Mabruka Muhammad Malam~Madori, Sista Abin Koyi Ga Sistocin Harka Islamiyyah,


Tare Da Dan Uwanku {Abdullahi Ibraheem Isah Dabai,

A Takaice kai tsaye Wani fili ne a Jaridar Almizan na aikawa da Sako Mai Ma'ana Wanda Ya Kumshi Ilmantarwa Da Fadakarwa Da Nuni Kule Da Sauran Su

Wata Rana Na  Amshi Wayar Abokina Na Aika Da SakonTaya Sistoci Murnar Zagayowar Watan Da Aka Haifi Sayyida Fatima  Zahra {S.A}Diyar Manzon Allah Matar Imam Ali Maman Tagwaye  {Hagan }Da {Husain}{A.S},

Almizan Na Fita Ranar Juma"a Abban Ta Ya Siyo Musu Daya Su Karanta Shi Kuma Ya Siya Wa kanshi Guda,

Bayan Ta Karanta Muhimman Kanun Labaran Dake Bangon Farko Sai Taje Ta Karanta Daga Gidan Annabta Tare da Malam Abubakar Abdullahi Almizan {Marigayi }Filin Dayake Dauke da Adduo'i Na Neman Tsari Da Samun Yardar Allah Da Sauran Su

Sai Taje Filin Tunatarwa Tare da Sayyid Ibraheem Yaqoub Zakzaky{H}Shima Tagama Karantawa Sai Ta Aje Jaridar Almizan Din Tayi Shiri Ta Tafi Fudiyya,

Bayan Tadawo Daga Fudiyya Tayi Alwala Tayi Sallar Maghribayn Ta Gama Tayi Tasbihuz Zahra Tayi Wa Kanta Da Iyayen ta Da Sauran Al'Umnar Musulmin Duniya Fatan Allah Ya Tsare Su ya Kare su yayi Musu Arzikin Duniya da Lahira ,Marasa Lafia Na Gida Dana Waje Allah Yabasu Lafia

Bayan Ta Kammala Ta Dauki Littafin Arba'una Hadees Taje Wurin Babbar Yayar su Mace{Sajida} ta Karanta na jiya Aka Kara Mata Hadisai Biyu aka Bata Minti Goma ta karanta Ta Maimaita  inda aka Kara Mata In tagama Taje Tayi Abunda Take so,

Tagama Nazarin Abinda aka Karanta Mata Ta Duba Agogo Taga Karfe Tara Da Rabi Daidai 9:30.

Maimakon Taje Ta Kwanta Sai Ta Kunna Alwilaya TV Ta Kalli Na Minti Talatin Tagama Komai Da Komai Karfe Goma Na Dare  Daidai,Sai Taje Tayi Alwala Tayi Sallah Raka'a  Biyu Ta Karanta Adduo'in Da Ya Kamata Mutum ya Karanta idan zaiyi Bacci,Ta Kwanta Yadda Ake Kwantawa Ma'ana Ta Fuskanci Alqibla Yadda Ake Kwantar Da gawa A Cikin Kabari,

Karfe Biyu Taji Wayar ta tayi Kaara Na Lokacin Tunatarwa {Alarm  Time }Ta Tashi Ta Zagaya Bayi Takama Ruwa Ta Fito Tayi Alwala Tayi Sallolin Nafiloli Na Dare Tana Gamawa Ta Dauki Nuurul Aãshiqeen Ta Karanta Adduo'In Neman Gafara Da Neman Yardar Allah ,Bayan Ta Kammala Ta Dauki Saheefatus Sajjadiyyah Na Imam Aliyu Zainul Aãbideen{A.S}Ta Karanta Wasu Munajatoti Bayan Ta Kammala Sai Ta Dauko Mafaatihul Jinaan Shima Ta Karanta Abinda Ta iya na Adduo'i,

Allahu Akbar Allahu Akbar Allahu Akbar Allahu Akbar

Ladanin Masallacin su Yakira Sallah Sai ta Ajiye Littattafan Addu'ar Gefe Guda Ta Kira Sallah Ta Tada Ikama Tayi Sallar Ta Ta Gama Ta Dauki Alkur'ani Ta Karanta Shafi Bakwai Gari Yafara Haske Taje Dakin Maman ta Ta  Duka Ta Gaishe ta acikin Sanyayyar Murya Dake Nuna Ladabi Da Biyayya Dake Tsakanin Uwa Da Diyar ta,

Tagama Gaishe Da  Umman ta Ta fita Dakin Taje Dakin Abban Ta Shima Ta Duka Cikin Ladabi Da Biyayya Ta Gaishe Shi ,

Bayan Tafita a dakin Abban Nasu Sai Taje Ta Dora Ruwan Zaafi Na Shayin Da Yara Zasu Sha su Tafi Fudiyya Nursery and Primary Ta Kuma Dora Ruwan Da Za'ayi Musu Wanka Dashi Ruwan Yayi Zaafi Ta Dauko Robar  Wanka Tazuba Tayi Surki Dana Sanyi Yayi Daidai Ayiwa Yara Wanka.

Maman Su Ta Dauko Yaran Biyu{Subaika}Da{Ali Karrar} Ta Kawo Su Tayi Masu Wanka Tayi Musu Shafa Tabasu Shayi Suka Sha Aka Goya Musu Jakar Makaranta a baya Akaba Driver Yatafi Dasu Makaranta,

Zan Cigaba Insha Allah ,

Tacewa da Yadawa Mas'udu Dan Masani Shinkafi 08149993999

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post