Dalilin Da Yasa Ake Kiran Fatimatu Da Az-zahra (S.A)


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


HASKE NE DA AKA SAMAR DA LIMAMAN SHIRIYA DAGA CIKINSA 


Azzahra na daga cikin sunayen da Allah ya ambaci Sayyidah Fatima (S. A) da shi wanda a yanzu mata suke cin sunayensu da shi tare da tinqaho da shi cikin suna mafi daukaka . 


Dalilin da yasa Allah (T) ya ambaceta da wannan suna ya zo cikin riwaya daga Abu Abdullah (A. S) kamar haka; 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


 ع، علل الشرائع أَبِي عَنْ مُحَمَّدِ بْنِ مَعْقِلٍ الْقِرْمِيسِينِيِّ عَنْ مُحَمَّدِ بْنِ يَزِيدَ الْجَزَرِيِّ عَنْ إِبْرَاهِيمَ بْنِ إِسْحَاقَ النَّهَاوَنْدِيِّ عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ حَمَّادٍ عَنْ عَمْرِو بْنِ شِمْرٍ عَنْ جَابِرٍ عَنْ أَبِي عَبْدِ اللَّهِ ع قَالَ:


 قُلْتُ لِمَ سُمِّيَتْ فَاطِمَةُ الزَّهْرَاءُ زَهْرَاءَ فَقَالَ لِأَنَّ اللَّهَ عَزَّ وَ جَلَّ خَلَقَهَا مِنْ نُورِ عَظَمَتِهِ فَلَمَّا أَشْرَقَتْ أَضَاءَتِ السَّمَاوَاتِ وَ الْأَرْضَ بِنُورِهَا وَ غَشِيَتْ أَبْصَارَ الْمَلَائِكَةِ وَ خَرَّتِ الْمَلَائِكَةُ لِلَّهِ سَاجِدِينَ وَ قَالُوا إِلَهَنَا وَ سَيِّدَنَا مَا هَذَا النُّورُ فَأَوْحَى اللَّهُ إِلَيْهِمْ هَذَا نُورٌ مِنْ نُورِي وَ أَسْكَنْتُهُ فِي سَمَائِي خَلَقْتُهُ مِنْ عَظَمَتِي أُخْرِجُهُ مِنْ صُلْبِ نَبِيٍّ مِنْ أَنْبِيَائِي أُفَضِّلُهُ عَلَى جَمِيعِ الْأَنْبِيَاءِ وَ أُخْرِجُ مِنْ ذَلِكَ النُّورِ أَئِمَّةً يَقُومُونَ بِأَمْرِي يَهْدُونَ إِلَى حَقِّي وَ أَجْعَلُهُمْ خُلَفَائِي فِي أَرْضِي بَعْدَ انْقِضَاءِ وَحْيِي.


" Nace, me yasa aka ambaci Fadimatuz-Zahra da suna Az-Zahra ?


 Yace , " Domin Allah mai girma da daukaka ya halicceta ne daga hasken azamarsa, yayin daya qago ta sai ya haskaka sammai da qassai da haskenta, sai ya haskaka idanuwan Mala'iku, sai Mala'iku suka fadi suna sujadah ga Allah. Kuma suka ce; 


" Yaa abin bautarmu kuma shugabanmu! Wannan wanne irin haske ne haka ?" Sai Allah yayi wahayi zuwa gare su cewa; 


" WANNAN HASKE NE DAGA HASKENA KUMA NA AJIYE SHI CIKIN SAMA. NA HALICCE SHI NE DAGA AZAMA TA KUMA ZAN FITAR DA SHI DAGA TSATSON WANI ANNABI DAGA CIKIN ANNABAWANA , KUMA ZAN FIFITA SHI AKAN DUKKAN ANNABAWA, SANNAN ZAN FITAR DAGA WANNAN HASKE WASU LIMAMAI (jagorori), SUNA TSAYUWA DA AL'AMARINA, KUMA SUNA SHIRYARWA ZUWA GASKIYA. SANNAN ZAN SANYASU KHALIFOFI CIKIN QASA BAYAN YANKEWAR WAHAYI. "


مصباح الأنوار، عن أبي جعفر ع‏ مثله بيان قال الفيروزآبادي قرميسين بالكسر بلد قرب الدينور معرب كرمانشاهان.


6- مع، معاني الأخبار ع، علل الشرائع الطَّالَقَانِيُّ عَنِ الْجَلُودِيِّ عَنِ الْجَوْهَرِيِّ عَنِ ابْنِ عُمَارَةَ عَنْ أَبِيهِ قَالَ: 


سَأَلْتُ أَبَا عَبْدِ اللَّهِ ع عَنْ فَاطِمَةَ لِمَ سُمِّيَتْ زَهْرَاءَ فَقَالَ لِأَنَّهَا كَانَتْ إِذَا قَامَتْ فِي مِحْرَابِهَا زَهَرَ نُورُهَا لِأَهْلِ السَّمَاءِ كَمَا يَزْهَرُ نُورُ الْكَوَاكِبِ لِأَهْلِ‏


Na tambayi Abu Abdullahi game da Fadima, me yasa ake kiranta Az-Zahra? Yace, 


" DOMIN ITA TA KASANCE IN TA TSAYA A MIHRAB (gurin da take yin sallarta) HASKENTA NA HASKAKA HALITTUN SAMMAI KAMAR YADDA HASKEN TAURARI KE HASKAKA SU ."بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج‏43، ص: 13


الْأَرْضِ.

Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da Ado Isah Guda. 


        (08126385470)


17th Sep, 2020/ 29th Muharram, 1442.

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post