'Yar Magana Kadan Sai Su Fara Yi Ma Gorin Masallaci !!!


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


ALLAH YA ZARGI IRIN WADANNAN MASALLATAI NAKU 


Duk wani aikin alkhairi akan gina shi ne bisa taqawa, kuma babu abinda ke bata shi har sai an canza ma'ana ko kuma niyya ko kuma wani aiki wanda ya sabawa manufar da aka gina shi ta farko. 


Akwai wasu mutane masu iqirari da cewa, " WANNAN MASALLACINMU NE !" Har ma ka ji suna gorantawa wasu wai su ba su da masallaci wanda za a kira cewa nasu ne. 


Abinda har yanzu iliminsu bai riske shi ba shine, Allah (T) cewa, 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


" وَأَنَّ ٱلۡمَسَٰجِدَ لِلَّهِ فَلَا تَدۡعُواْ مَعَ ٱللَّهِ أَحَدٗا ٨١."


" KUMA LALLE GURAREN SUJADAH NA ALLAH NE, KADA KU KIRA WANI TARE DA ALLAH ."


       (SURATUL-JINN:18)


Saboda haka da zarar mutum ya gina masallaci in dai don Allah ya gina, to, daga wannan lokaci ya tashi daga nasa ya koma na Allah, kuma duk wanda yayi imani da shi (Allah) yana da haqqin bauta masa a cikinsa. 


Sannan kuma kasancewarsa na Allah ba zai hana ka cigaba da samun ladan gina shi ba, sai dai ka kiyaye don kada ka bata ladanka. Allah (T) na cewa, 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تُبۡطِلُواْ صَدَقَٰتِكُم بِٱلۡمَنِّ وَٱلۡأَذَىٰ كَٱلَّذِي يُنفِقُ مَالَهُۥ رِئَآءَ ٱلنَّاسِ وَلَا يُؤۡمِنُ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِۖ فَمَثَلُهُۥ كَمَثَلِ صَفۡوَانٍ عَلَيۡهِ تُرَابٞ فَأَصَابَهُۥ وَابِلٞ فَتَرَكَهُۥ صَلۡدٗاۖ لَّا يَقۡدِرُونَ عَلَىٰ شَيۡءٖ مِّمَّا كَسَبُواْۗ وَٱللَّهُ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلۡكَٰفِرِينَ ٤٦٢."


" YAA KU WADANDA SU KAYI IMANI ! KADA KU BATA SADAQOQINKU DA GORI DA KUMA CUTARWA KAMAR WANDA KE CIYAR DA DUKIYARSA DON NUNAWA MUTANE (Riya), KUMA BAI YI IMANI DA ALLAH DA RANAR LAHIRA BA. TO, MISALINSA KAMAR FA'A/FAQO NE DAKE DA TURBAYA (a kansa) SAI RUWAN SAMA (mai qarfi) YA SAME SHI (ya wanke shi fes) YA BARSHI BA KOMAI , BA SU DA IKON KOMAI A KANSA DAGA ABINDA SUKA AIKATA, KUMA ALLAH BA YA SHIRYAR DA MUTANE KAFIRAI. "


        (BAQARA :264)


Idan kuwa ka toge da cewa masallacinka ne har kana aibanta 'yan'uwanka musulmi da kafirta su a cikinsa, to, lalle nakan ne, sai dai Allah na barranta da wannan masallaci naka. 


Koma cikin Suratul-Tauba kaji abinda Allah ke fada a kanka/ku.


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼



" وَٱلَّذِينَ ٱتَّخَذُواْ مَسۡجِدٗا ضِرَارٗا وَكُفۡرٗا وَتَفۡرِيقَۢا بَيۡنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ وَإِرۡصَادٗا لِّمَنۡ حَارَبَ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ مِن قَبۡلُۚ وَلَيَحۡلِفُنَّ إِنۡ أَرَدۡنَآ إِلَّا ٱلۡحُسۡنَىٰۖ وَٱللَّهُ يَشۡهَدُ إِنَّهُمۡ لَكَٰذِبُونَ ٧٠١ ."


"KUMA LALLE WADANDA SUKA RIQI MASALLACI DON CUTARWA DA KAFIRCI DA KUMA RARRABA TSAKANIN MUMINAI, DA KUMA TAIMAKON WANDA YA YAQI ALLAH DA MANZONSA GABANIN (wannan lokaci) , KUMA SUNA YIN RANTSUWA CEWA BA KOMAI MUKE NUFI (da ware masallatanmu ba) SAI DON KYAUTATAWA , KUMA ALLAH NA SHAIDAWA CEWA SU MAQARYATA NE !"


(Ba komai yasa suka ware masallatansu ba sai don yiwa muslimci zagon qasa da neman kafirta 'yan'uwansu musulmi da kuma yiwa Yahudu da Nasara aiki) .


To, irin wadannan masallatan naku ne Allah ya hani Manzonsa (S. A. W. W) shiga ciki da kuma sauran mabiyansa muminai har zuwa wannan lokaci/zamani.


  " لَا تَقُمۡ فِيهِ أَبَدٗاۚ لَّمَسۡجِدٌ أُسِّسَ عَلَى ٱلتَّقۡوَىٰ مِنۡ أَوَّلِ يَوۡمٍ أَحَقُّ أَن تَقُومَ فِيهِۚ فِيهِ رِجَالٞ يُحِبُّونَ أَن يَتَطَهَّرُواْۚ وَٱللَّهُ يُحِبُّ ٱلۡمُطَّهِّرِينَ ٨٠١ ."


" KADA KA TSAYA A CIKINSA HAR ABADA ! MASALLACIN DA AKA GINA SHI BISA TAQAWA TUN FARKO SHI YAFI CANCANTA KA TSAYA CIKINSA. A CIKINSA AKWAI WASU MUTANE (na kirki) DAKE SON SU TSARKAKA, KUMA ALLAH NA SON MASU TSARKAKA ."


  (TAUBA:107-108)


Idan mu kayi la'akari da masallatan wannan zamani za muga cewa duk masallacin da ka fara gani an gina cikin garin birni ko qauye shine masallacin kirki, wadanda suka biyo su kuma za ka tarar sun gina su ne don su riqa kafirta na farko da mushirikantar dasu ko bidi'antar dasu wanda hakan ke qara rarraba al'ummar Annabi (S. A. W. W), kuma yin haka taimakon Yahudu da Nasara ne da kuma yiwa muslimci zagon qasa. 


Saboda haka babu alkhairi cikin masallatan da aka gina su bisa wannan manufa. Wannan tunatarwar ce, Allah yasa a amfana. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda. 


        (08126385470)


12th November, 2020/ 26th Rabi'ul-Awwal, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post