DAN SHI'A A ISLAMIYAR WAHABIYAWA 1


Gajeren Labari marigayi

 Muhammad Bin Ibrahim


An wallafa labarin nan tun a ranar 18/9/2017




Jikinta ya 'dan motsa daga kwanciyar da take. Idanuwanta suka bud'e. Ganinsu ya cilla zuwa ga wani agogo da ke kallonta daga saman bango a bayan ta kunna wutar d'akin. Qarfe 3:30 na dare daidai. Har zuwa lokacin qarar alam d'in wayarta ba ta daina ruri ba. Ta miqa hannu ta kashe. Ta yunqura. Bakinta ya furta kalmar "Bismillahi laahaula wa laa quwwata illa billah!" Ta bud'e band'aki ta shiga. Zuwa jimawa ta fito. Fuskarta da hannayenta da qafafuwanta duk jiqe da ruwa. Ta d'auko dardumarta ta kalli gabas.


Kamar kowane dare,  wannan ma raka'a biyu ta yi. Ta bi su da addu'ar Allah ya ba ta miji nagari tare da sauran ababen da ta saba yi wa addu'a cikin sakankancewa da fauwala wa Allah komai. Ta d'auko Qur'ani ta karanta izifi biyu daga surar Maryam. Zuwa wannan lokaci tuni 4:30 ta yi. Muryoyin kiran sallar ladanai sai amo suke yi ta kowace kusurwa.


Ta ajiye Qur'anin. Ta kishingid'a. A sannan ne zuciyarta ta halarto mata fuskarsa. "Yes, ba mummuna ba ne. Amma d'an Shi'a ne. Matsalarsa ke nan kad'ai. Ita kuma ta ci alwashin ba ita ba d'an Shi'a. Domin ba za ta yi tarayya da mai zagin Uwayen Muminai da Sahabban Annabi (s) ba. Ina! Sam wallahi!! Ta girgiza kai ita kad'ai!!!.


To amma kuma ta rasa me ya sa take jin natsuwa a duk lokacin da ya zo hira wurinta. Gashi kuma shi ba wani mai magana ba. Amma dai zuciyarta na samun sakina a hallararsa. Me ya sa? Ko dai tsaface ta ya yi? 'Yan Shi'an nan fa shu'umai ne. "No!" Ta ji wannan kalmar ta su'buto daga bakinta. Ba haka ba ne. Ba magani ya yi mata ba. Domin ko a bayansa ma tana jin dad'i da natsuwa idan tana tunaninsa. Kuma tunanin ne kad'ai yake kwantar mata da hankali. Sannan a duk lokacin da ta sakankance a gaban Ubangiji a kan roqonsa da ya ba ta miji nagari, shi ne kad'ai yake zuwa mata a rai. Shin zai yiwu duk hakan ya zama asiri? 'A'a!' Qwaqwalwarta ta ce.


Bayan ta ji an fara tayar da iqamar sallar Asuba ne sai nan take ta yanke cewa, gobe da yamma za ta je Islamiyyarsu ta yi wa Mudir maganar. Ta ji a ranta lallai tana buqatar ta shaida wa malaminta don ya 

ba ta shawarar da za ta fisshe ta a kan wannan rikitaccen lamari.

***          ***       ***


Sheikh Mustapha Khalil Al-Gusawi yana ofis yana rubuce-rubuce a kan fayil-fayil na makaranta sai ya ji siriruwar murya ta yi sallama. Ya amsa tare da d'aga kai. Wata matsakaiciyar yarinya ce ta shigo sanye da cikakken hijabi mai ruwan toka da niqabi baqi. Ya kalle ta, ya sake kallon fuskarta da nufin ko zai gane ta. Fahimtar hakan ya sa ta ce: "Malam, Barirah ce."


Jin haka sai murmushi ya bayyana a fuskarsa. "Ai ban gane ki ba Barirah, ki yi haquri." Ya nuna mata wurin zama a wata kujera da ke gaban qaton teburinsa da ke cike da takardu da litattafai.


"Ba komai Malam." Ta fad'a tana mai jinjina masa a rai saboda yadda yake kame kansa. Shi ne kad'ai bai da kalle-kallen mata a ilahirin malamai maza da ke wannan Islamiyya. Salihin bawa ne. Don haka ma ta ce bari ta kawo kukanta gare shi.


Bayan sun gaisa ne ta ce: "Malam dama wata matsala ce ke damuna, shi ne na ce barin in zo in nemi shawararka..." ta datse labarin daga nan da nufin ganin damuwarsa a kai.


"Na'am, ina jin ki Barirah." Cikin zaquwa ya ce.


"Malam ka san duk qawayena sun jima da aure? Kuma a gida ana yawan damuna a kai. Gashi ni kuma ban da wanda ya fito min sai wani d'an Shi'a..."


"Dan Shi'a!?" Sheikh Mustapha ya katse ta tare da riqe baki. "Subhanallah!!"


Barirah ta ci gaba: "E Malam, d'an Shi'a. Wata qawar babata ce ta turo min shi. Ni ban ma san shi ba. Ta ce Injiniya ne a Matatar Fetur ta Kaduna. Ta kuma ce matarsa ta rasu ta bar shi da yara biyu qanana. Wai yana neman wata salihar mata ce da zai aura. Shi ne ta ce masa wai ai ni ce na dace da za'binsa."


Sheikh Mustapha ya girgiza kai, "Lalalaala! Ai 'yan Shi'a ba musulmi ba ne. Mutanen da suke ba da aron farjin matansu. Mutanen da suke zagin Sahabbai. Ki raba kanki da wad'annan mutane Barirah. Babu alheri a tare da su. Ke dai ki je ki yi ta addu'a Allah ya ba ki miji nagari.


