Inaso Mu Hadu Dake Amma Ba'a Gidan ku ba!!! _ Inji Saurayin Wata Sista
Inji Saurayin Wata Sista,

Kashi na farko

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai,

Tsira da aminci Su Tabbata ga Annabin da'ka aiko Shi da Sakon da Yahada komi Zuwa ga Al'ummar sa,da iyalan Gidansa Tsarkaaka,

Addinin Musulunci Ya Tanaji Wasu Shekaru Daya kamata Uba Namiji ya aurar da Yayansa Macece ko Namiji,Amma Kafin Haka Yafara Dorawa Iyayen Kula Da Dukkan Dawainiyoyin Yaran nee Kaama daga Ilmantarwa,Tarbiyyantarwa, Ciyarwa da Shayarwa Kafin Zuwan Wancan Lokacin Na Aurar Dasu,

To Yana Daga Basu Tarbiyya a kula da Shiga da Ficen su da Abokan su da Wuraren da Suke Zuwa,

Kuma Wannan Nauyin Kashi Sittin ko Saba'in Yanakan Mahaifiya nee,a Yayin da Sauran ke kan Mahaifi,

Yanada kyau ka kula dawa Yarinyar ka ke Tarayya,Yanada kyau ka kula dawa yaron ka ke Tarayya,Da Zaran Yaronka Yafara Soyayya Dolene kayi kokarin Sanin Da Yarinyar Wanne Gida Yake Tarayya Don ku sani ku Tunkari Abinda ke Gaban ku na Aurar dasu Idan Sun Fahimci Junan Su,

Yanayin Yadda Ake Tarbiyya Ada Yasaba da yadda ake Tarbiyya Yanzu,

A Baya Yaro Na Kowa nee,Amma Yanzu abin yakoma Yaro Kamar Na Iyayensa nee kawai,

Mutum Daya Kuma Baya Iya Baada Tarbiyya,Saboda Ba'agida kawai Yaran Suke Rayuwa ba,Akwai Wurare dayawa Da Yaran ke Zuwa Inda Babu Iyayen su a Wurin,Ko Ince dayawan mu Halayen mu a Gida Masu kyaune a Waje muke Nuna Marasa kyawun,

Yanada kyau mu Chanza Yanayin Da Yaran mu ke Samun Tarbiyya a Yanzu,Shiyasa Gayanan Tarbiyyar Taamu Jiya Iyau,

Mama Na!Inna ta!Umma na!Mummy na!

Wannan Rubutu kusan Ince Naki ne keda Mai Gidan ki akan Tarbiyyar Yaran ki,Mi Zaisa Kiyi Soyayyar Da Addini Ya Tanadar,Kuyi aure Irin Yadda Addini ya tanazar,Ku Haifi Yaara ta hanyar data Dace KU  Tarbiyyantar dasu Yadda Addini ya Tanazar daga Yarintar Su Zuwa Lokacin Balagar Su Sai Yazama Kunyi Sake a Daidai Lokacin Wani Yayi Kutse Yabata muku Tarbiyyar Yarinyar KU,

Da Farko Yanada kyau kisan Adadin Mazajen Da Yarinyar ki ke Fita waje Don Saurarar su a Matsayin Hira,Wanda hakan ma ba daidai bane,Sannan Yanada kyau kisan ko Su Waye Domin Yawan Su Zaisa a Saami Na Banza a Cikin Su,Yanada kyau ku Siyawa Yarinyar ku Waya Don Saukake Hanyoyin Fadada karatun ta Da Sanin Yadda Duniya ke Ciki da Sanin Cigaba da Wayewar Addini Da Zamani,

Saboda Rashin Siya Mata Wayar ma Wani hadarin nee,Saidai Yanada kyau kada kibari Wani a Waje da Baku Tabbatar da Waye Shi ya Hali da Tarbiyyar sa yake  ba Ya Siyawa Yarinyar ku Waya,Saidai in a kalla Kun Masa alkawarin Auren ta,in mada Haali a Bari Sai taje Gidansa Sannan Yasaya Mata,Saboda Yanzu Samari Suna Daukar Hakan a Matsayin Tarko ne,

Saidai hakan Bai Hana asa Mata ido Koda angama Yadda da Hankalin ta,

Illar Da Rashin Bibiyar Halin da Yarinyar ki ke Shiga Da Rashin Sanin Da Wadanne Samari take Hira da Rashin Sanin Mi take da Wayar ta Bazai Haifar wa Ita Diyar Taki dake kanki da Sauran Al'umma da Dã Mai Ido ba,

