Abinda yafi damuna dan gane da al`umma sayyid ibrahim yaqub al-zakzaky (h)



MA'ASUMAH NIGERIA NEWS UPDATE




Kasantuwar su mutane ne da suke gani basu San mene ne mafita ba. kasan idan mutum yana cikin wani hali Kuma ya San meye mafita, kaga yazama da sauki tunda yasan ta inda zaibi yafita kenan Amma mafi yawan mutane sun San akwai matsala In ka tambayi mutum ko wane irin mutum ne, ko da mutum 'Adiy' ka tare ka tambayeshi yasan akwai matsala amma bai San meye mafita ba. Don haka nema in Suka tashi wani lokaci suna Neman su fidda kansu sai su yi wanda zai Dade dilmiya su.


Alal misali, shekarun biyu da suka gabata, sunyi za6e sai suka ga cewa sakamakon za6en da aka fitar ba Wanda Suka kada bane  Amma da Suka tashi sai suka shiga ciccinna wuta a Gidajen shugabannin siyasa, Wanda ba abin da ya kamata suyiba kenan 


Kaga mutum yasan da matsala amma bai San magani ba. Kuma abin takaici ba a shirye yake ya saurari Wanda yasani ya Gaya Masa ba.kaga wannan abin takaici ne kaga mutum yana cikin wani dimuwa, ga mafita Amma bai San abin da ya dace ba.


Alal misali kamar ace ana cikin wani Babban zaure sai gobara ta tashi ga qofar da in aka biza afita Amma sai mutane suna ta kaiwa da komawa zuwa inda Mai yiwuwa ma konewa zasuyi . To wannan Shi ne Babban abin da ya dame mu. Cewa ga mutane suna cikin wani hali Amma Basu San mafita ba,Kuma kaico. Da ma idan aka fada musu ga mafitar za su yarda (Amma) ina! Zasu ga kamar kana nufin ka hallakasu ne 


     FATANMU A GABA :

Muna ganin akwai fata Da ace misali mutum Hali Da yake gani yana ganin ba wata fata to da ainishin sai ya yanke kauna. To Amma mu akwai fata a gare mu. Ganin cewa duk da halin da muke ciki Muna ganin alamomin da ke nuna cewa Nan gaba abubuwa zasu yi kyau Kuma tunda akwai wannan fatan to lallai akwai farin ciki tare damu akan cewa Nan gaba al'amura kyau zasuyi ba muni ba .insha Allah .


Cikin Jawabi Sheikh zakzaky (H) 


Faruq sani kudan ✍️

16/1/2021

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post