Wasiyyar Manzon Allah (S.A.W.W) Kafin Shahadar Sa !!!

 


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


BA A CINYAR UMMUL-MUMINA A'ISHA YAYI SHAHADA BA 


Akwai wasu riwayoyi Isra'iliyat wadanda aka riwaito wai cewa Manzon Rahma (A. A. W. W) akan cinyar Ummul-mumina A'isha ya rasu, wannan kuwa na daga cikin qarerayin da ake qirqirowa ne don a nuna wani matsayi na wani wanda ba haka bane. 


Amma dai abinda muke son kawowa anan shine wani bangare daga cikin wasiyyoyin da Annabi (S A. W. W) yayi ne kafin shahadarsa. 


1- ما، الأمالي للشيخ الطوسي الْمُفِيدُ عَنِ الْجِعَابِيِّ عَنْ يُوسُفَ بْنِ الْحَكَمِ عَنْ دَاوُدَ بْنِ رُشَيْدٍ عَنْ سَلَمَةَ بْنِ صَالِحٍ عَنْ عَبْدِ الْمَلِكِ بْنِ عَبْدِ الرَّحْمَنِ عَنِ الْأَسْعَدِ بْنِ طَلِيقٍ قَالَ سَمِعْتُ الْحُسَيْنَ بْنَ الْعَرَبِيِّ «1» يُحَدِّثُ غَيْرَ مَرَّةٍ عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ مَسْعُودٍ قَالَ:


Riwaya ce wacce ta tuqe kan Abdullahi Bn Mas'ud (R. A) yace; 


نَعَى إِلَيْنَا حَبِيبُنَا وَ نَبِيُّنَا ص نَفْسَهُ فَأَبِي «2» وَ أُمِّي وَ نَفْسِي لَهُ الْفِدَاءُ قَبْلَ مَوْتِهِ بِشَهْرٍ فَلَمَّا دَنَا الْفِرَاقُ جَمَعَنَا فِي بَيْتٍ فَنَظَرَ إِلَيْنَا فَدَمَعَتْ عَيْنَاهُ ثُمَّ قَالَ


" Masoyinmu kuma Annabinmu (S.A.W.W) ya miqa rayuwarsa zuwa gare mu. 


Mahaifinna da mahaifiyata da kuma kaina fansa gare Shi, gabannin mutuwarsa da wata guda (one month) . Yayin da rabuwa tayi kusa sai ya tattaramu a cikin gida , ya kalle mu, sai ga hawaye na kwarara daga idanuwansa, sannan yace; 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


 مَرْحَباً بِكُمْ حَيَّاكُمُ اللَّهُ حَفِظَكُمُ اللَّهُ نَصَرَكُمُ اللَّهُ نَفَعَكُمُ اللَّهُ هَدَاكُمُ اللَّهُ وَفَّقَكُمُ اللَّهُ سَلَّمَكُمُ اللَّهُ قَبِلَكُمُ اللَّهُ رَزَقَكُمُ اللَّهُ رَفَعَكُمُ اللَّهُ 


" MARABA DA KU, ALLAH YA RAYAR DA KU, 


ALLAH YA TSARE KU, 


ALLAH YA YA TAIMAKE KU (ya ba ku nasara), 


ALLAH YA AMFANAR DA KU, 


ALLAH YA SHIRYAR DA KU, 


ALLAH YA DATAR DA KU, 


ALLAH YA KUBUTAR DA KU, 


ALLAH YA KARBA MUKU, 


ALLAH YA AZURTA KU,


ALLAH YA 'DAUKAKA KU.


أُوصِيكُمْ بِتَقْوَى اللَّهِ وَ أَوْصَى اللَّهُ بِكُمْ إِنِّي لَكُمْ نَذِيرٌ مُبِينٌ أَنْ لَا تَعْلُوا عَلَى اللَّهِ فِي عِبَادِهِ وَ بِلَادِهِ فَإِنَّ اللَّهَ تَعَالَى قَالَ لِي


INA YI MUKU WASIYYA DA TSORON ALLAH , KUMA ALLAH YAYI MUKU WASIYYA GAME DANI CEWA , LALLE NI MAI GARGADI NE GARE KU MAI BAYYANARWA (da gaskiya). 


KADA KUYI GIRMAN KAI GAME DA ALLAH CIKIN BAYI DA KUMA GARINSA. DOMIN ALLAH (T) YA CE MIN ;


 وَ لَكُمْ تِلْكَ الدَّارُ الْآخِرَةُ نَجْعَلُها لِلَّذِينَ لا يُرِيدُونَ عُلُوًّا فِي الْأَرْضِ وَ لا فَساداً وَ الْعاقِبَةُ لِلْمُتَّقِينَ «3»

"KUMA LALLE WANCAN GIDAN LAHIRA GARE KU YAKE , MUNA SANYA SHI GA WADANDA BA SA NEMAN 'DAUKAKA CIKIN QASA KUMA BA SA (yin) FASADI . KUMA KYAKKYAWAN QARSHE NA GA MASU TAQAWA NE ."


