KO KUN SAN:- Abun da Ya faru Ga Sayeed Zakzaky (h) A Irin Wannan Ranar Ta,12 Ga Watan September 1996


WABACHA: Kama Sheikh Zakzaky (H) A Ranar 12 Ga Watan September 1996

 Yau ranar 13/September/2020 wanda yake alamta Shekaru 24 da Azzalumar Gwamnatin Dolo da bindiga (Sani Abacha) ta kama Sheikh Zakzaky (H). Gwamnatin Janar Sani Abacha ta turo Jami'an tsaron Yan Sanda ne hade da Mopol a wannan ranar ba tare da Sheikh Zakzaky din ya aikata wani laifi ba, inda Jami'an tsaron suka zo cikin jerin gwanon Motoci suka kewaye gidan da bindigogi suna surutai a da Asubahin ranar bayan an idar da sallah.

 Wannan surutan nasu yasa Malam Zakzaky (H) ya fito domin jin meye ya kawo su gidansa, yana fitowa suka bashi takardar cewa an basu daman su shiga gidansa suyi bincike saboda ana zargin akwai makamai a gidan. Nan dai Malam (H) yace musu zasu iya shiga amma lallai sai dai su samo yar Sanda mace ta shiga sashin da matansa suke saboda bazai yarda namiji ya shiga wannan sashin ba. Haka dai aka yi su shiga suka gama bincikensu basu ga komai ba sai suka fito.

 Bayan fitowarsu sai suka cewa Malam (H) zasu bukaci yace Ofishinsu a Kaduna domin yayi Signing na cewa anyi bincike a gidansa ba a ga komai ba, Nan take Malam yace "Wannan wani irin abu ne haka? Kun nuna min takardar bincike kuma yanzu daga baya kuce kamu zaku yi". ACP Mukhtar Ibrahim wanda ya Mutu yanzu haka ya dage da cewa lallai ba kamu bane, kawai za aje ayi rahoto ne Malam ya dawo. Sai Malam Zakzaky yace kar ka mai dani wawa mana, kawai kuce kunzo kamu ne!!

 A wannan lokaci Malam ya shiga ya dauko kayansa (Al'qur'ani, da sauran kayan addu'o'i) ya fito. Yan uwa suka fito suna nuna lallai ba a isa a tafi da Malam ba, amma Malam yace musu su hakura, kar yan uwa su damu. Yayi wasiyya ga yan uwa cewa " Duk abin da ake yi na Harka kar a fasa". Malam (H) ya cewa ACP Mukhtar tunda kunce ba kamu bane zanje da Kanina shi kuma Malam Turi zai tuka Mota nan suka shiga a tafi Malam Turi yana tuka mota shida Malam a gaba, Sayyad Badamasi da ACP Mukhtar suna baya, wannan tafiyar a nan ne suka kama Malam.

Bayan rike Malam da Gwamnatin Abacha tayi a lokacin, yan uwa sun fito Muzahara a ranar 13/September/1996 domin nuna rashin amincewarsu, inda a turo Jami'an tsaro suka aukawa yan uwa a ranar wannan yayi sanadiyyar Shahadan mutum 15. Sannan a ranar 18/September/1996 ma yan uwa sun sake fitowa Muzahara domin sake matsawa Gwamnatin akan ta saki Sheikh Zakzaky data kama, sannan kuma a nunawa duniya irin zaluncin da Gwamnatin tayi a ranar Juma'a 13/September/1996 a garin Zaria.

 Tun kafin ayi Muzaharar ranar 18 ga watan September Jaridu da dama sun bayyana cewa yan uwa zasu yi babban Jahadi a Kaduna, lokacin ne kwamishinan yan sanda Yakubu Shuaibu yayi barazanar in har yan uwa suka fito zasu karya qafafunsu, kai kace haka dokar da yake karewa ta tanadar. A ranar Laraba sai yan uwa suka fito Muzahara daga Masallacin Maiduguri Road, aka biyo ta Ahmadu Bello Road,  aka bi ta Katsina Road sannan a biyo ta Kano Road. A wannan ranar ma Jami'an tsaro su aukawa yan uwa sun zubar da jini sosai an dibi Shahidai a wannan ranar. Allah ya kara dauyin kasa ga Janar Sani Abacha ya nuna mana karshen su Janar Buhari da El-rufa'i da duk masu yakar Harka da baya dana yanzu dama na nan gaba, ya kuma dawo mana da Jagoranmu cikinmu.

 - Ibrahim Almustapha Saminaka
 - 12/September/2020

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post