Rayuwa Ta Da Marhuma Khalisat M Kabir: "Tana Da Halin Girma Khaleesaty" Cewar Jameel Ibraheem



Kowanne dan adam akwai jarabawar da zai tarar,cikin jarabawa mafi girma a waye gari ace babu wacce take kyautatama,ko wanda kake kyautatawama.


A cikin kwanakin nan,mun yi babban rashi ranar lahadi 8/11/2020 na yar uwa,abokiyar mutumci Khaleesat M. Kabeer.Wanda haqiqanin lamari shi ne,duk wanda ya santa,ko da mu'amala ce sau daya ta hadasu se mutuwar nan ta girgizasa.Kai har da wanda ma be santaba illa a suna.


Mun yi rayuwa da Khaleesat kusan shekara biyu a matsayin masoya,wani abun mamaki saboda amana da damuwa da kulawa,tun da muke bamu taba samun sabaniba,har ta koma ga mahallici,duk da cewa daga baya bisa wani al-amari na ja baya saboda ba yanda zan yi,amma hakan bai sa ta fito ta ce bata yiba,ta rike wannan alakar sosai.Haka nan nima.


Na kasance ni a tsarina ban shirya soyayyaba,har na yiwa kaina wani tsari na cewa bazan fara soyayya ba har sai na kammala secondary.Duk da cewa abokanai da yawa kowa yana soyayya wani lokaci ma na rakasu,amma hakan bai taba sa naji ni na yi wata budurwa a wanan lokacinba.Har wasu mutane da yawa suke fadin cewa:"Mu fah baza mu taba yarda baka da budurwaba,kawai dai kana boye mana ne",anan se na ce toh tunda ina boye muku ne ai se ku binciko.Haka dai a ta tafiya a haka.Cikin ikon Allah na kammala Secondary na a 2018.A wannan shekaran kuwa bayan da na kammala.Ban dadeba kawai se Allah ya sanyo min Khaleesat cikin rayuwata.


Mu yi soyayyarmu ba damuwa se shakuwa,ban mantawa,babban sallah ta zo,se na kirata na ce,zaki zo ziyara ne,se ta ce:"Wlhy sallah ma ya zo bata jin dadi ina kwance ne",se na ce Allah sarki,Allah ya baki lafiya.Har bayan babban sallah dai bamu haduba,ni ban bukaci hakanba,dayake dama na ce se ta bukata kafin nakai mata ziyara.Toh wata rana na kirata se muke hirarmu,se take cewa My yau she zaka zo,se na yi dariya na ce:Ai kece baki so na zo ba,saboda baki gayyacenba kuma kin san duk wurin da ba'a gayyaceka ba,in kaje ba a samun masauki mai kyau.Se ta yi dariya ta ce:"Toh na gayyaceka shikenan".Se na ce eh,to na amsa.Zuwa ranar Asabar zan zo.Ta ce:"Allah ya kaimu amma naji dadi".


Ranar Asabar ta zo,na shirya na tafi,se na tsaya a U/bawa wurin Mallam Labiru,dayake bai dade da dawo daga karatu a kasar Burkina-faso ba,na tsaya mu gaisa.Se nake cewa zan shiga Saminaka ne,wurin Khaleesat,se ya ce:"Ban ganetaba ni dayake yawancin sisters na saminaka,ban sansuba.Yanzu in ba wadan suka yi aureba".Se na ce,kanwar Mallam Saifullahi fa,se ya ce,ok ya gane,ya santa kila sunanta ne ya bace mishi.Nan dai na ce,zamuje ne ka rakani.Mu fita mu hau mashin mu je layinsu,har mu karasa cikin-fudiya.Dayake Asabar ne da safe suna karatu.


Bayan mun fito,se wani schoolmate nawa ya fito,ya ce:"Uhmm.Kuna neman wacece,se mu ce Khaleesat ce",se ya ce ka ce budurwanka.Se na yi dariya na ce Aa,se ya ce:"Ai mutumiyata ce sosai na san komai,na shiga na kira muku ita ne".Se na ce:Aa ka bari se kun tashi,saboda in ta fito zan yanke mata karatu.Nan dai bamu haduba se bayan sun tashi,karfe 2,se mu je mu yi sallar Azahar.Mu dawo se na Kirata,dayake dama na fada mata na shigo din,se ta ce muna ina yanzu,se na ce gamu nan mun yi sallah,amma yanzu zamu dawo.Nan dai mu dawo.Mu zo kofar gidansu,mu zauna.Se na kira number nata,kawai se ba'a dagaba,na kara se naji kanwarta ta dauka.Se na ce,ina Khaleesat take,se ta ce:"Dazu ta fita".Nan se na ce:Ki dan kai mata wayar in ba ta yi nisaba.Toh bayan mun gama wayar,se na hango wani Schoolmate nawaa se na ce,yauwa zo shiga dan Allah ka kira min Khaleesat,se ya ce.Ai kawai ku shiga,bata fitowa se dai ku shiga,se na ce:Aa ni ban zo da shirin hakaba.Ka shiga kawai ka kirata.Se ya ce:"Ai ko na fada muku zai yi wuya ta fito,ban san dai son da takema".Se na ce ka shiga kawai in ka kirata in ma bata fito ba shikenan se mu wuce.


