Matan ku Suna Burge Ni, _Inji Wani Dan Izalah !!!~WANI BAWAN ALLAH DAN...........

A Garin Dabai Karamar Hukumar Danja ta Jihar Katsina Aka Haife Ni,acan na kammala Primary Har Zuwa Secondary.

Dayake Sayyid Yana Umartar mu da Yin Sana'a ko Neman Na Kai da Gujewa Zaman Kashe Wando da Kaucewa Zama Nauyi Akan Wani/Wasu,

An Tafi Dani karshi{Abuja}da Niyyar In Nasami aikin yi Nasami Kudi Insayi Form na Makarantar Gaba da Secondary In Cike,da Nufin In Allah yasa Suna na Yafita Sai Muzo muyi Shirin Tafiya Makaranta,

Farko Kafin Insami abin yi Baba Na Kuma Malami Na Malam Ahmad Ibraheem Karshi Yakaini Wurin Wani Mai Goro Akayi magana Dashi Akan Zai Rika bani Kwando Daya a Farashi Ni Kuma in kasa a Faranti/Tire In Zagaya Duk abinda Nasamu na Riba Nawa nee Halak Malak.

Nayi Wannan Sana'a din Ta Tallar Goro,Bayan Haka an Rika Samun aiki na Leburancin Aikin Siminti Shima Ina Zuwa,Inada Ogogi Ko Mastoci,Daga Ciki akwai babana Malam Abbas Karshi, Sai Malam Usman {Dattijo}Sai Muh'd Auwal Abdullahi {Abokina}

Bayan Wannan Dayake Gidan Daya Daga Cikin Abokaina Yana Makwabtaka da Fudiyya nee,Watarana naje Wurin sa Yana Wanki muna fiira Sai Maman Shi tazo tace Masa batace Masa idan Yana Gida yaji Yara Suna Wasa/Surutu/ ya Rika Zuwa Yana Musu karatu kafin Maluman Su Suzo ba,

Sai Yacemin Tunda Yana Wanki In Shiga kafin yagama ko Kuma kafin Maluman Su Karaso,Dayake Makarantar tanada nisa da Gidan kowane Daya a Cikin Maluman,

Hakanan Na Shiga Muka Faara Karatu Da Yaran Nan,Muna Cikin Yi Saiga Malaman Makarantar Nan Su Uku Reras Duk Sistoci,

Daga Cikin Su Akwai Umma na,Matar Wakilin Yan Uwa Na Abuja{Malama Fatima}Sai take Cemin dama Tanaso tayimin Magana akan In Rika Zuwa Ina Taimaka Musu,Sai nace Mata ta bangare na ba komi,Amma Dayake Ina Zuwa aikine Kuma bamu dawowa da wuri da har Zansamu Lokacin Dawowa a kasa Daga Inda muka Gama aikin Inzo in wanka intaho Makarantar,

Daga baya ansami Yadda akayi na Rika Zuwa Makarantar Ina Koyarda Yara abinda Allah Yasanar Damu,

To Gaskiya banyi yawo da kyau ba a biranen Nigeria,Amma Gaskiya Naga Tsare~Tsare Daga Yan Uwa Na Karshi Na Cigaba da Burgewa da ban Sha'awa,

Ta Bangaren Tarbiyyar Yaran Su Sai Ince Maka Bazaka taba Ganin Yaro/Yarinya Tana Kiran Sunan Wanda Yafita Kai Tsaye ba,Saidai In Namiji ne kaji Ance Uncle/Yaya Wane,In Kuma mace ce kaji Ance Aunty Wance,

Ta Bangaren Matasa Maza Kuma Sai Ince Maka Bazaka Taba Ganin Matashi Daga Dan Shekara Sha Takwas Zuwa Ashirin Yasa Kai Ya Shiga Gidan Sister's ba,