 وَ قَالَ سُبْحَانَهُ أَ لَيْسَ فِي جَهَنَّمَ مَثْوىً لِلْمُتَكَبِّرِينَ «4»


Sannan Allah (S. W.A) yace; 


" ASHE BAI KASANCE CIKIN JAHANNAMA MAKOMA GA MASU GIRMAN KAI BA ?"


 (1) في المصدر: العرنيّ.


 (2) في المصدر: فبأبى.


 (3) القصص: 83.


 (4) الزمر: 60.


 (5) أمالي ابن الشيخ: 129.


 قُلْنَا مَتَى يَا نَبِيَّ اللَّهِ أَجَلُ ?قَالَ 


Muka ce, yaa Annabin Allah, yaushe ne ajalinka? Yace; 


دَنَا الْأَجَلُ وَ الْمُنْقَلَبُ إِلَى اللَّهِ وَ إِلَى سِدْرَةِ الْمُنْتَهَى وَ جَنَّةِ الْمَأْوَى وَ الْعَرْشِ الْأَعْلَى وَ الْكَأْسِ الْأَوْفَى وَ الْعَيْشِ الْأَهْنَإِ 


" LOKACI YA QARATO, DA KUMA MAKOMA ZUWA GA ALLAH , DA KUMA ZUWA MAGARYAR TUQEWA, DA ALJANNAR MAKOMA, DA AL'ARSHI MADAUKAKI, DA KOFUNA WADANDA AKE CIKAWA, DA KUMA RAYUWA MAI DADI ."


قُلْنَا فَمَنْ يُغَسِّلُكَ

Muka ce, waye (kuma) zai wanke ka (Idan kayi wafati) ?


 قَالَ أَخِي وَ أَهْلُ بَيْتِيَ الْأَدْنَى فَالْأَدْنَى «5».


Yace, " 'DAN'UWANA (Ali) DA IYALAN GIDANA NA KUSA DANA KUSA ."


(Wannan kuwa shine abinda ya auku, domin yayin da yayi wafatin duk wadanda ake cewa wai sune makusantarsa a girma su watse zuwa zabe (election) a Saqeefah, wadannan makusantarsa na haqiqa su suka yi masa wankan).


2- ما، الأمالي للشيخ الطوسي ابْنُ الصَّلْتِ عَنِ ابْنِ عُقْدَةَ عَنْ مُحَمَّدِ بْنِ سُلَيْمَانَ عَنْ إِسْمَاعِيلَ بْنِ أَبَانٍ عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ مُسْلِمٍ الْمُلَائِيِّ عَنْ أَبِيهِ عَنْ إِبْرَاهِيمَ بْنِ عَلْقَمَةَ بْنِ الْأَسْوَدِ عَنْ عَائِشَةَ قَالَتْ 

A wannan riwaya kuma wacce ta tuqe kan Ummul-muminina A'isha tace; 


قَالَ رَسُولُ اللَّهِ ص لَمَّا حَضَرَهُ الْمَوْتُ ادْعُوا لِي حَبِيبِي فَقُلْتُ‏


Yayin da mutuwa ta zowa Manzon Allah (S.A.W.W) sai yace; " KU KIRA MIN MASOYINA (na gaskiya ). " Sai nace, 


__________________________________________________


                  

ادْعُوا لَهُ ابْنَ أَبِي طَالِبٍ فَوَ اللَّهِ مَا يُرِيدُ غَيْرَهُ فَلَمَّا جَاءَهُ فَرَّجَ الثَّوْبَ الَّذِي كَانَ عَلَيْهِ ثُمَّ أَدْخَلَهُ فِيهِ فَلَمْ يَزَلْ مُحْتَضِنَهُ حَتَّى قُبِضَ وَ يَدُهُ عَلَيْهِ «1»


" Ku kira masa dan Abiy 'Dalib, wallahi ba wani yake nufi ba bayan shi . To, a yayin da yazo sai ya yaye mayafin da ke kansa, sannan ya shigar da shi cikinsa . Bai gushe ba yana ta rarrashinsa har aka karbi ransa hannunsa na kansa ."


      بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج‏22، ص: 456


NB: A lura da kyau, tunda kuwa hakane sune lullebe ne cikin bargo daya da Imam Ali (A. S) har yayi wafati, to, ta yaya ya kasance kenan kan qirjin Ummul-muminina A'isha ?


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da Ado Isah Guda. 

     (08126385470)


13th October, 2020/ 26th Safar, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post