GYARAN JIKI: Zinariyar Mace


 

MA'ASUMAH NIGERIA NEWS UPDATE.

Gyaran jiki abu ne mai matukar muhimmanci a rayuwa da zamantakewa ta dan adam. Kamar yadda yake a addini wajibine mutum ya kasance yana kula da tsaftar jiki da muhalli, asali ma tsafta tana daga cikin cikar imani. 


Gyara ko tsaftar jiki wajibi ne ga maza da mata amma zamu fi karkata shawar-warinmu zuwa bangaren mata saboda tsaftarsu tafi muhimmanci kasancewarsu abin kwalliya na duniya.


A wannan dandali na ZINARIYAR MACE,zamu bada hanyoyi da shawarwari da zasu taimakawa yan uwanmu mata wajen kula da jikinsu. 


Zamuyi bayani akan wasu daga cikin muhimman wurin gyara gareki, bari mu fara da gyaran gashi.

Gashi na daga cikin abubuwa da suka fi daukan hankalin namiji a jikin mace. Namiji kan ji farin ciki a yayinda ya kalli ko ya taba gashin uwar gidanshi musanman idan gashinta ya kasance mai sheki ne tare da laushi sannan kuma baki.


Akwai hanyoyi da dama na gyaran gashi, zamuyi bayaninsu daya bayan daya:


Amfani da tafarnuwa da man zaitun: yanda zakiyi saiki samu tafarnuwan da dan yawa kamar sama da goma saiki baresu ki yanyanka sannan ki jikasu da man zaitun saiki bari yayi kwana uku ajike saiki soya ki ajiye kina shafawa akayi bayan awa daya a wanke.


Kokuma ki samu man amla da man kwakwa da zuma: yanda akeyi shine zaki zuba man amla kadan zuma itama idan amla ya zama cokali hudu to zuma ya zama zuma cokali biyu man kwakwa shima cokali biyu saiki zuba a ruwan zafi shi kuma kamar cokali hudu a gauraya kamar idan za'ayi shampoo sai ashafa akai bayan mintuna talatin shikenan sai kiyi shampoo dinki.

Don samun cigaban shirye-shiryen mu, Ku ziyarcemu a www.ma'asumah ng.com


Tare dani ummu Radiyya.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post