Barirah ta yi shiru na rashin jin dad'i saboda ganin yadda Malam bai tsaya ya natsu wurin fahimtar inda ta dosa ba.


A nasa 'bangaren sam sai bai ma kula da hatta wannan shirun da d'alibar tasa ta yi ba. Ya miqe ya cusa wasu fayil-fayil a durowar bango da ke saman kansa.


"Ai tsakaninmu da 'yan Shi'a sai dai kafirtawa." Ya fad'a yayin da yake qoqarin komawa ga kujerarsa ta zama.


Barirah ta miqe, "To Malam. Na gode." 


"Yauwa Barirah. In ya zo wurinki ki daina fita. Kin san 'yan Shi'a na da ilimin mand'iqi, yanzun nan zai hure mi ki kunne; kamar shed'anu suke ji."


"To Malam." Barirah ta fad'a yayin da qafarta ta hagu ke tsallake dokin qofar ofishin a hanyarta ta fita.


A yammacin sai ta ji sam ba ta son shiga aji karatu da yara. Damuwa ce ke cinta a rai matuqa. Gashi ta rasa wanda za ta fad'a wa. Ita mace ce mai zurfin ciki. Ko kad'an ba ta son wani ko wata su san halin da take ciki, musamman irin wannan da ya shafi alaqa. Ta shiga ofishin malamai ta zauna ita kad'ai. Muryar yara masu karanta qaramin littafin Kitabul Tawhid ta riqa dukan kunnuwarta. Hakan sai ya hana ta natsuwar da take son samu a wannan ke'bancewa da ta yi. Don haka sai ta sake nufar ofishin Mudir da nufin neman izinin komawa gida. Ta quduri aniyar neman hanzarin da cewa ciwon ciki ne ya hana ta sukuni.

***       ***       ***


Misalin 8:11 na dare Injiniya Isma'il ya yi fakin a qofar gidan su Barirah. Ya kira wayarta har sau uku amma ba ta d'auka ba. Ya d'an tsahirta har na tsawon minti 20, sannan ya sake kiran wayar, a wannan karon ma dai ba ta d'auka ba. Ya sake, shi ma dai ba ta d'auka. Ya bud'e mota ya fito, ya tsaya yana waige-waige ko zai ga qaramin yaro ya aike shi. Can ya hango wani, ya tura shi. Yaro ya dawo ya ce an ce ta yi barci.


Ya shiga mota, har zai tayar, sai kuma ya qara d'auko wayar tasa, ya yi mata tes, kana ya ja mota ya tafi.


Ita kuwa Barirah ashe duk kiran da Injiniya yake yi, a kan idonta ne. Hatta yaron da ya shigo kiranta, ta la'be ne, ta ce wa qaninta ya ce masa ta yi barci. Ta yi haka ne domin bin abin da Mudir ya ce mata, duk kuwa da cewa abin da ya ce d'in bai kwanta mata a rai ba. Amma dai sai take ganin gara ta guje shi kawai don kada ta hallaka kanta a lahira. 


Ta ji ciwon abin da ta yi masa. Amma a nata tunanin shi ne kad'ai mafita. Tana cikin haka ne, sai ta ji shigowar tes. Ta duba wayarta, ta ga daga gare shi ne:


"Salam. Malama, na zo amma sai na tarar kin yi barci. Hala gajiyar d'alibai ce ta sa ki gaba. Sorry pls.

Ma'assalam."


Tes d'in ya sa ta ga girman laifinta a ranta saboda ganin shi bai ma damu ya zaqulo mata laifin wulaqancin da ta yi masa ba. Tuni ya riga ya ba ta uzuri. Ta lura shi ko irin waige-waigen nan na maza bai dame shi ba. Ga rashin son magana. Ga sanyin mu'amala. Idan ya zo, zantukansa qalilan ne, shikenan kuma sai ya yi sallama ya tafi. Ga shi da natsuwa. Me ya sa ta yi masa haka ne? Ta tuhumi kanta. Amma kuma ai d'an Shi'a ne..., ta kuma kwa'bi kanta. 


Wai ita yaya za ta yi ne? 


Qwaqwalwarta ta yi mata kashedin cewa, yanzu fa shekarunta 35. Tun tana d'aliba a Islamiyyarsu ta rasa wanda zai ce yana sonta da aure a cikin malaman makarantar ko mutanen unguwa. Ta kuma san cewa don ba ta da wani kyawun a zo-a-a gani ne. Kuma iyayenta talakawa ne. Gashi ba ta yi boko mai zurfi ba. Iyakarta sakandare. Sauran qawayenta da ke da kyau da wad'anda iyayensu ke da qumbar susa, duk sun yi aure sun hayayyafa. An barta ta zama 'Innar-yara'. 'Dan Shi'ar nan shi ne kad'ai ya fito ya nuna yana sonta fisabilillahi. Shin haka za ta bar shi ya tafi? Idan kuma ba ta samu wani ba fa? Shin haka za ta qare rayuwarta ba miji?


Can kuma sai wata zuciyar ta ce mata, a kul, kika aminta da mai zagin Sahabbai! Ai kuwa gara ki mutu kina gwauruwa da ki auri d'an Shi'a.


A take kuma, sai qwaqwalwarta ta ce mata, wai shin mece ce Shi'ar nan ma tukuna da kowa ya tsana haka?


Ci gaba a nan gaba insha Allah.


_____________________________


Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post