Rayuwa Ta Da Marhuma Khalisat M Kabir: "Tana Da Halin Girma Khaleesaty" Cewar Jameel Ibraheem.. Fita Na Biyu (2)


 

Gaskiya in ana batun rikon amana,dole a sawoya saboda iya rikon amanarta.Ta kasance mai fara'a da yawan kula mutane,ba wani wanda ta ware ta dauketa a matsayin kawar hamayya rayuwarta take cikin nuna damuwa da kowa.


Haka dai soyayyanmu ta cigaba ba tare da wani damuwa ba,ni kaina wani lokaci na kan yi mamakin yadda ta shaku dani sosai,duk da cewa wasu na sukan cewa ni yaro ne ban isa nemantaba.Ita da wannan yaron take soyayya,nima ta bangarena haka ne a yi ta cewa ta min girma,ba sa'an aurena ba ne da sauran ire-iren wadanan magan-ganu,amma duk da haka bai sanya dayanmu ya ja da bayaba.



Na sota so na aure,itama haka ne,saboda fatan da take yi kaina da "Mijina" take kirana.A wanna lokacin ni kuma da My numfashi.A wanan lokacin na damu da ita sosai har wasu suna ganin cewa ai ni ne ma na damu da ita,se dai sun manta shi so sirri ne abun da ya fito fili da shi ake hukunci.


Tana da halin girma,fiye da yanda ake tsammani,wanda yake mu'amala da ita zai tabbatar da maganata.Ban mancewa a zikira na shaheed Surajo Garun-Kurama.Na samu halarta,naje tun safe a yi addu'oi da sauransu tare da ni,ace da muzahara bayan sallah na tsaya don halartan wannan muzaharar,a wanan lokacin Khaleesaty ta kiran take cewa suna hanyan tafiya Garun-Kurama ne,se na ce ai nima ina can,ta yi murna.A wanna lokacin an zo muzahara ta fara kenan kawai na juya se mu hada Ido sai murmushi take,a wanna lokacin har ta nuna mu hadu(toh ni dayake a tsarina ban haduwa da ita lokacin da take wani abu mai muhimmanci dole se ta gama),haka dai bamu haduba se da a kammala muzahara.Bayan an tashi sai naga tana cikin mutane se na sanya wata sister na ta kira,da taje saboda halin girma irin nata haka ta rungumota su tawo tare ta sake mata fuska,da ta zo mu gaisa,muna tafiya haka muna hira,to dama akwai wani kyauta da na zo mata dashi,dayake babban yayanmu sun je ummara,se ta ce ita tana bukatar carbi ne kawai,mai 34 na tasbihi,toh hakan ya sa na yi kokari na kawo mata da yake ta dade tana tuna min,har wata rana mun yi waya take cewa yau ta ara shi wannan carbi na tasbihi a wurin wata,se ta zo zata amsa se ta ji haushi ta ce,nima mijina ya ce zai kawo min.Zan huta da aro.


Haka dai na zo mata da wanan carbin har da turare,mu ci gaba da hirarmu muna cikin tafiya se wata mamanmu ta kira sunana,cikin raha take cewa wannan ce sirikan tamu.Sai na yi dariya na ce kanwata ce fa,haka nan Khaleesaty itama ta yi dariya ta ce kanwarsa ce nan.Toh anan dai ta tsuguna har kasa ta gaishesu.A wanan lokaci se wata sister na ta kiran,wai na zo mu yi magana,sai na ce aa zamu hadu a gida,nan dai ta ce don Allah na zo,to da naje se take cewa wai wanna babban yarinyar ce budurwanka.Sai na yi dariya na ce eh ai aurentama zan yi.Na dai bata waje saboda irin wannan maganar har na gaji da ji.


Mu ci gaba da hirarmu dai muna tafiya,nan sai take ce min tare da Mama mu zo tana jirana.Haka dai na ciro wanna kyautar da na zo mata dashi,se nake ce mata kina sa turare?, sai ta ce eh mana sosai,sai nake mata wasa nake cewa ai na zata baki sawa,se ta ce ina sawa sosai ka bani kawai,na ciro na bata ta amsa hannu biyu ta ce ta gode.Mu yi sallama ta tafi su tafi gida,nima na fita na tsara mota na koma.


Soyayyanmu dai ta ci gaba,wanda a wanna lokacin na mata alkawarin bazan taba hada soyayyatar da wata,matukar muna tare,itama ta tabbatar min da hakan,kuma ta cika wannan amanar domin bata hada soyayyata da na waniba.


Ta kasance bata boye min duk wani lamari da ya shafeta,akwai wata rana da na Kirata muna hira,sai nake cewa My numfashi,sai take cewa na'am ruhina.Wanan lokacin ta ce na bata labari ne,sai na ce babu sai ta ce toh My zan ma kuka in baka baniba,anan se na ji alamun ta fara kuka.Can se na ji ta dariya,sai nake cewa amma kuka bai miki wahala sai ta ce,ai na fara ne sai naga mama ta kalle ni,sai na ji kunya,shi ne abun ya ban dariya.


Allah ya kyautata zatanmu kanki,bamu san komai kankiba sai alkhairi Khaleesaty.


Zan ci gaba...

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post