Muna cikin magana,kawai se ta zo ta wuce ta shiga gida,toh bayan ta shiga cikin zauren gidan, se na bita da kallo haka.Ita kuma bayan ta shiga zauren gidan lokacin itama ta juyo ta leko,ai ko tana lekowa mu hada Ido,se ta yi murmushi,nima haka ta shige ciki,se wata kanwarta ta fito se naji tana cewa Jameel Ramin-Kura ne ko.Nan dai nasa Daha ya shiga ya kirata.


Muna zaune mu uku,se gata ta fito,nan dai duk ta wuce su ta zo gurina.Ta tsaya.Se ta gaishen lokacin har ta tsuguna,bayan mun gaisa,se ta gaida sauran,nan dai Daha ya ce:"Ni zan tafi tunda ta fito".Mu fara hira ta zauna,se nake cewa kin zaunar damu da har na kusa fushima,se ta yi dariya ta ce:"Ku yi hakuri,na ce:Uhmm o'o ni bazan yi ba,se na miki hukuci,se ta yi dariya ta ce:"To Allah yasa ba bulala ba ne,domin ina tsoron bulala",se na yi dariya na ce.Lallai kam,toh ba bulala ba ne,ai hanuna bazai iya hukunta ki ba.Se na ce:Yau se kin rakani har garinmu,tun da kin zaunar damu.Se tayi dariya ta ce,toh tashi muje ai ga bakin titi can muje a sama mota.Nan dai mu tashi muna tafiya muna hira.Se mu zo daidai wani katanga,mu tsaya,mu cigaba da hirarmu.


Nan ta fara,ban labari,har take ban wani labarin lokacin da suke school a kaduna ta ce ita ba'a dokanta,duk wanda ya daketa kuwa zai sani.Ta ce wata rana wani mallami ya daketa ta yi kuka-tayi kuka,har da burgime.Nan se wani mallami ya zo ya bata hakuri,ya ce wa ya taba mana ke sharifiyya,Yau zai sani.A zo dai wancan da ya daketa,ya zo ya bata hakuri.Ta ce tun daga nan bai sake dukantaba.Se na yi dariya na ce:Nima ina tsoron bulala,amma in a fara min shikenan.Ta ce min bari ta zo,ta shiga gida ta dauko wayar Ummah,bayan ta dawo,se ta kamo hotunanta ta yi ta nunamin,ta kamo hotunanta tare da Ummah,ta nuna min ta ce,ita da umma ce da Babban sallah din nan mu dauka,se na ce gashi ban zo da babban wayataba da kin turamin,yanzu in ace za a tura ta bluetooth zai bada wahala.Kila ma yaki budewa.


Muna ta hira dai mu dade,wanda mu zo tare Mallam Labiru gefe guda suna tare da yayanta Ibraheem,se naji yana cewa:Wanna waye,se Mallam Labiru ya ce,dan Ramin-Kura ne,ya ce okay.Mu cigaba dai muna cikin farin-ciki ta yi ta ban labarin rayuwarta.Tun ina magana,na ce se kawai cewa nake eh,inaji-inaji.Se ga wani nan dan uguwansu ya zo zai wuce,se ya ce:"Lallai ma yarinyar nan,da rana nan ne kk hira,ko kunyarmu se ta masa dariya ta ce:"Uhmm mijin nawa".


Anan dai se na kalleta,na ce kallo ni,mu hada ido,se naga ta dan canza kamar taji kunya na,se nake ce mata wai yau she ne burinmu zai cika,se ta dago kai ta yi dariya ta ce:"Itama bata saniba,amma tana nan tana addu'a",se na ce toh Allah ya cika mana burinmu,se ta ce Ilahi ajib lana.Nan dai daga karshe se Mallam Labiru ya gaji da jiranmu.Nan dai ta ce min,ya gaji ya kamata mu tsaya anan,se na ce toh,lokacin se naga wani littafi nata,na addu'oi se na ce,wana littafi ne wanan se ta ban na gani,na bude se na ce:Ina so zan je na duba,in zan dawo gaba na dawo miki da shi,se ta ce"Kai littafin nan kusan kowa in ya gani se ya ce na bashi aro,boyewa nakema,yau na amso a gun wata kawata itama ta ara,kwana uku se yau ta ban".Nan se na ce,ai littafin ne akwai abubuwa masu amfani.Nan dai ta bani,ta ce se yaushe zan dawo,na ce:Monday in sha Allah,mu gama hirarmu Mallam Labiru ya taso,se cikin dariya,take ce mishi babana ka yi hakuri fa nan dai mu ban kwana,se taje kofar shiga gida ta tsaya,ta ce ita bazata shigaba se taga tafiyarmu,domin ita bata son wani abu ya cutar dani,se nima na ce:Ba zan tafiba se naga kin shiga gida,saboda kar wani abu ya cutar min dake.Se take cewa ai ni ba abun da zai cutar dani.Se na ce toh ai ni namiji ne zan iya kare kaina.Se ta yi dariya ta ce,toh ai na fika jarumta.Haka dai dakyar ta shiga zauren gidan,bata karisa cikiba se da taga mun tafi.


