UHMM A'A BAN MUTU BA, AI BAN MUTUBA: Mafarkina da marhuma Khalisat M Kabir !!!



Allahumma salli ala Muhammad wa a li Muhammad. Ba zan taba mantawa dake ba Khaleesat mai halin girma, ina kewarki har yau zuwa gobe, Allah ya kara daukaka matsayinki.


Ludufi na Allah, na ganta cikin baccini bayan kwantawa da na yi a daren 20/11/2020. Cikin kyakkyawan yanayi.


Tun da Allah ya mata rasuwa, ba zulumin da nake kamar yadda ta so mu yi Ido biyu da juna tun kafin ta fara rashin lafiya, amma hakan Allah bai yassare min ba. Tana gab da zata fara rashin lafiya na ajali, ta so in zo, duk san da mu yi waya sai ta ce, "Yau she zaka zo?", sai na ce, "Zan zo in sha Allah, in na samu dama". Amma Allah bai yarda min ba. Har an zo lokacin da bata da ko waya(wayar ta fadi a ruwa), tana aran na wata sister kawarta ta kiran mu gaisa maganar kenan yau she zaka zo?. Sai bayan komawarta ga Al-maliku mai iko kanta, na fahimci wannan kalmar: "Yau she zaka zo", kalmar ce ta ban kwana, amma ban fahimtaba, ban je mun yi ban kwanaba. Wanan kalmar tana min ciwo sosai in na tuna.


A ranar 19/11/2020, a ranar na kammala wani rubutu da nake kan rayuwarmu da Khaleesat mai taken "TANA DA HALIN GIRMA" wanda na mayar da shi "PDF", kuma a ranar da dare, na Kira Umma na kara mata ta'aziya, tare da makusantanta domin an yi addu'an bakwai ba ni a gida, na koma school.


Mafarki na yi da ita, kamar yadda na fadi a daren 20/11/2020. Ranar Jumma'a. Daga ciikin mafarkin:


Na ganta cikin kyakkyawan yanayi, sai murmushi take tana walwala. A lokacin sai naga wata mota, to sai ta shiga wanan mota ta tare can gefen hagu, ta ce wanan wurin ba wani wanda zai zauna ,tare dakai zamu zauna. A lokacin sai na shiga na zauna a gefen kofan hagu, ita kuma ta zauna gefena ta hannun dama. Sai muke hira haka (ban iya tuna wana hira mu yi), amma cikin murmushi da walwala, sai na kalleta nake cewa, kai! ba kin mutuba? Budan bakin ta sai ta yi dariya ta ce, "Uhmm. Ban mutu ba! Ai ban mutu ba!!". Sai na shiga mamaki nake cewa, "Amma to kin sa duk mun shiga zulumi, wallahi mun damu sosai, na shiga damuwa sosai, kin saka umma a damuwa". Sai ta yi dariya. Ta sake maimaita wanan kalmar "Ai ban mutu ba!".


Mun yi hira mun dade, wannan shi ne al-muhim cikin abubuwan da ya faru a mafarkina da Shaheeda Khaleesat. Kuma na ji labarin wasu mafarkai da wasu bayain Allah su yi, duk labarin kowa zai ce ya ganta a kyakkyawan yanayi.


Na tashi ranar Jumma'a da safe, na ji duk farin-ciki ya mamaye qalbina. Saboda mun ji daga mallamai cewa, "Mafarki da mamaci, gaskiya ne domin rayuwar barxahu gaskiya ne, duk yanayin da kaga mamaci ka kaddara haka ne kawai, in ka gansa a kyakkyawan yanayi to haka ne, in ka gansa a mummunar yanayi, yana bukatar addu'a".


Bayan haka, sai na ke ba wani mallamina labari, sai yake cewa, "Haqiqa in ka yi mafarki da wanda ya mutu, yake cewa "Ban mutuba, to lallai yayi shahada, ko kasan hanyar da yayi, ko baka san hanyar shahadar nasa ba. To haqiqa alamu ne na yayi shahada. Nan dai hankalina ya kwanta, na ji duk farin-ciki ya mamaye zuciyata. Wallahi sai na ji damuwar dake damuna na rashinta, ya ragu.


Haqiqa Shaheedah Khaleesat. Ta dade tana kwadayin shahada, wanda so da dama mu kan yi hira, har nake mata wasa nake cewa, "Ni gaskiya na fi son sai burinmu ya cika, domin rashinki zai sa ni cikin damuwa", sai ta ce, duk abun da Allah yayi daidai ne. Gashi Allah ya bata ta hanyar da bamu da zato ko tsammani.


Allah ya kara daukaka matsayinki Shaheeda Khaleesaty. Mu kuma Allah ya sa mu yi dacewa irin naki.


__Jameel Ibn Ibraheem

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post