Ya zauna da shi shekaru 13 a garin Makkah, sannan ya cigaba da zama shekaru 10 a garin Madinah. Jimlar shekarun da yayi da shi yana ba shi tarbiyya shine shekaru 27.

 


A matsayinsa(S.A.W.W)wanda yafi kowa tarbiyya kuma mafificinsu wajen iya tarbiyyantarwa, shine ya bawa Imam Ali (A.S)tarbiyya na tsahon shekaru 27, domin ya dawo hannunsa ne a shekara ta 6 kafin Annabtarsa, kenan ya zauna da shi tsahon shekaru 4 kafin ya zama Manzo.


Ya zauna da shi shekaru 13 a garin Makkah, sannan ya cigaba da zama shekaru 10 a garin Madinah. Jimlar shekarun da yayi da shi yana ba shi tarbiyya shine shekaru 27.

Wannan dalili yasa Imam Ali (A.S)yafi kowa cikin Sahabbai tarbiyyah, ilimi, jarunta da kuma kunya.

Duk wani guri da Annabi (S.A.W.W)ya je don yin wa'azi ko kuma yaqi sai ka tarar Imam Ali (A.S)yayi tarayya da shi (he is constant company), sai dai yaqin Tabuka ne kadai bai yi tarayya da shi ba bisa umarnin Manzon Allah (S.A.W.W).

Rashin halartar wannan yaqi nasa kuwa ya samo asali ne daga Allah (T)wanda ya umarci Manzonsa (S.A.W.W)cewa ya zaunar da shi a gida Madinah.

Ashe wannan zama nasa nassi ne na cewa shine zai gaji Annabi (S)cikin dukkan abubuwan da ya bari bayan wafatinsa.

‘’ ASHE BA KA YARDA KA KASANCE MATSAYINKA A WAJENA KAMAR MATSAYIN HARUNA A WAJEN MUSA BA, SAI DAI KAWAI DON BABU ANNABI A BAYANA ?‘’

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

07059911360-08137925034

~12th March, 2020.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post