Duk wanda ya tara Gashi ba ya taje shi, Allah (T) zai taje masa shi da matajin wuta a ranar Alkiyama !


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


SHI KUMA ZAMA DA TUFAFI SAI DA TSABTACEWA 


Shi gashi na daya daga cikin baiwar da Allah ke yiwa wasu daga cikin bayinsa don ya qara kyautata musu kyawunsu. Ba za ka taba samun kyawawan mutune biyu masu bambanci a yawan gashi sannan kace mai yawan gashin bai fi kyau fiye da mai qarancinsa ba. 


Akwai wanda zai yi sha'awar ajiye gashi a kansa amma sakamakon rashinsa sai ka riqa ganinsa a kullum tamkar wanda aka kifa masa qwarya a kansa.


A wannan zamani musamman cikin matasa za ka tarar da yawa suna yawan tara gashi (suma) a kansu fiye da yadda ake yi a shekarun baya. Ko menene sirrin hakan ?


Umarni masu yawa sun zo cikin wannan hadisi dake biye biye kamar haka; 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


ب، قرب الإسناد عَنْ هَارُونَ عَنِ ابْنِ صَدَقَةَ عَنِ الصَّادِقِ عَنْ أَبِيهِ ع قَالَ: مَنِ اتَّخَذَ نَعْلًا فَلْيَسْتَجِدْهَا وَ مَنِ اتَّخَذَ ثَوْباً فَلْيَسْتَنْظِفْهُ وَ مَنِ اتَّخَذَ دَابَّةً فَلْيَسْتَفْرِهْهَا وَ مَنِ اتَّخَذَ امْرَأَةً فَلْيُكْرِمْهَا فَإِنَّمَا امْرَأَةُ أَحَدِكُمْ لُعْبَةٌ فَمَنِ اتَّخَذَهَا فَلَا يُضَيِّعْهَا وَ مَنِ اتَّخَذَ شَعْراً فَلْيُحْسِنْ إِلَيْهِ وَ مَنِ اتَّخَذَ شَعْراً فَلَمْ يَفْرُقْ فَرَقَهُ اللَّهُ‏ يَوْمَ الْقِيَامَةِ بِمِنْشَارٍ مِنْ نَارٍ[3].


بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج‏76، ص: 298


Isnadi makusanci daga Haruuna, daga Ibn Sadaqata, daga Sadeeq, daga babansa (A. S) yace:


" DUK WANDA YA RIQI TAKALMI 👟 TO YA SABANTA SHI (ya zama mai kyau ne ba wanda zai zubar masa da mutunci ba), KUMA WANDA YA RIQI TUFAFI TO YA RIQA TSABTACE SU (don haka Allah ya umarci Manzonsa (S. A. W. W) da shi), KUMA WANDA YA RIQI DABBA TO YA RIQA FARRANTA MATA (ta hanyar ciyar da ita ba bisa zaluntarsa ba). KUMA WANDA YA RIQI MACE (a matsayin matar aurensa ) TO YA KARRAMATA, DOMIN MATAR 'DAYANKU ABOKIYAR JIN DADI CE . DUK WANDA YA RIQETA TO, KADA YA TOZARTATA. 


KUMA WANDA YA RIQI (tara) GASHI TO, YA KYAUTATA SHI, KUMA WANDA YA TARA GASHI AMMA BA YA TAJE SHI, ALLAH ZAI TAJE MASA SHI DA MATAJIN WUTA RANAR ALQIYAMA ."


Ashe dai barin gashi mai yawa a ka ba laifi bane kuma ba baqon al'amari bane, sannan ba qazanta bane kamar yadda wasu ke cewa. 


An fi samun masu barin gashinsu da yawa yanzu cikin mabiyan Sayyid Zakzaky (H) sakamakon ganin yadda 'ya'yansa (H) ke bari. 


Saboda haka masu barin gashi da yawa a kansu su kasance masu tsabtace su kamar dai yadda 'ya'yan Sayyid Zakzaky (H) ke yi.


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.


       (08126385470)


1st February, 2021/ 19th Jimada-Saaniy.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post