Wasiyyar Imam Musa Bn Jafar (A.S) ga Hishaam Bn Hakaam cikin ayoyin Alqur'ani (1)



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @



MASU SAURARON MAGANA SUBI MAFI KYAWUNTA SUNE SHIRYAYYU 



Imam Musa Alkazeem (A. S) yayi wasiyya da Hishaam Bn Hakaam game da amfanin hankalin da Allah ya bawa bayinsa, yin aiki dashi shine shiriya ba wai rashin amfani dashi ba. 


Ga wasiyyar nan kamar haka; 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


 ف، تحف العقول‏ وَصِيَّةُ مُوسَى بْنِ جَعْفَرٍ ع لِهِشَامِ بْنِ الْحَكَمِ وَ صِفَتُهُ لِلْعَقْلِ قَالَ ع


Ya siffanta masa hankali yace, 


" Yaa Hishaam ! Lalle Allah (S. W. A) yayi bushara ga ma'abota hankali da fahinta cikin littafi yace; KAYI BUSHARA GA BAYI WADANDA SUKE SAURARON MAGANA (idan sun ji ta) SAI SUBI MAFI KYAWUNTA (ta daidai ba ta qarya ko sharri ba), TO, WADANNAN SUNE WADANDA ALLAH YA SHURYAR DASU, KUMA WADANNAN SUNE MASU HANKALI ."


Kenan duk wanda ba zai tsaya ya saurari magana sannan yabi ta gaskiya ba, to, ba shiryayyen mutum bane kuma ba me hankali bane komai rawaninsa da gemunsa. 


 يَا هِشَامُ إِنَّ اللَّهَ تَبَارَكَ وَ تَعَالَى بَشَّرَ أَهْلَ الْعَقْلِ وَ الْفَهْمِ فِي كِتَابِهِ فَقَالَ‏ فَبَشِّرْ عِبادِ الَّذِينَ يَسْتَمِعُونَ الْقَوْلَ فَيَتَّبِعُونَ أَحْسَنَهُ أُولئِكَ الَّذِينَ هَداهُمُ اللَّهُ وَ أُولئِكَ هُمْ أُولُوا الْأَلْبابِ‏[58].



" Yaa Hishaam Bn Hakaam ! Lalle Allah mai girma da daukaka ya kammalawa mutane hujjoji da hankali sannan ya yalwata musu da bayani kuma ya nuna musu akan RububiyyarSa da dalilanSa (T) yace; " KUMA ABIN BAUTARKU ABIN BAUTANE GUDA 'DAYA ☝🏼, BABU WANI ABIN BAUTA FACE SHI, MAI RAHMA MAI JIN QAI. LALLE CIKIN HALITTAR SAMMAI DA QASSAI DA YADDA DARE DA RANA KE SASSABAWA DA KUMA JIRGIN NAN DAKE YAWO CIKIN KOGI DA ABINDA KE AMFANAR DA MUTANE, DA KUMA ABINDA ALLAH YA SAUKAR NA RUWA DAGA SAMA YA RAYAR DA QASA DASHI BAYAN MUTUWARTA (bayan qeqashewarta) , SANNAN YA WATSA CIKINTA DAGA KOWACCE (irin) DABBA, KUMA YAKE SARRAFA ISKA DA GIRGIJE SUNA HORARRU TSAKANIN SAMA DA QASA, AYOYI NE (abin lura) GA MUTANE MASU HANKALI ." 


7 يَا هِشَامَ بْنَ الْحَكَمِ إِنَّ اللَّهَ جَلَّ وَ عَزَّ أَكْمَلَ لِلنَّاسِ الْحُجَجَ بِالْعُقُولِ وَ أَفْضَى إِلَيْهِمْ بِالْبَيَانِ وَ دَلَّهُمْ عَلَى رُبُوبِيَّتِهِ بِالْأَدِلَّةِ فَقَالَ‏ وَ إِلهُكُمْ إِلهٌ واحِدٌ لا إِلهَ إِلَّا هُوَ الرَّحْمنُ الرَّحِيمُ إِنَّ فِي خَلْقِ السَّماواتِ وَ الْأَرْضِ وَ اخْتِلافِ اللَّيْلِ وَ النَّهارِ وَ الْفُلْكِ الَّتِي تَجْرِي فِي الْبَحْرِ بِما يَنْفَعُ النَّاسَ وَ ما أَنْزَلَ اللَّهُ مِنَ السَّماءِ مِنْ ماءٍ فَأَحْيا بِهِ الْأَرْضَ بَعْدَ مَوْتِها وَ بَثَّ فِيها مِنْ كُلِّ دَابَّةٍ وَ تَصْرِيفِ الرِّياحِ وَ السَّحابِ الْمُسَخَّرِ بَيْنَ السَّماءِ وَ الْأَرْضِ لَآياتٍ لِقَوْمٍ يَعْقِلُونَ‏[59