Haka dai,mu dawo na ajiye Mallam Labiru a u/bawa,ni kuma na shiga mota na koma gida cikin farin-ciki,da murna.Nan dai na dawo gida,se na shiga dakinmu na aje littafin nan.


Toh haka dai soyayyarmu ta cigaba,tun ban fadama Hajiyaba,taji labari,wata rana an taru a gidan,yayuna mata se suke cewa:Na Khaleesat,se Hajiya tayi dariya bata ce komaiba,se na ce:Uhmm sosai kuwa,se wata sister na ta ce,a saminaka zaka dauko kenan,se na ce eh.To anan ne se wata take cewa wai ko kunya,a gaban Hajiya din,se na yi dariya.


Toh haka dai,Monday ta zo,se na samu mashin na dauki,mutum biyu,mu tafi,da mu je U/bawa se mu sauke Nazee,mu tafi mu biyu da Abubakar,toh se muje mu samu tana makaranta,bata dawoba tukun.Nan se na kirata ta ce ai ta dawo,se na ce ai mu mun je ma al-huffaz ne,muna ciki yanzu,amma gamunan dawowa.Se ta ce toh.Bayan mun dawo se na kirata na ce,muna cin abinci ne,se tayi dariya ta ce lallai kam,kun sha yawo a saminaka.Da mu gama muje se na Kira number nata,bai shigaba,na kara se ya shiga ba'a daukaba,daganan na ce ma Abubakar kana ji mu jira kadan in bata fitoba mu tafi kawai,muna maganar,ashe tana zuwa tana jinmu.Nan dai ta ta ce ku yi hakuri,ai tuntuni ina cikin fudiya,nan su gaisa da Abubakar,ya ce bari ya zo.Se na ce:Toh,nan mu cigaba da hirarmu,har nake cewa yau ma kin sa munta jira koh,ku mata akwai jan aji,se ta yi dariya ta ce:"Ai kawuce jan aji guna".Nan dai se na ce toh se na miki hukunci yau,kuma bazan hakuraba.Se ta ce:"Uhmm wana hukunci ne".Na ce:kije ki nemo Sweet(lokacin da kwai wani sweet,mai dadi da ba ko ina ake samunaaba),se na ce shi nake so,se ta yi dariya ta ce:"Kamin hakuri se ka dawo nan gaba toh in baka",Se lokacin naga zobe a hannunta.Se na ce yauwa ga zobe nan ki fansa da shi.Anan se ta ce:"Wlhy na magani ne,bata cirewa amma in ina so gashi,se ta fara kokarin cirewa,se na ce.Aa kibarshi.Se take cewa:Tana da wani a gun yayanta,ko taje ba zata gansa ba da ya amso min.Se na ce ba komai.Ta ce amma zata amsa min.


Nan se Abubakar ya dawo,se yake cewa na baku minti uku,se tayi dariya ta ce,lallai mu din ne zaka bamu lokaci,ai ko zaka gaji da jira,ai ko fah ta dauko wata maganar.Karshe dai se Abubakar ya kiran,na je(dayake dama na ce zan ara wayarsa na dauketa hoto,saboda ban dashi),se ya ce min ga wayar,ko ka fasa ne.Se na amsa.Na koma wurinta.Mu ci gaba da hira,se nake cewa,banda hotonki ko daya a wayana bari in dauke ki,se ta ce min,bata daukar hoto ai,na ce ni dai se kin dauka.Daganan ne se ta ce:"Toh mu ga wayar".Na bata se ta ce,toh ni dai se dai ka shigo mu dauka tare,se na amsa wayar na kamo camera selfy,ta shigo mu dauka,se itama ta amsa na tsaya ta dauka.Se ta yi dariya ta ce,yanzu shikenan hankalinka ya kwanta,se na ce eh.Nan dai dayake mun sameta a school ne,se ta ce:"Bari ta koma mallam ya shiga ajinsu".Se na ce toh shikenan,yanzu se wani lokaci.Nan mu yi ban kwana.


Toh anan hanyarmu ta komawa,se muke hira haka da ni da Abubakar,nake cewa:Ni fah sonta nake da aure,se ya ce:"Wlhy nama murna,domin yarinyar tana sonka,kuma ta iya mu'amala",se na ce:Wai wasu suna cewa wai ta min girma,se ya ce wana girma,ba kana sonta tana sonka ba,ai kawai ka cigaba da nema ba wani girma.Nan dai ya kara min kwarin gwiwa,naji na kara sonta.


Allah ya miki rahma ya amsa uzurinki.


Zan ci gaba...

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post