Wasiyyar Imam Ali Zainul-Abideen ga ɗansa Imam Baqeer (A.S) !!!


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


ZALUNCI MAFI MUNI SHINE WANDA ALLAH NE KADAI KE 'DAUKAR FANSAR SA 


Zalunci zunubi ne daga cikin zunubai mafiya girma, babu wani mai so a zalunce shi ko da kuwa ace shi ya kasance yana zaluntar wasu. Kamar dai adalci ne da ya kasance ko da mutum ba ya yi za ka tarar yana so ayi masa, kuma yakan ji dadi in anyi masa. 


Allah ya haramtawa kansa zalunci kuma ya haramta shi cikin bayinsa. Saboda haka dukkan Manzanni da A'immah (A. S) sun yi hani ga aikata shi cikin bayin Allah, ko da ma akan dabba ce marar cutarwa. 



Gajeriyar wasiyyah amma mai girma kuma abin tsoro ga dukkan mumini wacce Imam Aliyu Zainul-Abideen (A. S) ya yiwa dansa Imam Muhammad Baqir (A. S). 


Ga wasiyyar nan kamar haka, 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


لي، الأمالي للصدوق الْهَمَدَانِيُّ عَنْ عَلِيٍّ عَنْ أَبِيهِ عَنْ إِسْمَاعِيلَ بْنِ مِهْرَانَ عَنْ دُرُسْتَ عَنْ عِيسَى بْنِ بَشِيرٍ عَنِ الثُّمَالِيِّ عَنْ أَبِي جَعْفَرٍ ع قَالَ:


Ya zo cikin Amaliy Lis-Sudduq Al-Hamdaaniy, daga Aliyu, daga babansa, daga Isma'il Bn Mihraan, daga Durusta, daga Isah Bn Basheer, daga Thumaaliy, daga Abu Ja'afar (A. S) yace, 


 لَمَّا حَضَرَتْ عَلِيَّ بْنَ الْحُسَيْنِ ع الْوَفَاةُ ضَمَّنِي إِلَى صَدْرِهِ ثُمَّ قَالَ يَا بُنَيَّ أُوصِيكَ بِمَا أَوْصَانِي بِهِ أَبِي عَلَيْهِ السَّلَامُ حِينَ حَضَرَتْهُ الْوَفَاةُ وَ بِمَا ذَكَرَ أَنَّ أَبَاهُ أَوْصَاهُ بِهِ فَقَالَ يَا بُنَيَّ إِيَّاكَ وَ ظُلْمَ مَنْ لَا يَجِدُ عَلَيْكَ نَاصِراً إِلَّا اللَّهَ‏[26].



" YAYIN DA MUTUWA TA ZOWA ALIYU BN HUSSAIN (A. S) SAI YA JAWONI ZUWA QIRJINSA, SA'AN NAN YACE, " YAA 'DANA ! INA YI MAKA WASIYYAH DA IRIN ABINDA BABANA (A. S) YAYI MIN WASICCI DA SHI YAYIN DA MUTUWA TAZO MASA, KUMA DA ABINDA YA AMBATA CEWA BABANSA YAYI MASA WASICCI DA SHI. SAI YACE, 


" YAA 'DANA ! NA HANE KA DA ZALUNTAR WANDA BA SHI DA MAI 'DAUKAR MASA FANSA A KANKA SAI DAI ALLAH ."


2- ل، الخصال أَبِي عَنِ السَّعْدَآبَادِيِّ عَنِ الْبَرْقِيِّ عَنْ إِسْمَاعِيلَ بْنِ مِهْرَانَ‏ مِثْلَهُ‏[27].


Isma'il Bn Mihraan ma ya riwaito irin wannan riwaya cikin Khisaal nasa. 



(7) أمالي الصدوق ص 110.


(8) الخصال ج 1 ص 11 و 12.


بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج‏72، ص: 309


Yanzu an wayi gari masu qarfi (dukiya) na zaluntar na qasa dasu ta hanyar yi musu qwace na fin qarfi ganin cewa suna da dukiyar da ba za aja da su ba. 


Sai kuma mahukunta masu gadarar suna da mulki da malami , su taka su harbe su kashe su bisne wasu da ransu don nuna fin qarfi , sun manta da cewa akwai wanda ya fi su qarfi (Allah) nanan yana ganinsu kuma yana jinkirta musu zuwa cikar ajali. 


Bayin Allah raunana na ta faman addu'ah suna miqa kukansu zuwa ga Allah wanda su kayi imani da shi cewa yafi qarfin dukkan wani mai qarfi don ya daukar musu fansa. 


To, ku sani lokaci ne ake jiran zuwansa wanda Allah zai daukar mana fansa. Kuma ku sani shi kamun Allah ba irin naku bane, domin ya fi naku qarfi da tsanani. 


Allah (T) na cewa, 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


 " إِنَّ بَطۡشَ رَبِّكَ لَشَدِيدٌ ."٢١


" LALLE (fa ka sani ) DAMQAR UBANGIJINKA MAI TSANANI CE ."



       (SURATUL-BURUJ :12)


YAA ALLAH KA 'DAUKAR MANA FANSA KAN WADANDA KE ZALUNTARMU, DOMIN BABU MAI 'DAUKAR MANA FANSA A KANSU IN BA KAI BA !


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼 Ado Isah Guda. 


        (08137925034)


30th November, 2020/ 15th Rabi'us-Sani, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post