Mama Na kada in Cika ki da Surutu,

Karanta kiji Abinda yasa Nike Wannan Rubutun,

Dayake Yanzu Anfi Samun Samari Anfi Soyayya  a Waya Saboda Akwai Hanyoyin Sadarwa Kamar Su Facebook, WhatsApp, Skype,Da Sauran su,

To Hakan Yasa Yanzu Samarin Suka Rage Zuwa Kofar Gida su Aika a Kira Musu Budurwa don Suyi Fiira,

A ita Wannan wayar ake komi,

Wata baiwar Allah tahadu da Wani bawan Allah Suna Gaisawa a Facebook,Sai yau da Gobe abin ya rikide Yazama Soyayyar da ba  Sanin  Mahaifiyar ta Balle Mahaifin ta,Shima Kuma Saurayin Iyayen Shi Basu Sani ba,

Saurayin Yakan Kira ta Su Gaisa a Waya,Sukan Kuma yi Fiirar Soyayya irin ta Zamani,Ana haka Sai ya yanke Shawarar Yana So Yazo Garin Su Ya Ganta,Sai kuwa ta Yadda, Watarana yayi Wanka Yayi aron Jakar Tafiya Da Takalmi na Fita Kunya,Yayi Sallama Da Abokan Sa akan Zaije Wurin Abokinsa,ko Iyayen sa Bai Sanar ba Saboda Baiyi Niyyar Kwana a Garin da Zaije Wurin Budurwar Tãsa ba,

Ana Saura Kwana Biyu Yaje Ya Sanar Da'ita zaizo Wajen ta,Saita amsa Masa,Bayan kwana Biyu Ya Shirya Yaje Tashar Mota Yahau Motar Garin Su Budurwar Taashi,Yana Isa Sai ya Kira ya Gaya Mata ya Sauka a........Sai Tace Yahau mashin Yace a kawo shi.........Tafada Mishi Sunan anguwar su,

Yana Isa dama ta dafa Masa abinci takawo Masa da Ruwan Sha da Sauran su,Ta Fita Waje ta bashi Wuri yagama cin abincin Sai Yazo Ya Zauna Sukayi Fiira,Suna Cikin Fiira Yariqa Surka Mata da Yan Maganganun da Basu Dace ba,Amma dai a Hakan ta Cigaba da Wasu adduo'i na Neman kariyar Allah akan Duk Abinda yake Nufi akanta mara kyau,

Hakan Suka Gama fiirar a Takaice,Da Rabon Za'ayi Sai Yace Mata aiko yanada Wani aboki Mai Suna.........Sai Tace Bayanan Yayi Tafiya,Sai Yace to Yanada wata Kawa/abokiya Yafada Mata Sunan ta,Tace Tasan Gidan su,To a Hanyar Tafiya Gidan Kawar Tasu ne Yadan Rika Fada Mata Maganganun da Basu Dace da'ita ba, Sai tayi kokarin nusar Dashi akan abubuwan Dayake fadan Nan basuyi daidai Dashi ba,Kuma itama batajin dadin Abinda yake Fada Mata,Sai yake Kokarin Nuna Mata kamar Bata wayeba, batasan Zamani ya Canza bane,???

Sukaci Gaba da Tafiya da Niyyar Zuwa Gidan Kawar tasa Daya fada Mata tace tasan Gidan Nasu,Suna kan Hanya Yace Su dan tsaya anan Mana,Tace Masa ai Nan ba Wurin tsayawa  bane,yace Mata ta tsaya taji ko mi Zai Fada Mata Mana,Tace bazata tsaya ba,yakama Mata Hijabi ya riqe,Tana Ya Saketa Yana Ta Tsaya ta Saurare Shi Mana, Sai Take ce Masa ya Za'ayi ta tsaya ta Saurare Shi a Yanayin da Suke Hijabin ta Na a Hannun Shi

A Maimakon yayi kokarin sakin ta Saboda Gudun ta taara Masa mutane ko tayi Masa Mummunar Fahimta da Tallata Shi don Mutane Su San Shi su Gujeshi,

Saboda Rufa Masa asiri Yanada kyau,Amma Kuma Barin shi Haka Zai Taimaka Masa Wajen Cigaba da ire~iren Wadannan Ayyuka da Basu Dace ba.....

TIRQASHI

Don Jin Yadda Ta Kaaya Mu Hadu a Kashi na Biyu,

Daga Abdullahi Ibraheem Isah Dabai

Tacewa Da yadawa Mas'udu Dan Masani Shinkafi 08149993999


DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

1 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post