Wanda Ya Zalumci Fadimatu Bayan Raina Tamkar Ya Zalumce Ta Ne A Halin Rayuwa Ta !!!


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

TSINANNEN ALLAH NE DUK WANDA YA CUTAR DA MANZON ALLAH (S. A. W. W) 

Masu karin magana na cewa; " KO MAYE NA JIN TSORON IDON UWA ."

Amma a gaskiyar magana ba haka bane, domin lokacin da Maye zai kama yaro uwarsa ma ba za ta sani ba. Saboda haka zai iya yin komai a lokacin da yaga dama, sai dai kawai kariyar Ubangiji. 

Kasancewar Annabi (S. A. W. W) na raye bai hana a cutar da shi ba ballantana bayan rayuwarsa, komai ya faru kafin da bayan rayuwar tasa (S. A. W. W. 

Ya zo cikin tafsirul-Qummy dangane da ayar da Allah (T) ke cewa; 

" إِنَّ الَّذِينَ يُؤْذُونَ اللَّهَ وَ رَسُولَهُ لَعَنَهُمُ اللَّهُ فِي الدُّنْيا وَ الْآخِرَةِ وَ أَعَدَّ لَهُمْ عَذاباً مُهِيناً[5] ."

" LALLE WADANDA SUKE CUTAR DA ALLAH DA MANZONSA , ALLAH YA LA'ANE SU A DUNIYA DA LAHIRA , KUMA YAYI MUSU TANADIN AZABA TA TOZARWA ." 

قَالَ نَزَلَتْ فِيمَنْ غَصَبَ أَمِيرَ الْمُؤْمِنِينَ حَقَّهُ وَ أَخَذَ حَقَّ فَاطِمَةَ وَ آذَاهَا وَ قَدْ قَالَ النَّبِيُّ ص

Yace, " Ta sauka ne kan wadanda suka qwacewa Amirul-Muminina (Aliyu Bn Abiy 'Dalib) haqqinsa , kuma suka karbe haqqin Fadimatu, suka cutar da ita . Haqiqa Annabi (S. A. W. W) yace; 

 مَنْ آذَاهَا فِي حَيَاتِي كَمَنْ آذَاهَا بَعْدَ مَوْتِي وَ مَنْ آذَاهَا بَعْدَ مَوْتِي كَمَنْ آذَاهَا فِي حَيَاتِي وَ مَنْ آذَاهَا فَقَدْ آذَانِي وَ مَنْ آذَانِي فَقَدْ

 آذَانِي اللَّهَ .وَ هُوَ قَوْلُ اللَّهِ‏ ,

.

" WANDA YA CUTAR DA ITA A HALIN RAYUWATA KAMAN YA CUTAR DA ITA NE BAYAN MUTUWATA. KUMA YA CUTAR DA ITA A BAYAN MUTUWATA KAMAR YA CUTAR DA ITA NE A HALIN RAYUWATA. HAQIQA WANDA YA CUTAR DA ITA NI YA CUTAR, KUMA WANDA YA CUTAR DANI HAQIQA YA CUTAR DA ALLAH .KUMA SHINE FADIN ALLAH (T); 

إِنَّ الَّذِينَ يُؤْذُونَ اللَّهَ وَ رَسُولَهُ‏ الْآيَةَ

" LALLE WADANDA KE CUTAR DA ALLAH DA MANZONSA..... "

__________________________

(1) الأحزاب: 57

بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج‏43، ص: 26

Allah ya qara mana shiriya. 

Daga wakilanmu na Bauchi zone. 

✍🏼 Tare da Ado Isah Guda. 

       (08126385470)

23rd October, 2020/ 7th Rabi'ul-Awwal, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post