@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
TSAGERANCI SUKE MANA IN JI IBN KHADDAB
Za ka samu da yawa matsalolin da ake samu a rayuwa ana samunsu ne sakamakon saba umarnin Manzon Allah (S. A. W. W). Da ace ana biyayya ga umarnin Annabi (S. A. W. W) ba tare da anyi masa jayayya ba, to, da ba za a sami matsala cikin zamantakewa a rayuwa ba.
Zamantakewar aure na yiwuwa ne ta hanyar haquri, juriya da kuma yin adalci cikinsa.
Ya zo cikin hadisi yadda matan Sahabbai suka riqa kuka game da dukan da mazajensu ke yi musu har Annabi (S. A. W. W) ya jaddada gargadinsa a kansu game da wannan mummunan aiki.
Hadisi ne da muka kawo muku cikin Babin yin wasiyya ga mata cikin Riyadus-Saliheen, ga shi kamar haka;
باب الوصية بالنساء
حديث رقم :279
وعن إياس بن عبد الله بن أَبي ذباب رضي الله عنه قَالَ:
قَالَ رَسُول الله صلى الله عليه وسلم: (لاَ تَضْرِبُوا إمَاء الله) فجاء عُمَرُ رضي الله عنه إِلَى رسولِ الله صلى الله عليه وسلم فَقَالَ: ذَئِرْنَ النِّسَاءُ عَلَى أزْوَاجِهِنَّ، فَرَخَّصَ في ضَرْبِهِنَّ، فَأطَافَ بآلِ رَسُول الله صلى الله عليه وسلم نِسَاءٌ كَثيرٌ يَشْكُونَ أزْواجَهُنَّ، فَقَالَ رَسُول الله صلى الله عليه وسلم: (لَقَدْ أطَافَ بِآلِ بَيتِ مُحَمَّدٍ نِسَاءٌ كثيرٌ يَشْكُونَ أزْوَاجَهُنَّ لَيْسَ أولَئكَ بخيَارِكُمْ) رواه أَبُو داود بإسناد صحيح.قوله: (ذَئِرنَ) هُوَ بذَال مُعْجَمَة مفْتوحَة، ثُمَّ هَمْزة مَكْسُورَة، ثُمَّ راءٍ سَاكِنَة، ثُمَّ نُون، أي: اجْتَرَأْنَ، قوله: (أطَافَ) أيْ: أحَاطَ
Daga Iyaasin Bn Abdullahi Bn Abiy Zubaba (R. A) yace,
Manzon Allah (S. A. W. W) yace:
" KADA KU BIGI BAYIN ALLAH (mata raunana) ."
Sai Umar yazo wajen Manzon Allah (S. A. W. W) yace,
" AI TSAGERANCI MATA KE YI GA MAZAJEN NASU ."
Sai yayi rangwame game da dukan nasu. Sai ga mata nan masu yawa suna kewayawa kan Iyalan Annabi (S. A. W. W) suna kokawa (game da duka) daga mazajensu.
Sai Manzon Allah (S. A. W. W) yace,
" HAQIQA MATA MASU YAWA SUN KEWAYE IYALAN GIDAN ANNABI SUNA KOKAWA GAME DA MAZAJENSU, LALLE WADANNAN (mazaje masu dukan matansu ) BA ZABABBUNKU BANE ."
A wani hadisi kuma cikin wannan Babin an kawo kamar haka;
باب الوصية بالنساء
حديث رقم :274
وعن عبد الله بن زَمْعَةَ رضي الله عنه:
أنَّهُ سَمِعَ النَّبيّ صلى الله عليه وسلم يَخْطُبُ، وَذَكَرَ النَّاقَةَ وَالَّذِي عَقَرَهَا، فَقَالَ رَسُول الله صلى الله عليه وسلم: {إِذ انْبَعَثَ أشْقَاهَا} انْبَعَثَ لَهَا رَجُلٌ عَزيزٌ، عَارِمٌ مَنيعٌ في رَهْطِهِ)، ثُمَّ ذَكَرَ النِّسَاءَ، فَوعَظَ فِيهنَّ، فَقَالَ: (يَعْمِدُ أحَدُكُمْ فَيَجْلِدُ امْرَأتَهُ جَلْدَ العَبْدِ فَلَعَلَّهُ يُضَاجِعُهَا مِنْ آخِرِ يَومِهِ) ثُمَّ وَعَظَهُمْ في ضَحِكِهمْ مِنَ الضَّرْطَةِ، وَقالَ: (لِمَ يَضْحَكُ أَحَدُكُمْ مِمَّا يَفْعَلُ؟! (1). مُتَّفَقٌ عَلَيهِ.(وَالعَارِمُ) بالعين المهملة والراء: هُوَ الشِّرِّيرُ المفسِدُ، وقوله: (انْبَعَثَ)، أيْ: قَامَ بسرعة.ــــــــــــــــــــ(1) قال النووي في شرح صحيح مسلم 9/162 (2855): (في الحديث النهي عن ضرب النساء لغير ضرورة التأديب، وفيه النهي عن الضحك من الضرطة يسمعها من غيره).
Daga Abdullahi Bn Zam'ata (R. A), cewa ya ji Annabi (S. A. W. W) yana Khuduba, kuma ya ambaci Taguwa (ta Annabi Salihu) da kuma wanda ya soketa, sai Manzon Allah (S. A. W. W) yace;
" YAYIN DA AKA AIKA MAFI SHAQAWARSU. "
An aika mata ne wani mutum mabuwayi, mafi hasara cikin jama'a.
Sa'an nan ya ambaci mata, yayi wa'azi a kansu yace,
" 'DAYANKU NA TINQAHU YA DOKI MATARSA (don wani kuskuren da yayi masa) IRIN DUKAN BAWA, MAI YIWUWA NE (don ba shi da kunya) YA NEMI SADUWA DA ITA A QARSHEN YININSA ."
Sa'an nan yayi musu wa'azi cikin dariyar da suke yi game da tsagerancin, yace,
" DON ME 'DAYANKU KE YIN DARIYA GAME DA ABINDA SUKE AIKATAWA ?"
Kenan duk mazajen da ke dukan matansu ba zababbu bane cikin al'ummar Manzon Allah (S. A. W. W).
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
(08126385470)
9th November, 2020/ 23rd Rabi'ul-Awwal, 1442.