Shahid Ishaq Muh'd Suleman: Jarumai suna zuwa su tafi Amma gwaraza suna nan har abada


Allah yake cewa Kar ku fada karma ka zata acikin zuciyarka cewa su wadanda aka kashe Akan tafarkin Allah su matattu ne a'a su rayayyune wajen ubangijinsu shi yake ciyardasu, Kuma yake azurtasu. Magana Akan Shahid Ishaq Muh'd Suleman wannan kamar wani kogi ne Wanda bansan yanda zan fada ba kokumi in bada misalinsa, na taso tun Ina Dan karami tareda Shahid, haka muka ta zama har zuwa lokacin da Allah T yasanya hijabi tsakanin mu da Shahid, 


Shahid Ishaq Muh'd Suleman, shi Dan gwagwarmaya ne zan Iya cewa sanidiyar Shahid mutane da dama sun fita program tun daga sokoto, zaria da Abuja wajen neman yancin jagora wannan aikin sane Yana Campaign Yan uwa zuwa duk wani taro Wanda zaayi na harka ni kaina nafita program, sokoto da Abuja sanidiyar Shahid, lokacin da na fara haduwa da *mas'ud Dan masani shinkafi*muzaharan kudus Wanda shine last program namu tareda Dan masani da Shahid, Shahid Yana Kira yanayin abinda ake Kira da suna *Mass Campaign* na Yan uwa Koda akwai Wanda baida sauran kudi zai Iya cikawa aikinsane, 


Shahid Ishaq Muh'd Suleman wajen bada Imfaki da biyan hakkin *Shuhadau* wannan shaida ne shi yake yin na farko wajen badawa, 


Halayensa basa misaltuwa tsawon shekaruna da Shahid bansan matsalarsa ba saidai murmushi Akan komai halayensane, Kadan Kenan daga cikin halayen Shahid Ishaq Muh'd Suleman, 


27/12/2020,

@bbakarlabbo, 

Public health concern,

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post