Gwargwadon hankalin mutum gwargwadon yadda za kayi masa magana !!!


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


MUKAN KAUCEWA WATA MAGANAR CE DON TA FI QARFIN HANKALINSU 


Ita magana ana furta tane a inda ta dace, ma'ana ana yinta ne cikin mutane gwargwadon iliminsu ko hankalinsu ko tunaninsu, amma duk da hakan wasu ba sa iya fahintarka. 


Dalilin hakan kuwa shine, sakamakon wani imani ko karatun da ya riga ya shiga cikin jama'a ya kanyi tasiri ta yadda in sun ji wata baquwar magana sabanin abinda suka sani sai su qaryata ka, kuma qaryata gaskiya kafirci ne. Wannan dalili yasa muke kaucewa wata magana cikin amawa don mu tarerayi imaninsu. 


Manzon Allah (S. A. W. W) na cewa, 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼



 قَالَ رَسُولُ اللَّهِ ص‏ إِنَّا مَعَاشِرَ الْأَنْبِيَاءِ نُكَلِّمُ النَّاسَ عَلَى قَدْرِ عُقُولِهِمْ.


" LALLE MU TARON ANNABAWA MUNA YIWA MUTANE MAGANA NE GWARGWADON HANKALINSU ."


A wata riwaya kuma, daga Naufaliyyu da Jahmu Bn Hakeem Al-Mada'iniy 

,daga Sakuniyyi, daga Abu Abdullahi, daga iyayensa (A. S) yace, Manzon Allah (S. A. W. W) yace; 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


5- سن، المحاسن النَّوْفَلِيُّ وَ جَهْمُ بْنُ حَكِيمٍ الْمَدَائِنِيُّ عَنِ السَّكُونِيِّ عَنْ أَبِي عَبْدِ اللَّهِ عَنْ آبَائِهِ ع قَالَ قَالَ رَسُولُ اللَّهِ ص‏


" IDAN LABARI YA ISO MUKU GANE DA KYAWUN HALIN MUTUM, O, KUYI DUBI ZUWA GA KYAWUN HANKALINSA (mai sauqi fahintar gaskiya ne ko a'a), DOMIN ANA SAKA MASA NE DA HANKALINSA ."


" إِذَا بَلَغَكُمْ عَنْ رَجُلٍ حُسْنُ حَالِهِ‏ فَانْظُرُوا فِي حُسْنِ عَقْلِهِ فَإِنَّمَا يُجَازَى بِعَقْلِهِ


بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج‏1، ص: 93



Saboda haka a riqa duba yanayin irin mutane kafin yin magana dasu. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda. 


          (08137925034)


27th December, 2020/ 13th Jimada-Ulah, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post