Tunatarwa: Nazari da hangen nesa kafin aikata kowane irin aiki


 TUNATARWA!!!

Mukan aikata ababe da dama a rayuwarmu, wanda daga baya muke nadamar hakan, nazari da hangen nesa kafin aikata kowane irin aiki, Yana taimakawa matuka wurin kaucewa hakan, karmu zamo cikin masu aikata aikin dana sani a kowane lokaci na rayuwarmu, tabbas idan muka zama hakan, to zamu kare rayuwarmu ne cikin nadama da kaico.


Mu zama masu daukar darasin rayuwa daga magabatanmu, domin duk abinda muke gani a yanzu to na sama damu sunyi irinsa ko makamancin sa, sannan dadewar su cikin duniya da fadi_tashi na rayuwa ya saka sun san ababe da daman gaske, harda wanda baka taba aikatawa ba.


Muna dama a rayuwa, Amma abin lura anan shine bawanda yakeda tabbaci na zaya wuce yau, kenan munada guarantee ne kawai da yanzun mu, tunda ita muka gani, kuma ita muke ciki a yanzu. Muyi anfani da lokacin mu wurin anfani da anfanar da al'umma da iya dan abinda Allah ya hore mana na daga rahamarsa, kar rudun duniya ya rinjayi zukatanmu da tunanikanmu.


Allah yasa mudace


✍️ Zarah A zamsarf

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post