمُ بِمَا كَفَرُواْ وَٱتَّخَذُوٓاْ ءَايَٰتِي وَرُسُلِي هُزُوًا  ٦٠١ 


" WANCAN NE,  SAKAMAKONSU SHINE JAHANNAMAH SABODA KAFIRCEWA DA SUKA YI, KUMA SUKA RIQI AYOYINA DA MANZANNINA ABIN IZGILI. "


Suna cewa a rasa wanda za a dora mana sai talaka marar kudi kuma yaro? 


    (KAHFI -103-106)


Wannan dai tunatarwa ce, Allah yasa mu fahinci abinda ake karantar damu cikin wadannan ayoyi za kuma daukar darussa daga cikinsu. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.


        (08137925034)


24th March, 2021/  11th Sha'aban, 1442.


Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post