YANA DAGA CIKIN NASSIN IMAMANCIN IMAM ALI (A. S): Imam Ali (A.S) Majibincin Dukkan Wanda Yayi Imani Ne !!!


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATES @

A duk lokacin da ake magana kan abinda Annabi (S. A. W. W) ya bari a matsayin abin koyi kuma abin riqo ga dukkan muminai dole ya zamana cewa an koma zuwa ga nassi don gujewa fadawa cikin rudani ko kuma yin riqo da wadanda su kansu ba shiryayyu bane ballantana su shiryar da kai. 


Imam Ali (A. S) ya kasance shine wasiyyi na farko cikin wasiyyan da Annabi yabar mana su domin su zame mana abin riqo kuma abin koyi. 


Tun kafin ranar Ghadeer da kuma lokacin wafatinsa (S. A. W. W) yayi mana wasu isharori dangane da bin Imam Ali (A. S) don kada mu fada rudani. 


Ya zo cikin Asbabun-Nuzul dangane da ayar nan dake cewa, 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


" إِنَّما وَلِيُّكُمُ اللهُ وَرَسولُهُ وَالَّذينَ آَمَنوا "


" ABIN SANI KAWAI MAJIBINCIN (al'amarinku) SHINE ALLAH DA MANZONSA DA WADANDA SU KAYI IMANI...... "


</span>                 

 


 قال الكلبي وزاد أن آخر الآية في علي بن أبي طالب رضوان الله عليه لأنه أعطى خاتمه سائلاً وهو راكع في الصلاة.<br>أخبرنا أبو بكر التميمي قال: أخبرنا عبد الله بن محمد بن جعفر قال: حدثنا الحسين بن محمد عن أبي هريرة قال: حدثنا عبد الله بن عبد الوهاب قال: حدثنا محمد الأسود عن محمد بن مروان عن محمد السائب عن أبي صالح عن ابن عباس قال: أقبل عبد الله بن سلام ومعه نفر من قومه قد آمنوا فقالوا: يا رسول الله إن منازلنا بعيدة وليس لنا مجلس ولا متحدث وإن قومنا لما رأونا آمنا بالله ورسوله وصدقناه رفضونا وآلوا على أنفسهم أن لا يجالسونا ولا يناكحونا ولا يكلمونا فشق ذلك علينا فقال لهم النبي عليه الصلاة والسلام 

<span class=hd4>

" إِنَّما وَلِيُّكُمُ اللهُ وَرَسولُهُ وَالَّذينَ آَمَنوا "


Kalbi yace, an qara cewa lalle qarshen wannan ayar (ta sauka ne) akan Aliyu Bn Abiy 'Dalib yardar Allah ta tabbata a gare shi, domin shi ya bayar da (sadaqar) zobensa ga mabaraci, alhali (Aliyu) yana ruku'u cikin sallah. 


Abubakar Al-Taimiy ya bamu labari yace, Abdullahi Bn Muhammad Bn Ja'afar ya bamu labari yace, Hussaini Bn Muhammad ya bamu labari daga Abu Hurairata yace, Abdullahi Bn Abdul-Wahab Bn Marwan ya bamu labari daga Muhammad As-Saa'ibiy, daga baban Salihu daga Ibn Abbas (R. A) yace, 


" Abdullahi Bn Salam yazo tare da mutanensa wadanda su kayi imani tare da shi suka ce, " Yaa Ma'aikin Allah! Lalle matsayinmu an nisantar da shi, bamu da wani gurin zama ko abokan hira. Yayin da mutanenmu suka ga munyi imani da Allah da Manzonsa kuma mun gaskata shi, sai suka yi watsi damu kuma suka yi alqawari ga kawukansu cewa ba za su zauna tare damu ba, kuma ba za su aurar mana ba, kuma ba za suyi magana damu ba, sai hakan yayi tsanani gare mu. "


Sai Annabi (S. A. W. W) yace musu, 


" ABIN SANI MAJIBINCINKU SHINE ALLAH DA MANZONSA DA KUMA WADANDA SUKA YI IMANI.... "


</span>      


           

 الآية.<br>


ثم إن النبي صلى الله عليه وسلم خرج إلى المسجد والناس بين قائم وراكع فنظر سائلاً فقال: عل أعطاك أحد شيئاً قال: نعم خاتم من ذهب قال: من أعطاكه قال: ذلك القائم وأومأ بيده إلى علي بن أبي طالب رضي الله عنه فقال: على أي حال أعطاك قال: أعطاني وهو راكع فكبر النبي صلى الله عليه وسلم ثم قرأ 


Sa'annan Annabi (S. A. W. W) ya fita zuwa masallaci, mutane na tsakanin tsayuwa da ruku'u, sai ya hangi mabaraci, sai yace, 


" WANI YA BAKA WANI ABU NE (cikin wannan masallaci) ?" Yace, 


" Wancan da ke tsaye ." Yana yin nuni da hannunsa zuwa ga Aliyu Bn Abiy 'Dalib (R. A). Sai (Manzon Allah) yace, 


" A WANNE IRIN HALI YA BAKA ?" Yace, " Ya bani ne alhali yana cikin ruku'u. "


Sai Annabi (S. A. W. W) yayi kabbara, sa'annan ya karanta, 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

<span class=hd4>

" وَمَن يَتَوَلَّ اللهَ وَرَسولَهُ وَالَّذينَ آَمَنوا فَإِنَّ حِزبَ اللهِ هُمُ الغالِبونَ "


" DUK WANDA YA JIBINCI ALLAH DA MANZONSA DA KUMA WADANDA SUKA YI IMANI, TO, LALLE RUNDUNAR ALLAH ITA CE MASU RINJAYE ."


Saboda haka tun a wannan lokaci ma wadanda suka ji wannan magana daga Annabi (S. A. W. W) suka san cewa lalle Imam Ali (A. S) shine majibincin al'amarinsu bayan Annabi (S. A. W. W) .


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼 Ado Isah Guda. 


6th November, 2020/ 20th Rabi'ul-Awwal, 1442.


      (08126385470)

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post