Cigaba... SHIN KOKUN SAN WANENE SHAIKH ZAKZAKY??? Na 7


         BABI NA FARKO

TARIHIN RAYUWAR SHAIKH IBRAHIM ZAKZAKY A TAQAICE.

Karatunsa na Addini :


Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya taso ne a gida na ilimi da addini, gidansu gidan malamai ne masu riqo da addini da koyarwar musulunci, dan haka Shaikh ya taso ne da karatun addini wanda ake kira “Karatun Zaure”. Ya fara karatun Alqur’ani ne a gaban mahaifinsa tun yana xan shekara huxu da haihuwa, ya kuma fara karatun ilimin Nahwu ne a wajan kakarsa Malama Hajara, wacce ake wa laqabi da “Mai Karatu”.


Tun Shaikh yana qarami ya yi karatun addini mai zurfi, domin ya kasance yana haddace duk karatun da aka yi masa, har ma yana haddace karatuttukan na gaba da shi da aka yi a gabansa. Ya yi karatu a gaban manyan malamai da dama a birnin Zariya. Kusan ya karanta duk wani littafin addini da ake karantawa bisa tsarin karatun zaure, kuma ya karanta dukkanin fannonin ilimi da ake karantawa a Zaure, kama daga karatun Alqur’ani, Fiqhu, Usul, Hadisi, Tarihi, Luga, Sarf, Aroud, Nahwu da sauransu.


Ya yi waxannan karatuttuka ne a gaban mahaifinsa Malam Yaqubu, da kakarsa Malama Hajara Mai Karatu, da fitattun gidajen ilimi na Zariya, daga ciki ya yi karatu a gidan Ladanai, da wajan Malam Sani Abdulqadir Fateh, da Malam Sani Na’ibi, da Malam Isa Kwarbai, da Malam Ibrahim Nakakaki, da Malam Aminu na Madaka da sauransu.


Sannan ya zurfafa karatun fannonin ilimi a zamansa na Kano a gaban Shaikh Nasiru Kabara, da Shaikh Isa Waziri (babban limamin Kano), da Malam Nuhu limamin Unguwar Yola, da Malam Datti Ahmad (qwararren malamin Luga da Adabi), da Malam Ibrahim Babarbare, da kuma Shaikh Abdur-Ra’uf Usman (wani malami xan qasar Masar). Duk waxannan masana Shaikh (H) ya yi karatuttukan fannonin addini ne a wajansu.


Shaikh Ibraheem Zakzaky ya ci gaba da halartar gaban manyan masana da malamai yana zurfafa bincike akan mas’alolin addini da faxaxa Bahasi a qasasen waje. Misali; ya yi karatu na tsawon lokaci a qasar Ghana, a gaban wani babban masani xan qasar Iran Sayyid Tabataba’i. Sannan tun a shekarar 2000 har zuwa 2015, kusan duk shekara yana zuwa qasar Iran na tsawon wata biyu dan zurfafa karatu a gaban manyan malamai da masana fannonin ilimi daban-daban. Yana karatu mai zurfi a fannonin nazari da bahasi akan wasu mas’alolin addini, tare da zurfafa karatu a fannonin ilimin Falsafa, Irfani, Manxiq, Usoul, Shari’a, da sauransu.

Zamu Cigaba...


Daga Wakilinmu:

Auwal M Tukur

09072712469

Daga littafin da cibiyar wallafa jawaban Sheikh Zakzaky ta wallafa mai Suna "SHAIKH ZAKZAKY IKON ALLAH".

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post