'Yan Bindiga Sun Kashe Manoma Bakwai a garin Babban Rami ta Jihar Neja


 

Daga

Wakilin mu Auwal M Tukur

4/12/2020


Wasu ‘yan bindiga sun kashe manoma bakwai tare da jikkata wasu da dama a Babban Rami, da ke karamar hukumar Mashegu a jihar Neja.


A rahoton da ya zo Mana shine cewa, manoman suna kwaso kayan gonar su ne domin su kawo kayan cikin. A yayin da wasu 'yan bindiga dauke da muggan makamai suka bude musu wuta ba kakkautawa, inda a nan take suka kashe kimanin mutane bakwai tare da jikkata wasu da dama.


Lamarin ya afku ne da sanyin safiyar Alhamis, 31 ga Disambar 2020. An garzaya da wadanda suka samu raunukka da wadanda suka tsira zuwa asibitin dake kusa da inda suke domin karbar kulawar likita a halin yanzu.


A binciken da muka gabatar ya tabbatar mana da cewa. Matar da daga cikin wadanda aka kashe din mai suna Ibrahim Danbanga, wanda yana daga cikin Yan kungiyar sa kai ta yan Bangan garin Babban Rami. Wacce ta yi magana da wakilinmu ta ce an kashe mijinta kuma ya bar ta da kimanin ’ya’yanta takwas. 


Sai dai a zantawar Sakataren gwamnatin jihar Neja (SSG), Ahmed Ibrahim Matane da manema labarai, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata gajeriyar hira da ya yi da manema labarai a Minna a ranar Asabar, ya yi Allah wadai da harin da ‘yan bindiga suka kai wa manoma marasa laifi, yana mai jaddada cewa Wai gwamnatin jihar na kan kokarin ta wurin dakile aikin yan ta'adda a yankin. 


Matane ya ci gaba da cewa a halin yanzu gwamnatin jihar tana kokarin canja fasalin tsarin tabbatar tsaro don fatattakar dukkan nau'ikan kalubalen tsaro a sassan jihar Neja.


Sai dai fa al'ummar Yankunan da yan bindigar suka fi addaba a cikin yankunan Neja, suna ganin wannan fa kawai shaci fadine na gwamnatin. Domin an dade ana barayi suna addabar yankin batare da daukar wani kwakwaran mataki ba.


An dai gudanar da sallar jana'izar wadanda suka rasa rayukkan nasu. A ranar Juma'ar 1/1/2021 a garin na Babban Rami, dake karamar hukumar Mashegu a jihar Neja a tarayyar Nijeriya.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post