Yanzu-yanzu: Zanga-zanga ta barke a birnin Barcelona kan shirin da Messi yake na tafiya

Dubunnan mazauna birnin Cataloniya a kasar Espana suna gudanar da zanga-zanga kan matsalar da dan kwallon kungiyar kwallon Barcelona, Lionel Messi, ya samu da shugabannin kungiyar.

Shahrarren dan kwallon ya bayyanawa shugabannin kungiyar kwallon cewa zai bar Barcelona nan take bayan sama da shekaru 20 yana taka musu leda.

Dan kasar Argentinan na shirin hannun riga da kungiyar kwallon da ya kasance yana bugawa wasa tun yana dan yaro saboda rashin jituwa da shugabancin kungiyar karkashin jagorancin Josep Bartomeu.

Mutanen sun yi tururuwa a kusa filin kwallon kungiyar da ofisoshin shugabanin domin zanga-zanga. Wasu daga cikin masu zanga-zangan na iwun 'Bartomeu yayi murabus'

Bayan kimanin shekaru 20, Lionel Messi ya shaida wa ƙungiyar Barcelona cewa yana son barin kungiyar.

Kungiyar ta tabbatar a ranar Talata cewa ɗan wasan ɗan asalin ƙasar Argentina ya rubuta mata wasika cewa yana son ya tafi. Sanarwar na zuwa ne kimanin kwanaki 11 bayan kayan da ƙungiyar ta sha na 8 - 2 a hannun Bayern Munich,

daya daga cikin kaye mafi muni a tarihin kwallon ƙafa. Wannan shan kayen ya ƙara wa kungiyar abin takaici - duba da cewa tun 2007-08 ba su ci kofi ba ga shan kaye kamar yadda Sky reports ta ruwaito.

Messi ya lashe Ballon d'Or guda shida yayin zamansa a Barcelona a matsayin ɗan wasan daga cikin mafi girma a duniya. Ya kuma taimaka wa kungiyar ta lashe kofin gasar wasar ƙwallon ƙafa na Spain guda 10 da gasar ƙwallon wasan 'Champions League' hudu

SOURCE:LEGIT.NG

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com
ZAINILABIDINA AHMAD SULEIMAN

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post