Littafin Allah Da Sunnah, Ko Dai Littafin Allah Da Tsatson Annabi (S.A.W.W) ???



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


ABUBUWA BIYU DA ANNABI YABAR MANA A BAYANSA 


Yana daga cikin dalilin da yasa wani Imami daga Imaman Ahlul-Bait (A. S) yake cewa; 


" KU RIQA KIYAYE ILIMIN DA ZA KU 'DURA A QWAQWALENKU FIYE DA YADDA KUKE KIYAYE ABINCIN DA ZA KU CI A CIKINKU ."


Illar abinda mutum zai ci shine kada yaci abinci mai guba (poison) ko gurbatacce wanda zai iya shafar lafiyarsa ko kuma wanda zaiyi sanadin barin duniyarsa. Shi kuma na ilimi shine mutum zai iya durawa qwaqwalwarsa abinda zai iya halakar da shi, sannan yayi sanadin fadawarsa cikin azaba a lahira. 


Akwai abubuwa biyu wadanda Annabi (S. A. W. W) ya bar mana su a Matsayin ababen riqo don kada mu halaka, sai dai an sami wadanda suka juyar da wannan abubuwa zuwa wani abin na dabam wanda hakan yayi sanadin halakar wasu ta hanyar jahiltar haqiqanin abinda aka bar mana don samun rabauta duniya da lahira. 


Bari dai mu leqa cikin Musnad na Imam Ahmad Bn Hambal muga me ya kawo cikin littafinsa don sanin gaskiyar magan.


Ga shi kamar haka; 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


10893- حَدَّثَنَا أَسْوَدُ بْنُ عَامِرٍ ، أَخْبَرَنَا أَبُو إِسْرَائِيلَ يَعْنِي إِسْمَاعِيلَ بْنَ أَبِي إِسْحَاقَ الْمُلَائِيَّ ، عَنْ عَطِيَّةَ ، عَنْ أَبِي سَعِيدٍ ، قَالَ : قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ : " إِنِّي تَارِكٌ فِيكُمْ الثَّقَلَيْنِ ، أَحَدُهُمَا أَكْبَرُ مِنَ الْآخَرِ ، كِتَابُ اللَّهِ حَبْلٌ مَمْدُودٌ مِنَ السَّمَاءِ إِلَى الْأَرْضِ ، وَعِتْرَتِي أَهْلُ بَيْتِي ، وَإِنَّهُمَا لَنْ يَفْتَرِقَا حَتَّى يَرِدَا عَلَيَّ الْحَوْضَ "


Aswadu Bn Ameer ya bamu labari, baban Isra'ila (yana nufin Isma'il Bn Abiy Ishaq Al-Mula'iy ) ya bamu labari daga Adiyyata daga baban Sa'id yace, Manzon Allah (S. A. W. W) yace; 


" LALLE NI ZAN BAR NAUYAYAN ABUBUWA BIYU A CIKINKU , 'DAYANSU YA FI GIRMA AKAN 'DAYA, LITTAFIN ALLAH MIQAQQIYAR IGIYA DAGA SAMA ZUWA QASA, DA KUMA TSATSONA IYALAN GIDANA.  


KUMA LALLE (su) BIYUN NAN BA ZA SU TABA RABUWA BA HAR SAI SUN RISKE NI A TAFKI NA !"


(Musnad Ahmad, hadisi me lamba 10,893).


            TAMBAYA 

          ------------------


To, dan Allah a ina ku ka samo cewa wai littafin Allah ne da Sunnah ?


Me yasa ku ke qoqarin kawar da Iyalan Annabi (S. A. W. W) daga cikin wannan wasicci ?


Shin, ko yin hakan shi zai nuna cewa ku masoyansa ne ?


Ashe ku ba ku san cewa haramun ne yiwa Annabi qarya ba ?



" FA'ATABIRUU YAA ULUL-ALBAAB "


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da Ado Isah Guda. 

       (08137925034)


7th October, 2020/ 20th Safar, 1442.


Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post