A'a,Saidai Ya Kwankwasa a aiko yaro/Yarinya Tazo Tagani,In an Sanshi ace Ya Tsaya Ana Zuwa,Idan Suka Shirya Sai a bashi Izinin Shiga,ko Kuma idan Sakon Bayarwa nee ya bayar a Shigar, In Kuma ba'asan Shi ba ace wayake nema in Yafadi in Yananan ace yajira a waje Yana Zuwa,In Kuma Bayanan a fada Masa,

Ta Bangaren Yan Matan Su Sai Ince maka Masu Kunya nee da Taya Iyayen Su Aiki Da Zumunci ga Juna,Basu Saka Kayan da Basu Dace ba in Zasu Fita Daga Gida ko Zasu bar Garin,

Basu Iya Gaida manya ko Iyayen su ko Wanin su a Tsaye,Akwai Wata ta taba kirana da Abdullahi Kai Tsaye batace Uncle Abdullahi ba Saida aka...........

Masu Karatu Kada in Cika ku da Surutu,

Da Fatan Baku manta da Taken Rubutu Na ba,

MATAN KU SUNA BURGE NI

Alakar Zama Anguwa Daya ta hadani da Wani bawan Allah Dan Izala nee a Fahimta,Amma Gaskiya Inka Duba Yadda yake da yadda yake Mu'amala da Mutane bazaka taba Cewa Dan Izala bane,

Watarana Muna Zaune a Masallacin Bye Pass Muna Hira Sai Yake Cemin "Gaskiya Matan ku Suna Burge Ni,

Sai Nace Masa Koh???da Nufin Ya karasa Maganar Yadda Zata bada ma'ana,

Sai Yake Cemin kaga Matan ku Basu Fita Daga Gida bada Izinin Mazajen su ba, Nace Masa Gaskiya nee,ai Addinin Musulunci nee ya Koyar da Hakan,Yace Yasani,Sai Nakece Masa Yataba ji ko karanta Inda Wata Mata Mahaifin ta ya rasu mijinta Bayanan taje wajen Annabi Muhammad {s.a.w.w.}akan Ya Zatayi Sai Manzo Yace lallai Sai Tabari Yadawo,kamar Ance Har Sau uku Tana Zuwa ko Annabi Zai Bata damar tafiya Amma Inaaaa,

Anyi Hakan nee don Nuna Girman Haqqi abin kiyayewa Akan Fitar Mace Zuwa Wani Wuri batare da Izinin mijinta ba.

Yakara Da Cewa kaga Matan ku Basu Fita ba gHijabi,

Sai Nace Masa ai Kuma naku Basu Fitowa ba Hijabin,Sai Yake Cemin bakaga Wance bane,yanamai nunamin Wata Mata Tana tuyar Waina/MaasaTa Fito Tun Daga gidan ta tazo har Inda take toya waina Maza Masu Wucewa aikin Kwadago Su Saya Amma ba Hijabi a Tare da ita Sai Gyale/Mayafi,Shi Kuma anyaye Shi Yazama Zuwa Dashi Bai amfani ba,

Bai Shiru ba ya Karamin da cewa Matan ku Basu sa Dangyalallen Hijabi Mara Ma'ana Nace Masa hakane,

Gaskiya Yan Uwa Na Garin Sunada Abubuwan da Za'ayi koyi dasu,

Nifa Tunda naje Garin Bantaba Ji ko Ganin Wata Sister a Waje Ta Tsaya Da Wani Wai Da Sunan Hira ba,

Sannan Yan Matan Su Basu Fita da dare Indai ba ranar Ta'aleem ba,

To Wai Mu da Muke da Wadannan Iyayen da Wadannan Yan Matan Har Muke Ganin Wasu Su Burgemu Har Muji Muna Son Su har Abin yakai ga Aure???

Haba Yan Uwa Na  Brothers and Sister's

✏️ Abdullahi Ibraheem Isah Dabai

Tacewa da Yadawa Mas'udu Dan Masani Shinkafi 08149993999

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post