(1) الزمر: 18.


(2) البقرة: 164.


بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج‏1، ص: 133



" Yaa Hishaam ! Lalle Allah wanda ya girma ya daukaka ya sanya dalilai (hujjoji) akan saninSa domin su suyi tunani. Yace; " KUMA YA HORE MUKU DARE DA YINI DA RANA DA WATA DA TAURARI SUNA HORARRU BISA UMARNINSA (al'amarinSa). LALLE CIKIN HAKA AKWAI AYOYI (abin lura) GA MUTANE MASU HANKALI ."


Kuma yace, " HAAMEEM ! INA RANTSUWA DA LITTAFI BAYYANANE (Qur'ani). LALLE MUN SANYA SHI (Qur'ani) ABIN KARANTAWA CIKIN HARSHEN LARABCI DOMIN KO ZA KU HANKALTA. "


Kuma yace, " YANA DAGA CIKIN AYOYINSA YAKE NUNA MUKU WALQIYA BISA TSORO DA KWADAYI (kuna jin tsoro idan kun ganta , kuma kuma kwadayin samun ruwa in kun ganta), KUMA YANA SAUKAR DA RUWA DAGA SAMA YA RAYAR DA QASA DA SHI BAYAN MUTUWARTA (yadda za kuga tsirrai koraye sun cikata da ban sha'awa ga kuma amfanin dabbobinku) , LALLE CIKIN HAKA AKWAI AYOYI (abin lura) GA MUTANE MASU HANKALI ."


7 يَا هِشَامُ قَدْ جَعَلَ اللَّهُ جَلَّ وَ عَزَّ دَلِيلًا عَلَى مَعْرِفَتِهِ بِأَنَّ لَهُمْ مُدَبِّراً فَقَالَ‏ وَ سَخَّرَ لَكُمُ اللَّيْلَ وَ النَّهارَ وَ الشَّمْسَ وَ الْقَمَرَ وَ النُّجُومُ مُسَخَّراتٌ بِأَمْرِهِ إِنَّ فِي ذلِكَ لَآياتٍ لِقَوْمٍ يَعْقِلُونَ‏[61] وَ قَالَ‏ حم وَ الْكِتابِ الْمُبِينِ إِنَّا جَعَلْناهُ قُرْآناً عَرَبِيًّا لَعَلَّكُمْ تَعْقِلُونَ‏[62] وَ قَالَ‏ وَ مِنْ آياتِهِ يُرِيكُمُ الْبَرْقَ خَوْفاً وَ طَمَعاً وَ يُنَزِّلُ مِنَ السَّماءِ ماءً فَيُحْيِي بِهِ الْأَرْضَ بَعْدَ مَوْتِها إِنَّ فِي ذلِكَ لَآياتٍ لِقَوْمٍ يَعْقِلُونَ‏[63].


(1) الفرقان: 62.


(2) النحل: 12.


(3) الزخرف: 1، 2.


(4) الروم: 24.


بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج‏1، ص: 134


Daga cikin wadannan ayoyi za musan cewa ashe dai shi hankali an bamu shi ne don mu riqa amfani da shi wajen daukar darasi da sanin ya kamata. To, me yasa mutane ba sa yin tunani cikin maganar da wasu maqiya ke yi don tantance maganar qarya data gaskiya ?


Ko kuma dai so suke su nuna cewa su mahaukata ne marar sa hankali yadda ba sa iya gane gaskiya ?


ZA MU CIGABA INSHA ALLAH. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.


       (08137925034)


11th February, 2021/ 29th Jimada-Saaniy, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post