"BAA DON NI SUKE ZUWA BA"

Daya Daga Cikin Hutunan Sheikh Yaqub A lokacin Zaman Juyayin Ashura


{KASHI NA DAYA}

Daga Shafin Ma'asumah Nigeria News Updated

Tare da l:-
,✓√ Abdullahi Ibraheem Isah Dabai✓√

Tunda aka faara Zaman juyayin waqi'ar ashura ta imam Husain baitaba faashi ko makara/latti ba, kawai Sai Wata Rana aka kula Mai Zama a wurin dayake Zama baizo ba,

Akayi Cigiyar  iyaye ko Yan uwa ko abokan sa ko Wadanda Suke anguwa Daya Amma ba'asamu ba,

Anje anduba takardar da'ake rubuta sunan mahalarta da Sunan Garin su da anguwa da lambar waya Sai aka saamu,

Ana Kira ta shiga Amma ba'a dauki Kiran ba,an maimaita haka har sau uku,

Ananan aka Kira Sai aka daga,Sai ake Tambayar dawa ake magana,saboda Namiji ake Kira amma Mace ta daga Kiran,

Sai take cewa"Ni Yar uwar Mai wayar ce,Sai aka Tambaye ta Ina ainihin Mai wayar???

Sai take cewa tun ranar Daya dawo Zaman juyayin waqi'ar ashura ta imam Husain dare bakwai bayajin dadin jikin sa ko fitama Bai iyayi,akace Mata Zai Yiwu Ayi magana Dashi???

Sai tace Bata Sani ba,Amma a gaafarceta ta  tambayo Shi,

Tana Zuwa kofar dakin sa taga a bude yasaki  Laabule,tayi Sallama Bai iya  amsawa ba saidai yayi mata gyaran Murya alamar Zata iya Shigowa,tana Zuwa taga yaasa kansa akasa Yana faaman ruusa Kuka,Yawan kukan dayayi yasa fuskar sa ta kunbura, idanuwan sa sukayi jajawur suka cuko,tayi kokarin lallashin sa don yabar kukan Amma abin yaafi karfin ta,

Ta Kira lambar da'aka Kira Tace ta Shiga Daki Domin Gaya Masa an kirasa aji dalilin Rashin Cigaba da zuwan sa wajen Zaman juyayin waqi'ar ashura ta imam Husain Amma ta ganshi a Yanayin da Bata taba Ganin sa a cikiba Tunda tayi wayau,

Masu kulada Wannan Bangaren Na Bincike da kulawa da Shiga da ficen mahalar ta suka yanke Shawarar Zuwa Garin su don duuba Yanayin jikinsa,

Suna Zuwa aka Sauke su a Bangaren saukar baaki Na Gidan Amma Bangaren mabiya mazhabar imam ja'afar as swadiq (a.s)akwai komi da komi da Mabiyin mazhabar imam ja'afar as   swadiq (a.s)yake Neema,Kamar Alƙur'ani Mai Tsarki da irin littattafan adduo'i irin su,Nuurul Aashiqeen,Saheefatus Sajjadiyyah da kaamila,Mafaatihul jinaan da Diyaa'us Swaaliheen da Sauran su,

Basuyi wata~wata ba sukayi alwala su Duka Daya a cikin su (Jagoran tafiya)ya Shiga Gaba yajasu sallar Zuhrain(Zuhr da asr)

Suna kammalawa Daya a cikin su ya dauki littafin adduo'i ya karanta ta'aqeebat Na sallar Zuhrain,Yana kammalawa Sukayi Sujuudush shukr Kowa yatashi a muhallin,

Sai ita wannan Yar uwar tashi taje taga ko sun kammala,tana Zuwa taga sun kammala Kowa najan Tasbaha(Carbi)

Ta Shiga dakin cikin Shigar Kamala da Hijabin ta Baki Mai haba,da safar hannu data rufe Hannun ta rijif Sai iya inda Zata riqa Amfani Dashi don dauka ko Riqe wani Abu,da Kuma Safar kafa Kamar yadda Addini ya tanada Kuma ya Koyar,

Tana Shiga ta duuqa har kasa ta gaishe su cikin Yanayi Na Tarbar baaqi,ta saki fuskar ta tana Mai musu maraba da sannu da Gajiyar hanya,

Cikin Yanayi Na bakunta suka Amsa cikin Yanayi Na Farin ciki da jin dadin Tarbar da akayi musu da Yanayin data Shiga wurin su cikin kammalalliyar Shiga,

Ana Gama Gaisawa suka Gabatar da kansu,Daya a cikin su(Jagoran tafiya)ya Gabatar da kansu da dalilin  zuwan su yanamai cewa:~...........

Mune masu kula da mahalarta da Shiga da ficen su,da Kuma kyautata Jin dadin su da karbar koke da kura~kurai Domin gyaarawa,

Mun Kula kwana uku Wannan Bawan Allah baya Zuwa Wurin Zaman juyayin waqi'ar ashura ta imam Husain,shine muka Zo muji ko Lafia Tunda rannan mun Kira bamu Samu damar magana Dashi ta waya ba,

Sai tace na'am ta Gaane su,Kuma tabbas sunyi Farin ciki da Jin Dadi da Wannan kulawa tasu,

Har tayi addu'ar imam Husain ya Karbi aikin su ya share hawayen su ya biya musu bukatun su,

Sai tanemi Izinin fita don Zuwa Kira Shi Yayan nata da akazo dubawa,tana Zuwa Sai tayi Sallama ya Amsa,Tace in Shigo yace na'am Shigo,tana Shiga ta gaida Shi ya Amsa,Ganin alamun Yadan Samu Sauki tajashi da wasa Nayan sakonni,

Sai tace mutanen da suka kiraka nee kwanaki Basu Samu damar yin magana dakai ba sukazo don duba ka da Yanayin jikin Naaka,

Sai yace Suna Ina ???

Sai tace Suna wajen saukar baaqi,Sai yace Mata Takai su inda ake gaanawa da baaqi dake cikin Gidan,

Taje ta amshi mabuudi ta Buude kofar Takai ruwan Sha Dasu Lemun barewa Dana kwalba,da abinci Na alfarma da'aka je aka siyo don tarba da Girmama Baki,taje ta Kira su suka Shigo dakin gaanawa da baaqi Tace su jira Shi anan Yana Zuwa,

Zan Cigaba  insha Allah,

Tacewa da Yadawa Mas'udu Dan Masani Shinkafi 08149993999

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post