Zaman Aure: Gare Mu Mata Da Maza... Kashi Na Biyu (2)


 Tunatarwa Gareku mazajenmu,abin alfaharinmu, jigon rayuwarmu,iyaye 'ya'yanmu, idan bada kuba babu abinda zamu iya yi.

 

Banda laifin wasu mata na rashin gyarawa, tofa kuma akwai laifinku, saboda yanzu ba kowane namiji bane yasan ya yabawa matarsa ba, bayan yafi kowa sanin cewa tunda shi ya ajeta a gidan, to dole duk abinda tayi don ta birgeshi ne ko ta sakashi farin ciki takeyi, sannan ba kowane namiji bane yake bada gudummawar data dace, wurin taimakawa matarsa tayi masa abinda ya dace ba, ina nufin ba kowa bane yake bata damar data dace ba, ta hanyar siya mata wasu abubuwan da zasu taimaka mata wurin gyarawa don yaji dadi ba.


Duk sanda kayi wankanka kasha turarenka, bata gajiya, daka fito sai tace kai maigidana kayi kyau sosai Allah dai ya bar min Kai, ta kiraraka fa sosai, amma saitayi wankan tayi kwalliyar amma shiru kakeji, babu wani comment akai, wata ma har magana takeyi ta tambaya tayi kyau, amma duk da haka baya gyarawa lokaci na gaba ya yaba tun kafin ta tambaya din, kuma wallahi yabawan na kara mata kwarin gwiwa, wurin nema maka sabbin salalen da zasu kara sakawa kaji dadi, ko budurwarka ceka ya ba mata, wallahi saita kara sonka to bare kuma mata.


Ke kuma yar uwa kar kiji nace da laifinsa, saboda baya siya maki abubuwan da zaki gyara, to bari kiji!! a yanzu zamani ya sanja mata, anbar zama a gida ace komai sai miji yayi maki,akwai hanyoyi halastattu da akebi wurin samun abubuwan da zasu taimakawa zaman aurenki, nasan kin fini saninsu.


To Kar kice komai sai shine zaya yi maki, yanzu yayin zama babu sana'a ya zama kauyenci, duk da akwai mazajen da basa barin matansu suyi sana'a, amma fa ka sani idan har ka hana matarka yin sana'a, tofa ka tabbar a wurinka ba abinda zata nema ta rasa, saboda akwai yanayin rayuwa, wata ran zaka iya tashi bakadashi, amma idan tana 'yar sana'arta sai kaga an taru an rufawa juna asiri, itama fa sana'ar tanada nata alfanun maigida........


Insha Allah lokaci na gaba zan dan kara fadar wani abu. Allah ya bamu ikon gyarawa baki daya.


_ Zarah A Zamsarf

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post