ALKALIMMU, ALLAH..._(Labari Mai Sosa Zuciya).


@Ma'asumah Nigeria News Updated

Assalamu Alaikum Wa Rahmatullah Wa Barakatuhu.

Sunana Ummu Abiha, Ni ce wadda azzalumin gwamnan kaduna ya sa karnukansa mashaya jini suka afka wa 'yan'uwana a ranar 10 ga watan Almuharram,  ranar Ashura,1442 a Kadunan Najeriya,  ranar tunawa da kisan gillar da kakannin el-rufa'i suka yiwa jikokin Manzon Allah (S) a Filin Karbala a shekara ta 61 bayan Hijirar Nabiyul A'azam (S.A.W.W).

A ranar da akayi wannan harin ta'adanci (Lahadi) da rana tsaka  aka harbi 'yan'uwana. Wasu suka jikkata, wasu kuma suka yi Shahada ciki har da Sahibina, abin kaunata, farin cikin zuciyata, Masoyina wanda nake burin ya zamo uban 'ya'yana wato Shaheed Bashir Muhammad Kaduna.

Ni ce wadda azzalumin gwamnan kaduna yasa aka kashe wa masoyi wanda na sa a raina, wanda saura kiris a saka mana rana dashi saboda soyayyarmu da shakuwarmu ta riga tayi nisa mun riga mun gama aminta mu zama miji da mata tsakanina dashi.

Allah Sarki, ban manta farkon haduwata dashi,   bai zo mani da yaudara ba domin bai fara magana da ni ba sai da ya nemi izinin Mahaifina, kuma cikin ikon Allah Babana ya bashi dama. Bayan ya gabatar mani da bukatarsa na karbi Soyayyarsa hannu bibbiyu kuma daga nan muka damke juna ni da shi, kai kace tare aka haifo mu saboda yadda muke kula da girmama juna. A haka muka shafe tsawon lokutta muna shayar da juna madarar kauna, duk da ba a gari daya muke ba hasali ma akwai tazara mai nisa tsakanimu amma sakon Soyayyarmu da zuciyoyimmu bai hana kusanto da Junammu ba tamkar a gari daya muke.

Da tafiya tayi tafiya maganar aurenmu ta taso,  amma sai yace mani, "tunda ba a nan garinku nake ba, ki bari ki ida karatunki sai a saka mana rana, tunda yanzu kina a Level Two ne". Hakan kuwa akayi, wannan shi ne dalilin jinkirta auranmu da akayi sai na idasa karatuna a University. Haka muka ci gaba da rike amanar juna har izuwa lokacin shahadarsa shekararmu Ukku a tare.

Shaheed Bashir Muhammad Kaduna, mutumin kirki ne bawan Allah na gari, ba ya wasa da Addini, kuma kullum yana tunatar dani da kara mani kaimi gami da zaburar dani kan al'amarin addini dan gyra lahira ta. Mutum ne mai kyauta da son mutane bugu da kari shi baya da rowwa shi yasa ma da ka zauna dashi zaka ji cikin dan kankanin lokaci baka yi aune ba ya gama shiga ranka.

Labarin shi ya game kawayena da dangina da duk wani na tare dani, gashi ba wani saninsa sukayi irin sosai dinnan ba amma da sunji labarinsa zaka ji kowwa na yabonsa. Shi yasa ma da labarin shahadarsa ya riskesu kowwa sai da ya zubda kwalla yayi kuka. Ba ya da wasa kan duk abinda ya tunkara har ma ya taba ce mani " indai kika ga abin nan bai yiwu ba (Aurammu) sai dai in babu raina, ni dai nafi son ki kwantar da hankalinki dan bana son bacin ranki" Allah Sarki, idanuwa ba zasu daina kuka da zubar hawaye ba a duk sadda na tuna da irin lallashi hadi da tausasan kalamansa a gareni.

Kullum burinsa shi dai yaga ya faranta mani, baya fushi ko kuma rike mutane ko da kayi masa laifi, kai shi na daban ne Wallahi.

Rabuwarmu ta karshe dashi, yazo lokacin da aka fara zaman karatun Ghadeer a garimmu (tunawa da ranar nada Imam Ali a matsayin Khalifan Annabi S.A a bayanSa). Daga nan muka rabu ya koma Kaduna,  dama ana yin Ghadeer a watan Zulhijja ne (watan karshe a shekarar Musulunci). Daga nan aka shiga watan farko wato Al'muharram...watan bakin ciki, watan alhini da zubar kwalla (Allah Sarki zuriyar Gidan Annabi) ba tsinanne sai mai farin ciki a ranar Ashura...

Zan Ci Gaba Insha Allah.

Rubutawa: Bin Yaqoub Katsina


Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post