Kwadaitarwa Game Da Yin Sallar Nafila A Cikin Gida !!!


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


KU SANYA SALLAR NAFILFILUNKU CIKIN GIDAJEN KU 


Yin sallar farilla ga maza an fi son yinta a masallaci sabanin sallar mata, duk da cewa yin sallar mata a masallaci halas ne amma suyi ta cikin gidajensu kuma cikin dakinsu yafi girman lada. 


Kuskure ne babba ace mutum yana da lafiyarsa kuma ba bisa wani uzuri mai qarfi ba ace ya riqa yin sallarsa a gida ba tare da zuwa masallaci ba. Ko da ace mutum ya makara da zuwa masallaci akan lokaci ya daure ya tafi masallaci yayi sallah ko da shi kadai ne tafi girman lada fiye da yayi ta a gidansa. 


Yin sallar farilla a masallaci cikin jam'i na qarawa mutum mutunci da soyuwa wajen mutanen kirki bayan ladan da yake samu. 


Ita kuwa sallar nafila ko ma wacce iri ce yinta a cikin gida yafi girman lada, hatta sallar tarawihi wacce Umar ya qirqiri yinta a masallaci cikin jam'i. 


Akwai hadisai da dama wadanda suke kwadaitar damu yin sallar nafila cikin gidajenmu. Saboda haka yinta cikin gidaje shine mafi soyuwa wajen Annabi (S. A. W. W) kuma mafi girman lada gare mu. 


Ga riwayoyin nan kamar haka; 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼



435 - (1) [صحيح] عن ابن عمرَ رضي الله عنهما؛ أنّ النبي - صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ - قال:

"اجعلوا من صلاتِكم (1) في بيوتِكم، ولا تَتَّخِذوها قبوراً (2) ".


رواه البخاري ومسلم وأبو داود والترمذي والنسائي


Daga Ibn Umar (R. A), Annabi (S. A. W. W) yace, 


" KU SANYA DAGA SALLOLINKU CIKIN GIDAJEN KU, KADA KU RIQE TA (gidan tamkar) QABURBURA ."

.


436 - (2) [صحيح] وعن جابرٍ -هو ابنُ عبد الله رضي الله عنهما- قال: قال رسول الله - صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ -:

"إذا قضى أحدُكم الصلاة في مسجدِه فليجعل لبيته نصيباً مِن صلاتِه، فإنّ الله جاعلٌ في بيتِه مِن صلاتِه خيراً".

رواه مسلم وغيره.


Daga Jabir, shine Ibn Abdullahi (R. A) yace, Manzon Allah (S. A. W. W) yace, 


" IDAN 'DAYANKU YA GAMA SALLAH (ta farilla) A MASALLACINSA, TO, YA SANYA WANI KASO NA SALLARSA A GIDANSA, DOMIN ALLAH ME SANYA ALKHAIRI NE CIKIN GIDAN NASA DAGA SALLARSA ."


437 - (3) [صحيح] ورواه ابن خزيمة في "صحيحه" من حديث أبي سعيد (3).


Ibn Kuzaimata ya riwaito cikin sahihinsa daga hadisin Abiy Sa'eed (misalin na sama). 


438 - (4) [صحيح] وعن أبي موسى الأشعري رضي الله عنه عن النبي - صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ - قال:

"مَثَلُ البيتِ الذي يُذكرُ اللهُ فيه، والبيتِ الذي لا يُذكر اللهُ فيه، مَثَلُ الحيِّ والميِّتِ".

رواه البخاري ومسلم. (4)


Ya inganta daga daga baban Musa Al-Ash'ariy, daga Annabi (S. A. W. W) yace, 


" MISALIN GIDAN DA AKE AMBATON ALLAH A CIKINSA, DA GIDAN DA BA A AMBATON ALLAH A CIKINSA, MISALIN RAYAYYE NE DA MATACCE ."


Mun tattaro muku wadannan riwayoyi ne daga littafi mai suna (SAHIHU JAAMI'US-SAGEER) 


Saboda haka mu dage wajen yawaita sallolin nafila cikin gidajenmu don samun albarka cikinsu. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda. 


          (08137925034)


21st November, 2020/ 6th Rabi'us-Sani, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post