Kyawawan ɗabi'un Sayyidah Fatima Salamullahi Alaiha !!!


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


BAN TABA GANIN MAI GASKIYAR MAGANA KAMARTA BA BAYAN BABANTA IN JI UMMUL-MUMINA A'ISHA


A dabi'u kyawawa ba a taba samun mace mai kyakkyawar dabi'a kamar Sayyidah Zahra (S. A) ba, duk wata mace mai kyawawan dabi'u bata kaita ba ko da kuwa wacece ita. 


A dabi'u ta gaji mahaifinta (S. A.W.W) ne, saboda haka ba za a sami kamarta ba sai dai mai koyi da ita. RIWAYOYI DAGA UMMUL-MUMINA A'ISHA 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


Ya zo cikin Manaqeeb na Ibn Shahr Aswaabi Hilyatu Abiy Nu'aim, da Musnad na Abu Ya'alah yace, A'isha tace;  المناقب لابن شهرآشوب حِلْيَةُ أَبِي نُعَيْمٍ وَ مُسْنَدُ أَبِي يَعْلَى قَالَتْ عَائِشَةُ :


" BAN TABA GANIN WANI MAI GASKIYAR MAGANA KAMAR FADIMATU BA BAYAN MAHAIFITA ."


مَا رَأَيْتُ أَحَداً قَطُّ أَصْدَقَ مِنْ فَاطِمَةَ غَيْرَ أَبِيهَا.An riwaito daga gare shi (mai riwaya ta sama) yace, wani abu ya kasance tsakaninsu, sai A'ishatu tace; 


" YAA MA'AIKIN ALLAH, KA TAMBAYETA DOMIN ITA BA ZA TAYI QARYA BA ."


وَ رَوَيَا أَنَّهُ كَانَ بَيْنَهُمَا شَيْ‏ءٌ فَقَالَتْ عَائِشَةُ يَا رَسُولَ اللَّهُ سَلْهَا فَإِنَّهَا لَا تَكْذِبُ.

Haqiqa Ada'u da Amruu Bn Dinar sun riwaito hadisai guda biyu kan haka. 


وَ قَدْ رَوَى الْحَدِيثَيْنِ عَطَاءٌ وَ عَمْرُو بْنُ دِينَارٍ.Hasanul-Basari kuma yace, " BAI KASANCE CIKIN WANNAN AL'UMMA MAI YAWAN IBADA KAMAR FADIMATU BA, TA KASANCE TANA TSAYUWA HAR SAI DUGADUGANTA SUN KUMBURA ."الْحَسَنُ الْبَصْرِيُ‏ مَا كَانَ فِي هَذِهِ الْأُمَّةِ أَعْبَدَ مِنْ فَاطِمَةَ كَانَتْ تَقُومُ حَتَّى تَوَرَّمَ قَدَمَاهَا.


Manzon Allah (S. A. W. W) yace mata, 


" WANNE ABU NE MAFI ALKHAIRI GA MACE ?" Tace, 


" Kada taga namiji, ita ma kada namiji ya ganta ." Sai (Manzon Allah) ya jawota a jikinsa yace, 


" ZURIYA CE SASHENTA DAGA SASHE ."


وَ قَالَ النَّبِيُّ ص لَهَا أَيُّ شَيْ‏ءٍ خَيْرٌ لِلْمَرْأَةِ قَالَتْ أَنْ لَا تَرَى رَجُلًا وَ لَا يَرَاهَا رَجُلٌ فَضَمَّهَا إِلَيْهِ وَ قَالَ‏ ذُرِّيَّةً بَعْضُها مِنْ بَعْضٍ‏.


بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج‏43، ص: 85


Wadannan na daga cikin dabi'unta (S. A), kuma ga dukkan mai sonta da gaske dole yayi koyi da ita, don hakanne zai tabbatar da soyayyar gaskiya gare ta. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.


       (08137925034)


6th February, 2021, 24th Jimada-Saaniy, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post