Sirrin 'da Namiji !!!

 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @ABUBUWAN DA ZAKI KULA DASU YAYIN DA KUKE SHIRIN AURE DA SAURAYINKI 


Bayan kin fahimci Saurayinki kunyi soyayya da hira irin wacce musulunci ya umurce ku kuyi, abu na gaba shine ku fara maganar aure domin kuwa babu amfanin soyayya da saurayi idan har ba aure zakuyi ba. Kuma musulunci bai yarda da irin wannan soyayya ba ko in ce tarayya tsakanin da namiji da mace ba.


Abinda ya kama ce ki kiyi a yayin da kuke soyayya da saurayinki shine, idan har aka kai matsayin da soyayyar ku tayi nisa ki fara masa maganar aure domin a fara shirye shiryen auren naku, hakan zai sa idan ma ba da gaske yake ba ko kuma bai shirya ba zaki ga ya fara ja baya akan soyayyar ku. Idan kuma ya shirya sai ki tabbatar kun tsara komai kamar yadda addini ya tanadar.


Idan kuma ya amince aka fara maganar auren naku, to, abinda ya kama ce ki kiyi shine, kada ki kuskura ki saka karya a cikin hidimar bikin ku domin kuwa wannan shine babban kuskure da ma'aurata suke yi kafin aure. Ki tabbatar da bakiyi kokarin yin abinda yafi karfi matsayin gidanku ba, domin wannan na iya saka ki cikin damuwa a gidan auren ki. A duk lokacin da za ayi aure yana da muhimmanci musan cewa addini ya riga ya tsara mana komai cikin sauki, sannan kuma akwai al’adu daban-dabam wanda kuma idan har basu sabawa addini ba babu matsala za a iya yi.


Dan haka idan akwai wata al’ada da kike sha’awar yi amma babu halin yi a gidanku, kuma mijin bai da halin yi, to, kada ki kuskura ki matsa masa akan sai anyi wannan al’adar domin kuwa albarkacin aure yafi yawa ga auren da aka gina shi akan tausayin juna.


Kuma Saurayin naki zai fi ganin mutuncin ki da na gidan ku a yayin da yasan cewa baki matsa mishi akan abinda yafi karfin sa ba. Wannan wani babban kuskure ne da wasu mata ke yi tun kafin su shiga gidan auren su, ganin anyi wani abu a bikin wance itama tanaso ayi a nata bikin. Kada ki manta, tausayin juna wani abu ne mai muhimmanci a zamantakewa, tare da gaskiya da rikon amana.  Ki tabbatar da ba kiyi wani abu ba domin burgewa ba, sai dai dan Allah da kuma irin soyayyar da ke tsakanin ki da shi saurayin naki.


ALLAH YAYI MANA ZABI NA GARI. 


~Abubakar Aliyu Ahmad Ningi. 


12th January, 2021.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post