Hukumcin Musulmin da ke yin sihiri !


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


ANA KASHE MASIHIRTAN MUSULMI AMMA BANDA NA MUSHIRIKAI 


Sihiri aiki ne na kafirci wanda Allah ya haramta yinsa ga dukkan wanda yayi imani da shi. Duk wanda ya aikata sihiri a muslimci ya kafirta, sai dai ya tuba zuwa ga Allah idan ba a yanke masa haddi ba sakamakon rashin gwamnatin muslimci. 


Shi kuwa kafiri ba a kashe shi in an same shi yana aikata sihiri, dalilin hakan kuwa nanan biye cikin hadisi daga Manzon Allah (S. A. W. W). 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


9- ع، علل الشرائع عَنِ ابْنِ الْوَلِيدِ عَنِ الصَّفَّارِ عَنِ الْبَرْقِيِّ عَنِ النَّوْفَلِيِّ عَنِ السَّكُونِيِّ عَنِ الصَّادِقِ عَنْ أَبِيهِ ع قَالَ قَالَ رَسُولُ اللَّهِ ص‏ سَاحِرُ الْمُسْلِمِينَ يُقْتَلُ وَ سَاحِرُ الْكُفَّارِ لَا يُقْتَلُ فَقِيلَ يَا رَسُولَ اللَّهِ ص وَ لِمَ لَا يُقْتَلُ سَاحِرُ الْكُفَّارِ قَالَ لِأَنَّ الشِّرْكَ أَعْظَمُ مِنَ السِّحْرِ وَ لِأَنَّ السِّحْرَ وَ الشِّرْكَ مَقْرُونَانِ.


Ya zo cikin ILALUS-SHARA'I'I, daga Ibn Waleed, daga Saffaari, daga Barqeey, daga Naufaleey, daga Sakuniyyi, daga Sadeeq daga babansa (A. S) yace, Manzon Allah (S. A. W. W) yace; 


" MASIHIRCIN MUSULMI ANA KASHE SHI, SHI KUWA MASIHIRCIN KAFIRAI BA A KASHE SHI ."


Aka ce, " Yaa Ma'aikin Allah! Don menene ba za a kashe masihircin kafirai ba ?" Yace; 


" DOMIN (ita) SHIRKA TA FI GIRMA FIYE DA SIHIRI, KUMA DOMIN SHI SIHIRI DA SHIRKA A GWAME SUKE (abu guda ne ) ."


                    NAZARI 

                ____________



Idan muka yi nazari za mu iya fahintar wannan hukunci cikin sauqi, domin shari'a na kan wanda yayi imani ne da Allah. Duk wanda yayi imani bayan kafirci sannan ya aikata kafirci (shirka), to, ya kafirta (riddah) kenan , wanda yayi riddah kuwa hukuncinsa kisa. 


Shi kuwa kafiri dama bai yi imani ba ballantana irin hukuncin muslimci ya hau kansa. Da ma can shi kafiri ne sannan ya qara aikata wani aikin kafirci, saboda haka tunda ba a kashe shi saboda kafircin nasa na farko ba ba za a kashe shi don ya qara aikata wani kafirci da bai kai girman na farko (shirka) ba. 


Sannan kuma ya zo cikin wata riwaya cewa, 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


وَ رُوِيَ‏ أَنَّ تَوْبَةَ السَّاحِرِ أَنْ يَحُلَّ وَ لَا يَعْقِدَ[20].


" TUBAR MASIHIRCI SHINE YA WARWARE (wannan qulli da ya qulla na sihiri), KADA YA QULLA (a gaba) ."


Ya qara zuwa cikin wata riwaya cikin abubuwan da Annabi (S.A.W.W) yayi hani zuwa wajen Boka, yace; 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


10- لي، الأمالي للصدوق فِي مَنَاهِي النَّبِيِّ ص‏ أَنَّهُ نَهَى عَنْ إِتْيَانِ الْعَرَّافِ وَ قَالَ مَنْ أَتَاهُ فَصَدَّقَهُ فَقَدْ بَرِئَ مِمَّا أُنْزِلَ عَلَى مُحَمَّدٍ ص‏[21].


" DUK WANDA YAJE MASA KUMA YA GASKATA SHI (kan shirmen nasa na bokanci), TO, HAQIQA YA BARRANTA DAGA ABINDA AKA SAUKARWA MUHAMMAD (S. A. W. W) ."



(4) علل الشرائع ج 2 ص 233.


(5) أمالي الصدوق ص 239.



بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج‏76، ص: 213


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda. 


(08137925034-08126385470)


25th December, 2020/ 11th Jimada-Ulah, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post